An ware duk ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da ci ta gumi ko bautar da yara ta duniya.
Taken ranar a wannan shekarar 2023 ita ce “Adalcin Zamantakewa ga kowa: Mu kawar da Bautar da Yara”.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranar, kuma tun shekarar 2000 duniya ta samu cigaba mai wajen rage aikatau da bautar da yara.
Sai dai cikin ‘yan shekarun da suka gabata, rikice-rikice da annobar COVID-19 sun jefa iyalai cikin kangin talauci.
Wannan ya haddasa fadawar miliyoyin yara cikin aikin kwadago don ceton danginsu.
A yau, akwai yara miliyan 160 da suke ayyukan da ba su kamaci shekarunsu ba, wanda yake nuna ana ci da gumin yaro daya cikin duk yara 10 a fadin duniya.
A Afirka matsalar ta fi kamari, inda ake ci da gumin yaro daya cikin duk yaro biyar, kuma yara miliyan 72 abin ya shafa.
Bayan Afirka, ana aikatau da yara miliyan 11 a Latin Amurka, da miliyan shida a Turai da Tsakiyar Asiya, da miliyan daya a kasashen Larabawa.
Alkaluman Hukumar Kwadago ta Duniya, da Hukumar Abinci ta Duniya sun nuna kashi 70 cikin 100 na yaran da ake ci da guminsu, suna harkar noma da kiwo.
Akwai yara miliyan 112 mata da maza da suke aiki tsawon awanni a yanayi mai hadari.
Ci da gumin yara ya saba wa hakkokin yara, sakamakon saka lafiya da iliminsu cikin hadari.
Yawaitar wannan matsala wani sakamako ne na talauci a karkara, sai kuma rashin shirye-shiryen tallafi da kariya ga marasa karfi.
TRT Afrika ta tattauna da Nura Ahmed Muhammad, babban daraktan kungiyar Mufarka, mai kula da lamuran matasa; da kuma Mrs Dorathy Nuhu Akevona, shugabar wata kungiyar kula da kare ‘yancin yara, da ke Minna a jihar Nejan Nijeriya.
Ma’ana da yawaitar ci da gumin yara
A cewar Lauya Nura Ahmed Muhammad, “Ci da gumin yara shi ne amfani don gudanar da ayyuka, a yanayin da zai hana su damar more rayuwa cikin mutunci da kariya.
"Yarinta mataki ne mai muhimmanci kuma wajibi ne a kare shi.”
It ma Mrs Dorathy, ta ce bautar da yara shi ne, “Sakawa ko daukar yaran da ba su kai shekara 18 ba aiki, a irin yanayin da ba za su iya zuwa makaranta ba ko yin abubuwan da ya kamaci yara irinsu ba, domin habaka rayuwarsu.”
Ci da gumin yara yakan kunshi bautarwa, da cin zarafi, da gallazawa, wanda hakan yake cutar da al’umma.
Wannan al’ada takan dakushe cigaban yara manyan gobe, saboda suna shagaltuwa da ayyukan da ba su kai yi ba, wanda ke iya tasirin a manyantarsu.
Nau’ukansa sun hada da:
1) Tallace-tallacen yara
Yara a Nijeriya suna ayyukan neman kudi daban-daban kamar tallace-tallace a kan tituna, wanda shi ya fi yaduwa a duk fadin kasar.
Ana ganin yara a titi da tashoshi, da kasuwanni. Mafi munin wannan abu shi ne suna yin sana’ar ne a lokacin da ya kamata a ce suna makaranta.
Iyalai da dangi su ne ke da alhakin daukar nauyi ‘ya’yansu, da kare mutunci yara. Amma a al’ummomin da ba su barin iyaye mata su fita waje don neman kudi, a kan samu yara ne ake turawa.
Kalubalen talauci ba ya zama dalili, saboda hakkin iyaye ne su kula da ‘ya’yansu don kyakkyawar rayuwa.
2) Aikatau a gidaje
Yara ‘yan kasa da shekara 18 suna aikin gida, yawancin a kan kai su gidajen cikin birane, a yanayin da babu mai tallafa musu kuma ba su da wata alakar ‘yan uwantaka.
Lauya Nura Ahmed ya ce aikatau tamkar nau’I ne na bauta wanda doka ta haramta.
Mrs Dorathy Nuhu ta ce, “Mun lura a shekarun nan yadda ake cin zarafin yara a hanu su lokacin hutu, ba a kula da lafiyarsu, ba a ciniki, a buge su, a ci mutuncinsu.
Wasu a kan musu alkawarin saka su a makaranta amma a saba. Idan ma suna makaranta ba sa iya mayar da hankali kan karatu.
3) Karuwancin yara
Ana samun yara da ake ajiye a gidajen karuwai suna ma’amala da manyan mutane, ba tare da kare lafiya da ‘yancinsu ba.
Akwai kuma yaran da ake gani a otal-otal, da kulob-kulob, da gidajen rawa, da na raye-raye, wadanda a karshe rayuwarsu take lalacewa.
Mrs Dorathy Nuhu ta koka kan cewa, “Duk da cewa gwamnatin Nijeriya ta kafa dokar kare hakkin yara tun shekarar 2003, har yanzu yawancin al’umma ba su san me dokar ta kunsa ba, kuma ba a zartar da hukunce-hukuncenta yadda ya kamata”.
4) Koyon sana’a a yanayi mara kyau
Koyar da yara sana’a abu ne mai kyau, matukar an yi shi bisa tsari, inda yaran za su samu karatu, da koyon sana’a ba tare da an saka su aikin da ya fi karfinsu ba.
A kauyuka yara sukan shiga aikin noma ko kiwo, wanda yake hana su halartar makarantu, da sukunin wasanni da nishadi.
A kan samu yara a shagunan siyar da kaya, da na gyaran mota, da wajen yin bulo, da aikin gini, da kwasar shara, da sauran sana’o’i, a irin yanayin da bai dace da lafiya ko tunaninsu ba.
5) Bara da gararamba
Ana ganin yara masu yawon bara a tituna da layukan, musamman a birane, inda wasu daga cikinsu, sun baro gaban iyayensu kuma ba mai kula da cinsu ko shansu, balle lafiya.
Akan ce talauci ne ke sa iyalai amfani da yara wajen neman kudi don tafiyar da rayuwarsu.
Baya ga samar da turbar tattaunawa kan fafutukar kawar da matsalar, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, babban abin yi shi ne bibiyar tushen matsalar, da hadin kai kan yarjejeniyoyin karancin shekarun aiki, da zartar da kariyar shari’a daga dukkan nau’ukan ci da gumin yara.