Luckmore da kanwarsa mai suna Peace suna shan yabo domin bajintar da suka nuna. Hoto  Emmerson Mnangagwa      

Daga Charles Mgbolu

A ranar Lahadi, 3 ga watan Maris na bana ce Luckmore Magaya mai shekara 13 da ƙanwarsa mai suna Peace mai shekara 10 sun samu zama na musamman da Shugaban Kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, inda daga shigarsu wajen ganawar ya rungume su.

An karrama Luckmore da Peace ne saboda bajintar da suka nuna, inda suka fuskanci wani babban kada, suka kwaci mahaifiyarsu da karfin tsiya a cikin rafi.

Shugaban Kasa Mnangagwa ya ce zai ba kowanne daga cikin yaran wadanda suka ceci mahaifiyarsu Dala 5,000.

Lamarin ya auku ne kimanin wata biyu da suka gabata a gabar tekun Mupfure da ke garin Mhondoro, wani kauye da ke da nisan kilomita 114 daga Babban Birnin Harare.

A ranar Lahadi, 17 ga Janairun ce, Blantinna Magaya da yaranta suna tsaka da kamun kifi ne a bakin teku wani babban kada ya lallabo, ya ja kafarta.

Ko wata-wata Luckmore da Peace ba su yi ba suka far wa kadan domin kwato mahaifiyarsu.

Blantinna Magaya da yaranta bayan sun kwato ta. Hoto: Others

"Da na ga haka, sai na kama mahaifiyarmu, na rike ta karfi, sai ita kuma kanwata ta taka kan kadan da kafarta, sannan ta rika caccaka masa itace a ido," inji Luckmore a lokacin da yake bayyana wa mutanen kauyen yadda lamarin ya auku.

Duk da haka kadan bai saki mahaifiyar ta su ba, inda ya cigaba da kokarin janye ta cikin ruwan, amma suma a daya bangaren, yaran ba su gajiya ba, suka cigaba da fafatawa domin ceto ta. A karshe sun samu nasara, amma sun sha bakar wahala.

"Kadan na da karfi sosai, inda har ya kusa jan dukkanmu cikin rafin," in ji Luckmore.

Sai yaran suka jawo mahaifiyarsu, sannan suka nemi taimakon mutane wajen dauko ta.

A wani jawabi da Shugaba Mnangagwa ya wallafa a shafinsa na X, ya ce bajintar yaran abin, "ayaba" ne.

"Na dauki nauyin karatunsu, sannan na ba kowannensu Dala 5,000. Ya kamata mu rika karfafa irin wannan jarumta da tausayi a tsakanin matasanmu."

An ba yaran kyautar kudi, sannan an dauki nauyin karatunsu. Hoto: Emmerson Mnangagwa

Ita ma mahaifiyar yaran Blantinna Magaya, wadda ta kasance a wajen taron, cikin hawaye ta yaba wa bajintar yaran, inda ta ce, "Ba zan iya tuna duk abin da ya faru ba. Abin da zan iya tunawa kawai shi ne lokacin da suka kawo min dauki a lokacin da kadan ke kokarin ja na cikin ruwa."

Hukumar Kula da Gidajen Zoo da Gandun Dajin Zimbabwe ZimParks, ta gargadi mutane su guji zuwa kamun kifi a duk rafin da aka san akwai kada a ciki.

A cewar hukumar ta ZimParks, an kadoji sun kashe kusan mutum 50 a shekarar 2023, sannan 85 sun samu rauni.

TRT Afrika