Ƴar-tsanar Ayabavi Atohoun na da siffar Afirka

Daga Firmain Eric Mbadinga

Baƙar ƴar-tsana da ke magana da harsunan Afirka ba abu bane da aka saba gani a duniya, wanda shi ne a halin yanzu Ayabavi Atohoun ke da zummar ganin samfurin nata sun zama na daban da sauran na Ƙasashen Yamma.

Waɗannan bebin robar waɗanda kamfaninta da ke Faransa mai suna Beautiful Darkness ke haɗawa, ana yinsu ne domin yara baƙar fata su rinƙa alfahari da asalinsu na Afirka da kuma murna da kyawunsu.

Ƴar tsanar da take samarwa ana yinsu ne domin nuna yadda baƙar fata take, da irin hancinsu da gashinsu da kuma laɓɓansu.

Atahoun ta samu horo a matsayin injiniyar sadarwa a Benin. Ta bayyana cewa burinta shi ne ta ga ta sauya yadda ake kallon baƙar fata, inda ta ce ba a samun 'yar-tsana baƙar fata sosai a Afirka.

"Na samar da wannan nau'in ƴar-tsanar ne sakamakon ɓacin rai a lokacin da na so na sayi baƙar ƴar-tsana ga wata ƴar ɗan uwana. Ƴar-tsanar wadda na yi zato tana da kyau sosai, ana samunta ne kawai a Amurka ga kuma tsada sosai. Sai na gano cewa ba ni da wani zaɓi, kuma zaɓin da nake da shi a lokacin yana da tsada," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika

An yi ƴar-tsanar ne ta yadda za su rinƙa tuna wa yara ƴan Afirka kan asalin yadda suke.

Akasarin ƴar-tsanar da Ayabavi ke sayarwa ana raɗa musu sunayen wasu fitattun mutane a tarihin Afirka.

Kamfanin Beautiful Darkness ya soma aiki ne a hukumance a 2019 inda ƴar-tsanar da ya fara sayarwa aka yi maraba da ita a kasuwa.

Bayan ta samu yabo mai kyau daga kafafen sada zumunta da kuma samun kuɗi, bayan shekara daya sai Ayabavi Atohoun da ma'aikatanta suka fito da shawarar samar da baƙaƙen ƴar-tsana waɗanda suke magana da harsunan Afirka.

"Mun fara ne da harsunan Afirka bakwai inda a halin yanzu muna da 15, baya ga Faransanci da Ingilishi," kamar yadda Atohoun ta shaida wa TRT Afrika.

Harsunan na Afirka sun haɗa da Bambara, Fongbé, Lingala, Mina, Mooré, Wolof, Yoruba da Swahili. Haba kuma ƴar-tsanar na magana da Fang, Peulh, Baoulé, Malinké, Sango, Dioula da Douala.

Ƴar-tsanar za su iya furta jimloli 80 waɗanda aka samo daga kalmomi kusan 400. Kuma maganganun da ƴar-tsanar ke yi na koya wa yaro ganin darajar kansa.

"Ni da kaina na tace kalmomin da nake so ƴar-tsanar su rinƙa furtawa. Waɗannan kalaman na ƙara ƙarfin gwiwa sakamakon za su samar da babban mutum gobe daga wanda yake yaro a yau. Ƴar-tsanar na iya cewa: Ina da kyau kamar ku, ina da ƙoƙri, ni mace ce mai jarumta. Haka kuma za su iya yin waƙoƙin ƴan naziri," kamar yadda Atohoun ta bayyana.

Ƴar-tsanar na taimaka wa yara yan Afirka son harsunan nahiyar.

Sabon ƙalubalen da Ayabavi ke fuskanta a halin yanzu shi ne samun sabbin kwastamomi.

"Bai kamata iyaye su yi tunanin cewa gayu ne kawai ba domin, bayan yayin da aka yi na Black Lives Matter, kowa yana sha'awar baƙar fata. Amma mun dade kafin haka.

"A yanzu ina yin iyakar ƙoƙarina domin nuna wa iyaye cewa ba wai tallar ƙawa bane kawai, amma ya kamata su rinƙa siya wa ƴaƴansu ƴar-tsana baƙar fata," kamar yadda Ayabavi mai shekara 28 ta bayyana.

A halin yanzu kasuwar Beautiful Darkness ta fi yawa ne a Afirka, inda take samun karɓuwa a Faransa da Amurka da Benin wanda wuri ne da Atohoun ta buɗe shagonta na farko.

Tana aikin buɗe wani shagon a Côte d'Ivoire da Senegal da ƙasashen Afirka da dama. Tana yin haka ne domin ita ma ta taka rawa wajen taimaka wa al'adun Afirka.

TRT Afrika