Babanmu ya kasance dan gwagwarmaya. A matsayinsa na mai yakin neman ‘yanci kuma wani shugaba a yaki tsakanin Eritria da Habasha, ya rasa idonsa na hagu sakamakon fashewar nakiyar kasa.
An kore shi daga kasarsa saboda ya hango mulkin kama karya.
Saboda haka, labarinmu ya faro ne kafin a haife mu, a lokacin da mahaifinmu da ya rasa ido daya da mahaifiyarmu mai dauke da ciki suka taka daga Asmara a Eritrea zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira a Gibra da ke Sudan — kwatankwacin tafiya a kafa daga birnin Los Angeles zuwa San Francisco.
Babanmu ya taba gaya mana cikin murmushi cewar: "Mun shafe watanni kadan muna yi, amma mun isa wurin.”
Sun yi wannan ba tare da wani zabi ko kudi ba, kuma sanye da kayayyakin da ke bayansu. Mahaifiyarmu ta haife mu cikin wata bukka da aka yi da tabo da ciyawa, yayin da mahaifinmu ya tsaya a waje cikin hakuri yana jiran wani abin ban mamaki.
Saboda rashin fasahar da za ta bayyana musu jinsin jaririnsu kafin haihuwar, sun yi imanin cewar za su haifi da namiji ne, don mahaifiyarmu ba ta da tsayi kuma cikinta ya yi tudu sosai. Amma sai aka haife mu tagwaye mata masu kama da juna.
Iyayenmu suka kalli sansanin ‘yan gudun hijiran kuma suka ga cewar ba wurin rainon iyali ba ne.
Duk da cewar babu kudi kuma babu komai fiye da fatan alkhairi, mahaifiyarmu ta nemi shiga shirin Amurka na bai wa ‘yan gudun hijira mafaka.
Ya kai shekara daya, da imaninta da kuma jajircewarta, an dauke mu.
Wannan na nufin za mu bar danginmu, barin dukkan abubuwan da muka taba sani, don samun wani gida a Rochester da ke New York — garin da aka raine mu kuma ya bude mana ido kan yadda muke ganin duniya.
Da muka isa wajen, sai da muka koyi sabon harshe da kuma sabon yanayi, kuma muka rungumi sabuwar al’ada. Shekarunmu na farko a Amurka na da matukar wuya. Mun ga yadda iyayenmu ke shan wahala.
Sun yi iya kokarinsu wajen kare mu daga abubuwan da suke tsoro da kuma abubuwan da ke ba su takaici, yayin da suke rainon yara hudu, da kudi kadan a kasar da ba su saba da ita ba. Amma akwai lokutan da abubuwan za su iya taba mu.
Yara a sabuwar kasa
A matsayinmu na yara a sabuwar kasa, mun dubi yadda iyayenmu suka dukufa wajen biyan bukatunmu.
Hali da yanayi mai wahala da muka shaida na yadda iyayenmu suka bi kafin su yi nasara - da kuma hakuri da jajircewarsu - sun sa muma mun yi koyi da su har muka zama yadda muke a yau.
Mahaifinmu ya yi aiki a matsayin mai kula da gida, mahaifiyarmu ta zama mai aiki a cocin da ya dauki nauyinmu, suna wadannan ayyukan a lokacin da suke zuwa ajin koyon Ingilishi — abin da suka mayar da hankali a kai a ko wane lokaci — suna kula da mu.
Da suke fuskantar wadannan kalubalen ba su yanke kauna a kan burukansu ba. Sun kwashe shekaru, amma daga baya mahaifinmu ya samu shaidar digiri na biyu a fannin gudanarwa (Public Administration) kuma mahaifiyarmu ta fara aiki a matsayin ma’aikaciyar jinya.
Juriya a cikin jininmu take, Kwarewarmu wajen sanin hanyoyin warware matsaloli da zurfin tunani da kuma fatan alkhairi - wadanda halayen iyayenmu ne - sun bi mu yayin da muke girma.
Mun yanke shawarar barin inda iyayenmu suke a Rochester zuwa Los Angeles, kuma muka zama ‘yan kasuwa.
Kwarewa da gogewa
A wannan lokacin, mun zama Feven, gogaggiyar mai tsara gida, da Helena, shugabar gudanarwa ta kamfanin tallace-tallace da baiwa.
Duk da cewa wadannan ayyukan sun mana yawa, mun samar da kamfanin kayan kwalliya na 2•4•1.
"Two-four-one" ake kiran kamfanin, amma ya kara girma yayin da mutane a Rochester kan kalle mu su tambaya "Ku 'yan biyu ne?"
Bayan haka sai su yi tambayoyi irin “za ku iya tsayawa a gefen juna don na ga bambancin da ke tsakaninku?" ko kuma "Wace ce mai wayo kuma wace ce mai kirkin cikinku?"
Yayin da muke kara girma, tambayoyin da suke mana da wasa na kara ma’ana mai zurfi a zukatanmu. Sun sa muna tambayar kanmu, "me ya sa ba za ku zama halaye biyu masu karfi cikin daya ba?" Amsar ita ce, "Za ku iya rungumar duka biyu."
Saboda haka alamar kamfanin 2•4•1 manuniya ce ta imaninmu cewar mu din abu biyu ne a hade, kwakwalwa da kuma kyau - ba sai mun zabi daya mun bar dayan ba; za mu iya zama duka biyu.
A hanyarmu daga gabashin Afirka zuwa yammacin Amurka, mun fahimci cewar kalmomi tamkar sihiri suke idan aka yi amfani da su ta hanyar da ta dace. Muna kallon kwalliya a matsayin wata hanyar tunani mai zurfi.
Don labaran da mu kanmu ke bai wa kanmu na da karfi, sunayen da muke bai wa abubuwan da muke sayarwa da yadda muke bayyanawa sun kasance kayyadaddu da kuma masu bukatar tunani mai zurfi.
Abubuwan da muke sayarwa — masu suna kamar Role Model, Honor da kuma Class Act — abubuwa ne da ke bukatar tabbatarwa na kullum. Ba mu zo nan don bai wa mutane kwarin gwiwa ba kawai; muna so ya shiga zukatansu ne.
Daukar nauyi
Jim kadan bayan mun fara 2•4•1 a matsayin masu kamfani, mun ga yadda annobar korona ta zaftare iya yawan cinikinmu da kuma tattalin azriki gaba daya, kuma mun yi fargaba game da dorewar kamfanimu.
Amma ta hanyar shafukan sada zumunta, mun samu mun fahimci juna da abokan cinikinmu kuma mun gane halayensu.
Mun yi amfani da shafin sada zumunta na Instagram domin bajekolin kayayyakinmu tare da ba da labarinmu, mun kuma kara karfafa hulda da masu bibiyarmu.
Har mun samu mun ja hankalin wata muhimmiya - wata mai juyin juya hali, amma ta wata hanyar daban.
A gidajenmu da ke Los Angeles (wadanda rukunin gidaje uku ne kawai suka raba su), mun ajiye hotuna biyu iri daya kan teburinmu. Na daya ya nuna mu a matsayin yara mata, abin da a kullum ke tuna mana yarintarmu.
Yayin da muke kara girma kuma nauyi ke karuwa a kanmu, za mu iya manta mu su wane, kuma me muke wakilta. Amma wadannan ‘yan mata biyun cikin hoton nan suna tuna mana muhimman dabi’unmu da kuma abubuwan da suka fi muhimmanci a gare mu.
Hoto na biyu shi ne inda Oprah Winfrey take rike da kayan kamfanin 2•4•1.
Wannan wani hoto ne mai bayyana yadda muka cimma burinmu. Yadda wata mai fada a ji kuma wadda mutane ke girmamawa kamar Oprah, ta shaida mu a matsayin wadanda suka sauya duniya.
Hakan ya yi tasiri a kan kasuwancinmu yadda har yanzu muna tunani a kai.
A lokacin da ta gani kuma ta rungumi kayayyakin kamfaninmu, 2•4•1, Oprah ba ta san cewar littafinta mai suna 'What I Know for Sure’, ne ya karfafa mu wurin kirkiro wannan kamfanin ba.
Kuma muryarta da darrusan da ta koya mana ta hanyar littafin sun riga sun zama mana jagora a tafiyarmu ta kasuwanci.