Tasiri mafi girma da ‘yan Makerere suka yi ya faru ne a lokacin samu ‘yanci daga mulkin mallaka

Daga Jacob Katumusime

Wani labari da ba a tabbatar da sahihancinsa ba ya nuna cewa sunan Makerere ya samo asali ne a karni na 18 inda Kabaka (sarki) Ssemakokiro wanda yake tashi da sassafe daga fadarsa zuwa tsaunin da jami’ar take zaune domin ya je ya samu ganin Tafkin Nalubaale daga nesa.

Yadda ake kirari ga salon yadda tafkin yake burge Kabaka da sassafe a harshen Luganda shi ne ‘Kabaka ayagala kulaba mazzi makereere!’

Yayin da Kabaka ya dauke fadarsa daga wurin, tsaunin ya zama wurin tunawa da yadda tafkin ke burge shi ta hanyar daukar sunan Makereere.

Ko ma mene ne sarkin yake samu daga zuwa kallon tafkin da sanyin safiya, abun da za a iya fahimta shi ne duk abin da mutum yake so, dole mutum ya tashi da sassafe domin sa.

Tun da aka kafa jami’ar kan wannan tudun mai tarihi, mene ne jami’ar ke yi da sanyin safiya a kullum? Saurari yadda Mekerere take bayar da tarihin kanta a lokacin da ta cika shekara 100.

A lokacin da take bikin cika shekara 100 da kafuwa kwanan nan, Jami’ar Makerere ta tuna yadda sama da shekara 20 bayan kafuwarta ta fara bai wa mata gurbin karatu kuma ta sauya takenta daga ‘Bari mu zama maza’ zuwa ‘Mu yi gini don gobe’.

Cikin gomman shekarun da suka biyo baya, jam’iar tana dab da nuna wa duniya cewa za ta iya sauya duniyar da ke kewaye da ita.

Baya ga samar da gogaggun kwararru, Makerere ta samar da sama da shuwagabannin kasa biyar bayan an gama mulkin mallaka, ciki har da Mwalimu Julius K. Nyerere da Apollo Milton Obote da Benjamin Mkapa da Paul Kagame da Mwai Kibaki da kuma Joseph Kabila.

Daliban da Makerere ta yaye sun kafa tarihi ta hanyar nasara da kuma bala’i. Duk da haka Makerere, kamar yadda ko wace uwa take yi, tana alfahari da dukkan ‘ya’yanta.

Jami'ar Makarere ta yaye da dalibai da suka zama shugabannin kasashe ciki har da Paul Kagame/AA

Abubuwan da ‘yan Jami’ar Makerere suka bari a baya ba na wadanda suka kammala karatu daga jami’ar ba ne kawai, amma kamar yadda wakar jami’ar ta bayyana, na dukkan ‘wadanda suka bi ta kofofin Makerere ne.’

Tasiri mafi girma da ‘yan Makerere suka yi ya faru ne a lokacin samu ‘yanci daga mulkin mallaka da kuma bayan wannan lokacin inda jami’ar ta zama wata cibiya ta masu nazari da aka samu bayan mulkin mallaka.

A shekarar 1961, Rajat Neogy ya kafa mujallar Transition a Makerere. Mujallar ta zama wata kafa ta musayar ra’ayoyi inda aka yi renon gogaggun masana da ‘yan siyasa.

Mujallar ta samu mafi muhimmancin muryoyi daga ciki da wajen Afirka ciki har da Martin Luther King Jr, Nadine Gordimer da Wole Soyinka, wadanda suka samu lambar yabo na Nobel.

Bessie Head, Langstone Hughes da James Baldwin ma sun yi rubutu a mujallar.

Shi ya sa Makerere ta karbi bakuncin taron ‘marubutan Afirka masu rubutu da harshen Ingilishi’ a shekarar 1962, taron da ya hada manyan marubutan Afirka da marubuta masu tasowa a daki daya.

A nan ne Chinua Achebe ya hadu da James Ngugi, wani dalibi wanda daga baya ya sauya sunansa zuwa Ngugi wa Thiong’o.

Makerere ta nuna sadaukarwarta a kan lamarin al’adu da kuma kishin kasa na kin jinin mulkin mallaka.

Alal misali ta bai wa jagoran neman ‘yancin kai na kasar Kenya, Shugaba Jomo Kenyatta, digirin girmamawa a shekarar 1963.

Wadannan alaka da Makerere ke da su sun nuna muhimmancin jamiiar ga tafiyar kishin Afirka.

Makerere ta taka rawar gani a matsayinta na abar alfaharin Afirka. Za ka iya jin wakokin yabo irin su ‘Makerere ita kadai ce jam’ia da ke yamma da Tekun Indiya, Kudu da Sahara, arewa da Limpopo kuma gabar da Congo.’

Wadanda suka yi karatu a Makerere suna yawan alfahari da cewa a Uganda, Makerere ne tsaunin da ya fi yawan masu kwakwalwa a wuri daya.

Zama gagarabadau

Bugu da kari, a fagen musayar ra’ayi Makerere lamiri ne na jami’a – idan aka ambaci ‘Makerere’ kuma aka kara ‘jami’a’ a kai, maimaici ne. Ta yaya Makerere ta iya yin abin da ya kamata don sauya duniyar da muka gada?

A cikin shekarun 1960, masu mu’amala da Makerere, malamanta da daliban da ta yaye da kuma daliban da ke karatu a jami’ar suka zama gagarabadau.

Okot p’Bitek ya katse al’adar adabi ta mulkin mallaka yayin da ya wallafa wakokin adabin Afirka, musamman Song of Lawino.

Hoto a nan

Ngugi wa Thiong’o da ire-irensu sun tayar da hankali a jami’o’i a Afirka da gangamin neman a soke fannonin koyan Ingilishi.

Da p’Bitek da Ngugi daga baya za su zo su nemi mayar da jami’o’i cikin jama’a ta hanyar shirya bukukuwan al’adu da kuma wasan kwaikwayo a fili cikin Uganda da Kenya.

A kasar Tanzaniya, Nyerere yana warware rarrabuwan al’umma da mulkin mallaka ya yi tare da samar da manufar daidaito tsakanin ‘yan kasa.

Daliban Makerere sun kasance suna shirya zanga-zangar kin jinin mulkin wariyar launin fata, kin jinin Amurka da kuma sauran zanga-zangar kin jinin tsarin mulkin da bai yarda da saba wa ra’ayin mai mulkin kama-karya ba.

Jami’ar, wadda gwamnati ce ta samar da ita ta kusa zama wata kafa wadda ke fitar da sabon tunani na gwamnati.

Duk da haka, masani a Makerere Ali Mazrui, bai yarda da wannan hali na jami’ar ba.

Ya ce a kokarinta na ba da amsa ga lamuran siyasa da zamantakewa da suka fi kusa da ita, jami’ar ba ta mayar da hankali kan muhimman manufofi na bai daya da sauran jami’o’i da kuma inganci.

Walter Rodney a jami’ar Dar Es Salaam ya hakikance a kan muhimmancin jami’a ga inda take.

Idan Mazrui ya yi shakka kan ra’ayin Rodney na muhimmancin masu ilimi na jami’a, sake farfadowar kama-karya na gwamnati bayan mulkin mallaka bai bar wa masana na jami’o’i zabi ba, sai dai su shiga fagen siyasa. .

Shekarun 1970 da 1980 sun tura kasar Uganda cikin hargitsi. Al’adun masana da ke tasowa daga Jami’ar Makerere sun samu koma baya.

Korar da Idi Amin Dada ya yi wa ‘yan nahiyar Asiya ta hada da wasu masana.

Yawancin mutanen Makerere sun tafi gudun hijira ko kuma an kashe su a hargitsin da ya biyo baya.

Bukukuwan cika shekara 100 na Jami’ar Makerere sun tuna da wannan tarihi ta hanyar shirya tarukan gabatar da jawabai da lacca.

An karrama shugaban Jami’ar Makerere, Frank Kalimuzo, wanda ya bace a lokacin mulkin Idi Amin ta hanyar rada wa babban dakin koyarwa na jami’ar sunansa.

An kuma rada wa wani babban dakin koyarwar jami’ar sunan Yusuf K. Lule, dan Afirka na farko da ya kasance shugaban Jami’ar Makerere, kuma shugaban Uganda na wucin gadi bayan an kawar da gwamnatin Amin.

Kishin kasa

Yawancin mutanen Makerere sun samu kansu a cikin yakin neman ‘yanci kuma ba da jimawa ba karin mutane sun samu kansu cikin aiki sake gina kasa.

Jami’ar ta fara ganewa cewar ba za ta iya rayuwa cikin fanko ba.

Dole al’adar ilimin jami’a bayan samun ‘yancin kai ta hada inganci da yin abin ya dace da inda jami’ar take.

Babu wata kira ga yin abin da ya dace da inda jami’ar take kamar harin sauyin jari-hujja wanda ya mayar da jami’ar kasuwanci.

Makerere ta kasance abu na farko da ta fara mutuwa a tsarin mayar da karatun jami’a hannun ‘yan kasuwa.

Jami’ar ta ba da gurbin karatu ga dalibai fiye da iya wadanda za ta iya koyarwa, kuma fannonin da ba za su iya bai wa isassun dalibai gurbin karatu ba sun zama kwararrun kamfanoni masu ba da shawara don neman kudi.

Mahmood Mamdani ya takaita wannan matsalar cikin (littafinsa) Scholars In the Marketplace.

Kasuwannin Ugandan sun fi yiwuwar kamawa da wuta. Babban ginin da aka fi sanin Makerere da shi ma ya kama da wuta kuma a lokacin da jami’ar take murnar cika shekara 100 ana kan sake gina ginin.

Amma Makerere na koyon darasin cewar kudin makaranta kadai bai isa gudanar da jami’a ba kuma saboda haka ta yi amfani da bikin cikanta shekara 100 wajen farfado da asusun da za a yi ta juyawa don taimaka wajen ba da karatu mai zurfi.

Duk da haka, a kwai yanayi na mantuwa a kan Makerere.

Jami’ar ta cigaba da manta yanayi na kawar da mulkin mallaka wadda ta bai wa gagarumar gudumawa.

Cikin dukkan shahararrun shuwagabannin kasa da Makerere ta samar bayan mulkin mallaka, babu wanda ya daga tutar kawar da mulkin mallaka da Nyerere ya hada.

Wasu bangarorin cikin jami’ar har yanzu ba su gane abuabuwa da tsarin digirin hadin gwiwa na fannoni mambabobinta (interdisciplinary MPhil/PhD) da ya tsara tare da cibiyar nazarin zamantakewa na Jami’ar Makerere (Makerere Institute of Social Research, MISR) ba.

A kokarinsa na sake fasalin MISR, Mamdani ya nemi ya barranta daga irin tsarin karantarwar yammacin duniya da kuma tsarin karantarwar mulkin mallaka da tsadar karatu mai zurfi da kuma lalacin aikin kwararru da masu ba da shawara da kuma yanayin kaka-ni-ka-yi na bincike.

Yana da fatan horar da sabbin masu bincike da masana masu kawar da mulkin mallaka.

‘Yan fannonin da suka dauki tsarin karatu na hadin gwiwa a Jami’ar Makerere na yi ne don kara wa tsarin karatunsu dandano, ba tare da tabbatar da sauya tsarin manhajar ko kuma sauya fasalin fannonin karatu ba.

Saura da dama kuma suna amfani da maganar kawar da tasirin mulkin mallaka ne tamkar wata waka da ta shahara.

A daidai lokacin da jami’ar take bikin cika shekara 100 da kafuwa, ta cigaba da mantawa da kason matan Makerere da aka kashe duk da cewa taurarinsu sun bayyana.

An kashe Dr. Theresa Nanziri Bukenya, wata masaniyar lissafi kuma shugabar masaukin dalibai ta Jami’ar Makerere mai suna Africa Hall, don ta kalubalanci zaluncin sojojin Amin, amma ba a ba da labarinta ba a wajen bukukuwan.

Duk da cewa wasu matan kamar Dr. Specioza Wandira Kazibwe, wadda ta samu ta zama mace ta farko da ta rike mukamin mataimakin shugaban kasa a Afirka, sun taka rawar gani.

A lokacin da Makerere ta yabi Sarah Ntiro, tsohuwar dalibar da ta zama wadda ta fara kammala karatu a Jami’ar Oxford a Afirka ta Gabas da ta Tsakiya, jami’ar ta manta da gwagwarmayarta ta neman tabbatar da mutuncinta a matsayinta na ‘yar adam, ba na mace ba kawai.

Yayin da Makerere ta nemi ta tsaya kan tunawa da nasarorinta don suranta yadda duniya za ta kasance a gaba, ta mance da darrusan gwagwarmayarta.

Makerere wadda aka gina kan sadaukar da kai na al’umma ta yi murnar cika shekara 100 da kafuwa da kewaye filin jami’ar da ganuwa tamkar tana kore al’ummar da ta ba da tsaunin daga shige ta.

A cikin wannan ganuwar Makerere da ta kai shekara 100, za a yi fatan cewar za a iya samun farfadowar al’adar ilimi wadda za ta mayar da hankali kan abun da ke faruwa a lokacinta.

Yadda karfin kafafen sadarwa na intanet irin su TRT Afrika ke karuwa, ana fatan mutanen Makerere za su iya ta tashi da sassafe kuma su yi iya kokarinsu don sauya fasalin al’umma.

TRT Afrika