Tun bayan fara rikicin a watan Oktoba an kashe Falasdinawa sama da 18,000. Hoto: AA

Daga Charles Mgbolu

Labarin rayuwa a Gaza ba shi da dadin ji inda mutane da dama ke rayuwa a sansanoni budaddu, ga rashin isasshen abinci da ruwan sha.

Isra'ila ta kashe kusan Falasdinawa 20,000 tun 7 ga Oktoba, kuma mafi yawan wadanda ta kashe mata da yara kanana ne.

Wadanda suka tsira na amfani da kiraruwa wajen dafa abinci. Hoto: AA

Idan dare ya yi, yanayi na yin sanyi sosai, da asuba mutane na farkawa cikin dimauta da yadda za su rayu zuwa yammaci.

Suna amfani da murhun duwatsu wajen dafa abinci da gasa burodi. SUna kuma amfani da wannan dama wajen jin dumi.

Da yawan motocin kayan agaji ba s aiya zuwa yankunan. Hoto AA

Busassun ciyawa da kirare ne suke amfani da su a matsayin mai na girki, kuma girkin ba ya sauri, amma kuma babu wani zabi da ya wuce wannan din, saboda an riga an kaste bayar da lantarki da man fetur a yankin.

Samun garin fulawar da za a yi burodi da shi ma na wahala sosai a kowacce rana.

Wasu Falasdinawan sun koma bara suna rokar abinci. Hoto: AA

'Yan jaridu da ke yankin sun ce motocin dakon kayan agaji ba sa iya zuwa yankin d ka yi wa ruwan bama-bamai inda mafi yawan jama'a suka koma bara da rokon burodi.

Har yanzu mutane na tattaunawa, a koyaushe sannan yara kanana na yin murmushin karfin hali.

An mayar da yunwa wani babban makami a yakin, Falasdina na bukatar juriya sosai don iya ci gaba da rayuwa.

TRT Afrika