Babatunde wanda yake da mabiya sama da 300,000 a shafinsa na Instagram, ya samar da wata duniya wadda ke saka mutane cikin mamaki / Hoto Babs Cadini Twitter

Daga Charles Mgbolu

Matasa ne daga nahiyar Afirka wadanda akasarinsu suke tsakiyar shekarunsu na 20, da suke yin wani abu da Michael Caine a cikin fim din ‘The Prestige’ ya alakanta da “daukar wani abu a tsurarsa ka sa ya zama wani abin ban mamaki”.

Suna tsayawa gan ‘yan kallo domin yin wasa inda suke tattaro duka basirarsu don yin wani abu da zai burge 'yan kallo su yi ta ihu da tafi.

Siddabaru irin wannan ya zama abin magana a nahiyar sakamakon irin wadannan matasan 'yan Afirka da suka fito da irin wannan sabuwar hanyar nishadin.

A kasashen yamma, shahararrun masu rufa-ido kamar su Dynamo da David Copperfield da Paul Daniels da David Blaine na jan zarensu a kafafen sada zumunta.

A yanzu matasa daga Afirka sun soma kaurin suna inda suke amfani da zamani da kuma karfin kafafen sada zumunta domin samar wa mutane abin da zai sa su saki baki, TRT Afrika ta tattauna da wasu matasa biyar masu siddabaru.

Babatunde wanda yake da mabiya sama da 300,000 a shafinsa na Instagram, ya samar da wata duniya wadda ke saka mutane cikin mamaki.

Ya sha yin wasa ga manyan mawaka da kuma kai tsaye a talabijin wanda a kullum yana barin 'yan kallo cikin shauki da mamaki.

Babs Cardini (Nijeriya)

Babatunde Kasumu Tinubu wanda aka fi sani da Babs Cardini, dan jihar Legas ne kuma shekararsa 23, wanda ya fi kaurin suna wurin siddabaru a Nijeriya a kafafen watsa labarai na kasar da kuma na waje.

“Tun dama ina so na zama mai rufa-ido. Na san wannan shi ne abin da ya dace da ni tun ina da shekara biyar. Masoyana sun fi sanina da mai siddabaru na kan titi,” in ji shi.

A wani bidiyo wanda ya karade shafukan sada zumunta wanda akwai mawakan Nijeriya a ciki irin su Davido da Mayorkun, an ga Babs yana wani siddabaru inda aka ga Davido yana jin ana taba masa kafada, amma shi kuma Babs kafadar Mayorkun yake tabawa. Wannan ya sa duka mawakan suka rinka ihu cikin jin dadi.

“Rufa-ido yana da wani karfi da zai iya kawo sauki ga kowane irin yanayi mutum yake ciki. Irin wannan yanayin nake son kawowa.

Irin wannan kyautar nake son bai wa kowa musamman matasa 'yan Afrika wadanda suke fama da matsaloli da dama a yanzu,” in ji Babs wanda ya yi zarra bayan ya kammala wasa a zagayen kusa da na karshe a gasar nuna basira ta kasa a Legas.

Mwesigwa Jonathan (Uganda)

An taba yi wa Mwesigwa Jonathan siddabaru a lokacin da yake dan shekara 16.

Ya soma yin nasa rufa-idon a kan titi inda yake bin sahun dan rufa-idon nan na Amurka Criss Angel, inda a halin yanzu Mwesigwa mai shekara 23 ya samu ya fito da irin nasa siddabarun da kuma zama daya daga cikin wadanda suka yi fice ta bangaren wannan harka a Uganda.

“Ina kallon Criss Angel yana dabonsa a talabijin inda nake so na kwaikwaye shi. Zama mai rufa-ido a gare ni ya kasance wani babban mataki na daukaka. Ina so na zama wani wanda zai zama allon kwaikwayo ga matasa,” kamar yadda Jonathan ya shaida wa TRT Afrika.

Siddabaru wani abu ne da bai yi suna ba a Uganda, sai dai Jonathan a halin yanzu na baje kolinsa inda yake wasa ga manyan kungiyoyin kasa da kasa kuma ake nuna shi a kafafen watsa labarai na kasar.

“Ba ni da wani tasiri a kafafen sada zumunta amma na soma jan hankalin mutane. Akwai matasa da dama da suke kallon bidiyoyina suke turo mani sako kai tsaye inda suke bayyana yadda nake karfafa musu gwiwa.

"Mutanen da suke siddabaru a nan a baya a kan titi ba sa yin abin yadda ya kamata. Suna shiga ta dauɗa da kuma fito da siddabaru a matsayin wani abu mara kyau, kuma na shaidanci bayan ba haka ba ne,” kamar yadda ya yi bayani.

“Wannan ya yi tasiri kan yadda mutane ke kallo da kuma mu’amala da masu rufa-ido, kuma ina yin iya kokarina domin ganin na sauya matsayar mutane kan wannan lamari.

Ba abu ba ne mai sauki, amma ina da yakinin zan yi aiki sosai kan wannan aikin nawa domin sauya tunanin jama’a.” Jonathan yana da burin zuwa hedikwatar 'yan siddabaru.

“Ina so wata rana na yi wasa a Las Vegas. Nan ne hedikwatar rufa-ido. A ranar ce babban burina zai cika,” in ji shi.

Bernard Badu Arkoh (Ghana)

Ba kamar Jonathan ba, Bernard Badu Arkoh mai shekara 27 wanda masoyansa suka fi kira da Benard mai siddabaru, ba wai yana da wani da yake kwaikwayo ba ne a waje, ya samu siddabarun ne tun a gida.

“Mahaifina dan rufa-ido ne. Gadonsa na yi saboda ba na so na manta da shi…saboda a kullum yana ba ni karfin gwiwa. Ina so kullum ya zama abin alfahari,” kamar yadda Bernard ya shaida wa TRT Afrika.

Bernard, wanda injiniyan lantarki ne daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah, ya kammala karatunsa a 2018 inda ya soma koyarwa a matsayin mataimakin malami a jami’ar kafin ya yi gaba a sana’arsa ta rufa-ido.

Bernard ya soma wannan siddabaru a matsayin kwararre a 2018, kafin nan a makaranta kawai yake nasa wasan.

Benard ya yi kokari tun da ya soma wannan sana’a, inda ya ja hankalin manyan mutane ciki har da mataimakin shugaban Ghana.

“Ina so na yi wasa a lokacin Gasar Cin Kofin Duniya. Wannan ne babban burina,” in ji matashin dan siddabarun wanda yake da gwanaye ta wannan fanni da suka hada da David Copperfield da David Blaine da JS Magic.

Kelvin Kimotho (Kenya)

Kelvin Kimotho wanda aka fi sani da K Magician shi ne a halin yanzu ya lashe gasar nuna basira ta Talanta Mtaani da aka gudanar a Kenya.

Ya shafe shekara 13 yana siddabaru. “Na soma son siddabaru bayan na ga David Blaine yana wasa a talabijin,” kamar yadda Kelvin mai shekara 24 ya shaida wa TRT Afrika.

A lokacin da yana yaro, an gano cewa Kelvin yana da wata larura wadda ke sa yara su kasa mayar da hankali.

“Zama wanda yake siddabaru ya taimaka mini yaki da alamomin larurorin da nake fama da su da dama. Wannan ya taimaka mini kwarai da gaske a lokacin da na soma siddabaruna," in ji shi.

A halin yanzu Kelvin ya zama sananne a Kenya wanda yake da fasaha ta musamman ta siddabaru da karta ko kuma kati.

Anotidaishe Chikaka (Zimbabwe)

Yana da shekara 23 kuma ya shafe shekara biyar yana yin siddabaru na ban mamaki ga ‘yan kallo a Zimbabwe.

Anotidaishe Chikaka wanda aka fi sani da Vortex, ya kasance mawakin gambara kuma an zabe shi a matsayin wanda ya fi taimaka wa wurin bayar da gudunmawa a gambara a bikin bayar da kyaututuka ta Zimbabwe, wato Changamire wadda ake yi duk shekara.

Vortex kuma ya yi suna matuka wurin irin wasannin da yake yi a kan layi, kuma irin bidiyoyin da yake yi sun sha karade shafukan sada zumunta a lokuta da dama.

“Ina yin haka ne domin ina so mutane su ji dadi su yi murmushi. Ba wai ina yin haka ba ne don neman suna,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Kamar sauran masu rufa-ido, Vortex ya samu kwarin gwiwarsa ne daga wadanda suka fi kwarewa a wannan harka. Shin Lim da Spidey sun ja hankalinsa matuka.

“Rufa ido har yanzu harka ce mai tasowa a Zimbabwe amma na ji dadi ina cikin wadanda suke mayar da hankali domin bai wa harkar alkibla domin karfafa gwiwar masu tasowa da kuma wadanda suke so su yi rufa-ido,” in ji shi.

TRT Afrika