Daga Mary Mundeya
Rayuwa ta canja wa Loveness Mainato bayan da ta haifi zabiya, mai kuma fama da cutar autism da farfadiya a shekarar 1999.
Mainato ta ce ta shiga mawuyacin hali saboda tsangwamar da ta rika fuskanta daga danginta da kuma al'umma don lalurorin da yarinyar da ta haifa take da su.
"Ina shiga damuwa sosai, saboda mutanen da nake kallo muna tare sun juya min baya. Mijina ya guje ni hakazalika al'umma ta juya min baya," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Zabiya ciwo ne da yake shafar fatar mutum da gashinsa da kuma idonsa, hakan yana faruwa ne saboda rashin isasshen sinadarin melanin a fatarsu.
A wasu lokuta zabiya sukan yi fama da matsalar gani da saurin kamuwa da cututtukan fata da hadarin kamuwa sa cutar kansa.
Kamar yadda wani rahoto na Hukumar Kididdiga ta kasar Zimbabwe a shekarar 2022 ya bayyana akwai zabiya 9,753 da ke rayuwa a kasar.
Akwai canfe-canfe da dama da ake jifan zabiya da su a Zimbabwe da wasu kasashe da ke yankin wanda hakan yake jawo musu tsangwama da kuma wariya saboda lalurar da suke tattare da ita.
"Wasu suna cewa laifi na yi wa Ubangiji shi Ya sa yake ladaftar da ni. Wasu suna kiran mayya ko kuma karuwa," in ji Mainato.
Mainato, mai shekara 50, ta ce saboda mawuyacin halin da ta shiga sai da ta kwashe tsawon wata daya a asibiti tana karbar magani.
Yayin da take kokarin mayar da komai ba komai ba, bayan haihuwar ta farko a karshen shekarun 1990, sai kuma ta sake haihuwar zabiya a shekarar 2007.
Wannan ya jawo mata babbar matsala a rayuwar aurenta. Mijinta ya guje ta ya barta da 'ya'yan, ya koma makwabciyar kasarsu wato Botswana da zama.
Mainato ta ce wannan ya kara jefa aurenta cikin babbar matsala. Saboda canfe-canfen da ake dangantawa da zabiya a Zimbabwe, zabiya da iyayensu mata suna fuskantar tsangwama.
Daga wacce ta fada matsala zuwa mai ba da taimako
Duk da wannan mawuyacin halin da ta shiga, Mainato ba ta karaya ba. Ta jajirce don taimakon kanta da kuma wasu masu irin matsalar.
Ta kafa kungiya wadda ta sanya wa suna Albino Charity Organisation of Zimbabwe, inda take kula da fiye da yara zabiya 50.
"Bayan da aka sallame mu daga asibiti da taimakon mahaifiyata da 'yan uwana na yi karbi kaddarar da Ubangiji ya jarabe ni da ita, watakila Yana so na zama uwar zabiya ne," in ji ta.
Mainato ta ce ta fahimci magungunan kula da fata da zabiya ke bukata suna da tsada kuma galibin iyaye ba su da karfin saya.
Ta ce zabiya suna bukatar kula ta musamman don kare fatarsu da su mayuka kuma suna fuskantar kalubale lafiya kamar hadarin kamuwa da kansa.
"Wannan ya sa yawancin iyaye suke shan wuya kafin su karbi kaddamar samun 'ya'ya zabiya amma sai na cewa kaina wannan ita ce rayuwata kuma babu wani abu da zan iya yi na canja haka," in ji Mainato.
Kungiyarta Albino Charity Organisation of Zimbabwe, wadda aka kafa a shekarar 2010, tana bayar da horo da darussa kan yadda za a kula da zabiya da kuma batutuwan kare hakkin masu fama da lalurar.
'An rika zagin mahaifiyata'
Kungiyar da Mainato ta kafa tana garin Chitungwiza a lardin Harare. Tana samun kudin gudanarwarta ne daga gudunmuwar da mutane suke bayarwa - wadanda ake amfani da su wajen shirya horo da biyan kudin makarantar yaran - 15 daga cikinsu suna zaune ofishin kungiyar.
Ana bai wa zabiya horo a bangarori da dama kamar kiwon kaji da yin kek. "Bai dace a ce iyayen yara zabiya suna kin rungumar kaddara dangane da lalurar da ke tattered da 'ya'yansu," in ji Mainato.
"Yawancin yara suna bukatar kulawa da kariya. Fahimtar yadda al'umma take kallon zabiya, hakan ya sa yawancin yaran sun gwammace su zauna a wajenmu madadin su zauna a gidajen iyeyensu saboda kwanciyar hankali," in ji ta.
Kamar yadda ta ce, yara zabiya suna fuskantar tsangwama daga mutanen gidansu ta ce " 'yan kalilan ne daga cikinsu suke samun kulawa a gida."
Wasu daga cikin ma'aikatan kungiyar su ma zabiya ne ciki har da Zvidzai Juma wacce ta ce tana tuna yadda aka rika tsangwamarta da mahaifiyarta.
“La'akari da kalubalen da na fuskanta lokacin ina yarinya, na fuskanci matsaloli iri-iri musamman mahaifiyata wacce wasu suka rika zagi a kowane lokaci," kamar yadda ta bayyana wa TRT Afrika.
Juma ta yi amannar cewa kungiyarsu tana taimakawa wajen magance wasu matsaloli da zabiya musamman yara ta fuskar iliminsu da daukar nauyinsu da kuma kare hakkinsu.
Samun farin ciki da annashuwa
Daya daga cikin wadanda suka amfana daga ayyukan kungiyar Albino Charity Organisation of Zimbabwe ita ce Nyaradzo Kusekwa.
"Abin da kawai na sani shi ne na fara zama da ita lokacin da nake da shekara biyar a duniya kuma Misis Mainato ta zama kamar uwa a gare ni," in ji Kusekwa.
Yarinyar tana farin ciki saboda yanzu tana yin karatu."Yanzu ina aji bakwai a makarantar firamare. Babu wani abu da zan ce ina korafi a kansa," kamar yadda ta bayyana wa TRT Afrika.
Ta ce cibiyar da kungiyar ta samar ya zamar mata tankar gidansu " wani waje da muke dariya da nuna farin cikinmu ba tare da an yi la'akari da fatar jikinmu ba."
Sai dai Kusekwa ta ce har yanzu tana fuskantar tsangwama a makaranta daga dalibai wadanda suke yin nesa-nesa da ita.
Ta hakan ba zai sa ta ta karaya ba, "Ina karatu sosai da fatan zama injiniya wata rana," in ji Kusekwa.
Ko da yake ayyukan kungiyoyi kamar na Albino Charity Organisation of Zimbabwe suna tasiri sosai wajen inganta rayuwar zabiya, Mainato ta ce ya kamata a kara wayar da kan iyalai da al'umma gaba daya kan kawo karshen tsangwamar da ake nuna wa zabiya.