Daga Kudra Maliro
A fadin yankin Kudancin Afirka inda zabiyoyi ke fuskantar tarin ƙalubale da suka haɗa da kai musu hari, an gudanar da gasar kyau ta zabiyoyin, wani lamari da ya samar da damar sauya tunanin mutane da dama a kan yadda suke kallon masu wannan lalura.
An gudanar da gasar kyau ta maza da mata na zabiya a Harare, babban birnin ƙasar Zimbabwe a wannan watan, inda mutum 18 suka yi takara daga ƙasashen Afirka ta Kudu da Zambiya da Mozambique da Malawi da Angola da kuma Tanzania.
Ƴar ƙasar Angola Andreia Solange Sicato Muhitu ce ta yi nasara a gasar kyau ta mata ta zabiya ta Kudancin Afirka, yayin da ɗan Zimbabwe Ntandoyenkosi Mnkandla ya lashe kyautar ta fannin maza.
Muhitu mai shekara 28 tana aiki ne a matsayin shugabar sashen yawon buɗe ido a gudnumar Cuando Cubango da ke kudu masi gabashin Angola, ta kuma ce ta sha shiga gasannin kyau a ƙasarta tun tana ƴar matashiya, ta kuma yi nasarar lashe wasu daga ciki.
Amma babu wacce ta sanya ta samun gamsuwa kamar wannan ta yankin Kudancin Afirka da aka yi.
"Zan iya zama abar koyi ga ƴan mata da dama, musamman masu lalurar zabiya, don su saki jiki da jin cewa su kyawawa ne a yadda suke," in ji Muhitu. "Wannan shi ne ƙwaƙƙwaran saƙon da muke fatan aikewa."
An shirya gasar ne da nufin bai wa zabiyoyi ƙwarin gwiwar cewa kyawawa ne su da kuma taimaka musu wajen cimma muradunsu. Waɗanda suka yi gasar sun haɗa da masu kwalliya da ma'aikatan lafiya da kuma ƙwararrun masu tallan kayan ƙawa.
A lokacin da suke kaɗa tutocin ƙasarsu, sun nishaɗantar da masu kallo da waƙoƙi da ƙasidu da kuma raye-raye.
Sun yi fareti a cikin yanayi na ƙasaita cikin kayayyakin aikinsu, da rigunan shan iska da suturun Afirka da aka yi da fatun dabbobi, kafin daga bisani su amsa tamboyi daga tawagar alkalai a kan al'amuran da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki.
An zaɓi ƴan takarar ne bisa ga duba kwarjininsu da ƙwarin gwiwarsu da salon yangarsu da kuma basirarsu.
Waɗanda suka yi nasarar sun kuma samu kyautar kuɗaɗe lakadan da kambi da kuma furanni. Ita kuwa wacce ta zo ta ɗaya ta samu kyautar dala 250.
Akwai zabiya sosai a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka, inda ake samun guda ɗaya a duk cikin mutum 5,000, a cewar alkaluman MDD.
Yawansu ya kai samun mutum ɗaya a cikin duk mutum 1,000 a Zimbabwe da sauran yankin Kudancin Afirka, idan aka kwatanta da mutum 1 cikin 17,000 ko 20,000 da ake samun su a yankin Arewacin Amurka da Turai.
"Wannan kambin ya ba ni damar yin wani abu na daban ga rayuwar zabiyoyi ta wata hanya da ban taɓa zato ba, ba a ƙasata ba kawai har ma a yankina baki ɗaya. Ba na jin kunya, na ji cewa an ƙara min azama," Ms Muhitu ta ƙarƙare da cewa.