Precious Marange tana buga wasan ƙwallon Rugby da kurket ga kungiyoyin kasar Zimbabwe. Hoto: Precious Marange  

Daga Pauline Odhiambo

Precious Marange tana aiki a matsayin 'yar aikin gida a Zimbabwe lokacin da ta fara kallon wasan kurket a akwatin talabijin mai baƙi da fari a gidan da take aiki.

Wasan wanda ya kunshi 'yan wasa 22 da suka bazu a wani irin yanayi mai ɗaukar hankali da ban sha'awa, yanayin da ya matukar birge Precious ganin irin rawar da suke takawa a cikin kowane minti.

Makonni kadan bayan haka, wata damar buga wasan kurket a Harare babban birnin kasar Zimbabwe ta samu, tun daga lokacin Precious ba ta daina buga wasan ba.

"Ina hanyar wucewa ta kungiyar wasan kurket taTakashinga a shekarar 2004, sai na ji zuciyata ta raya min na shiga in gwada wasan," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

"Na samu nasara a kan masu horar da 'yan wasan, kuma tun daga wannan lokacin ake fafatawa da ni a wasan," in ji ta.

Takashinga na daya daga cikin kungiyoyin wasan kurket na bakaken fata na farko a Zimbabwe kuma matattarar manyan 'yan wasan kasar.

A lokuta da dama, Precious kan sulale zuwa kulob din don yin atisaye kafin ta gaggauta komawa aikinta na aikatau da take yi a unguwar Harare Highfield.

"Babban hutun da na samu na farko ya zo ne a shekara ta 2006 lokacin da na samu damar tafiya tare da 'yan wasan kurket zuwa Botswana da kuma wasan share fage na Afirka a wannan shekarar," a cewar 'yar wasan.

Tana mai cewa "Na hau jirgina na farko zuwa ƙasar Afirka ta Kudu don buga wasa da Pakistan a shekarar 2008."

Precious ta soma buga wasan ƙwallon cricket ne a shekarar 2004. Hoto: Marange

Babbar 'yar wasa

A lokacin da wata abokiyar wasan ta ba da shawarar cewa Precious ta gwada buga wasan rugby, ba ta taba tunanin yin fice a wani sabon wasa ba, sai gashi a ƙarshe ta samu matsayin ƙwararriya a fannin wasannin.

''Dole ne na kula da motsa jiki a kowane lokaci don na ci gaba da buga wasan kurket da rugby,'' in ji ta.

"Na kasance cikin kuzahari ta hanyar horarwa da motsa jiki don inganta saurina da kuma ƙarfin zuciya, da ƙarfi a filin."

Dabi'u da ƙa'idojin aikinta sun bai wa Precious dama ba kawai ta buga wasan kurket da rugby ga kasarta ba har ma da zama kyaftin din kungiyoyin kasa a wasanni biyu.

Aikin da Precious mai shekaru 41 ke yi a ko da yaushe ya ƙunshi tashi da misalin karfe 5 na safe don motsa jiki kafin ta je aikinta da take zuwa kullum a masana'antar ƙarafa da misalin karfe 7.30 na safe.

Duk da nasarar da ta samu a fagen wasan rugby da kurket, Precious tana daraja aikinta a masana'antar ƙarafa da take zuwa saboda yana taimaka mata wajen tallafa wa ɗanta mai shekaru 12 da sauran danginta na kusa a rayuwa.

''A ko yaushe Ina samarwa iyalina da wassanin da nake bugawa lokaci. Ɗana yana jin dadi saboda ya san cewa mahaifiyarsa tana iya ƙokarinta domin ganin ta ba shi rayuwa mai kyau,'' in ji Precious wadda ke tallafa wa wasu 'yan uwanta mutum biyar.

''Ina kokarin ganin na kula da kowa, duk da cewa ba lalle ne kudadensu isa ba yin komai ba.''

Precious mai shekaru 41, ta zama abar koyi da alfahari ga sauran matasa 'yan wasa. Hoto: Precious Marange

Abar koyi

Precious tana mai godiya ga waɗanda suka da ɗauke ta aiki da kuma shugabannin masana’antar da take aiki, wadanda suke taimaka mata ta hanyar ba ta hutu daga aiki don ci gaba da sana'anta a fannin wasanni.

"Shugabannina tamkar iyayena suke, suna bani goyon baya a kan komai. Sun fahimci irin girman sadaukarwar da cikin wakilci wa Zimbabwe a gasar Rugby da kuma kurket," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Yayin da wasannin mata a Zimbabwe ke samun karbuwa, da alama nasarar da Precious ta samu na kara zaburar da wasu da dama don kokarin shiga fagen da 'yan wasa maza suka mamaye.

A matsayinta na ɗaya daga cikin manyan ƴan wasa a ƙungiyoyin biyu, ana ɗaukar Precious a matsayin abin koyi ga ƙanana ƴan wasan da ke da wurin samun ci gaba na a matakin ƙasashen duniya.

Babban burinta shi ne ta fara makarantar koyar da wasanni inda mata 'yan shekaru daban-daban kuma daga wurare daban-daban za su sami damar yin fice a wasannin da suka zaba.

"Kowace mace na iya buga wasan da ake gannin maza ne kawai za su iya bugawa," a cewar Precious "Shekaru lamba ce kawai, kuma babu abin da ba zai taɓa yiwu ba."

TRT Afrika