Daga Charles Mgbolu
Wasu mutanen na kyamar ganin gwangwanayen lemo ko kayan abinci idan aka zubar da su a shara, amma a wajen Chibuike Ifedilichukwu, mai shekaru 37, wannan wata babbar dama ce!
Ifedilichukwu dan asalin yankin kudu maso-yammacin Nijeriya, yana kirkirar abubuwa da dama ta hanyar amfani da gwangwanayen kayan sha ko na ci.
Yana sanye da safar hannu baka mai kauri, ga alkalami a hannunsa, Ifedilichukwu ya yanka tare da nannade gwangwanin kamar wani maciji inda har sai da ya sauya kama.
Kara daraja
Ya ce "A kowacce rana ana zubar da shara da aka samar daga ayyukan masana'atun da daidaikun jama'a ba tare da tunanin tasirin hakan ga zamantakewa ba. Hakan ya sanya na zabi hanyar tattara gwangwanayen da aka zubar a shara ina kara musu daraja, abin da nake kira 'kirkira da kara daraja'."
Goran-ruwa na daya daga cikin karafa da ba sa cutar da muhalli , saboda yadda yake da sauki wajen sake sarrafawa. Amma kuma, suna da tasu illar idan ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba.
Zubar da gwangwanaye da suaran kayan da aka yi da goran-ruwa na gurbata kasa da ruwa. Kona goran-ruwa kuma na fitar da hayaki mai guba da ke gurbata iskar da ake shaka.
Sake sarrafa goran-ruwa na taimaka wa wajen rage yawan dattin da ake zubarwa a kasa sannan yana taimakawa wajen tsare ma'adanan karkashin kasa, in ji Hukumar Kare Muhalli ta Amurka.
Tarin bola
Ifedilichukwu na son zane-zanensa su cimma manufofi biyu: samar da surori masu kyau da kayatarwa, sannan su bayar da gudunmawa wajen kare muhalli.
Koyo da kwarewa wajen gudanar da ayyukansa wata babbar dama ce. Ya yi godiya ga kakarsa, wadda ya taso a hannunta, wadda kuma a karkashin kulawarta ne ya koyi saka tabarma da ganye.
Nijeriya na tara shara kimanin tan miliyan 32 a kowacce shekara. Amma kadan daga ciki ne kamfanoni suke sake sarrafa su.
Ifedilichukwu ya bayyana cewa yana jin dadin wannan aiki na sake sarrafa gwangwanaye. Ya fara wannan sana'a ta hanyar yayyanka gwangwanaye da aka tattaro daga ko'ina - shara, kwata da bola.
Ya ce "A lokacin da ka je bola don tattara gwangwanaye, za ka fuskanci kalubalen jama'a da za su dinga cewa ba ka san me kake yi ba kana yawon bola; za su dinga yi maka kallon ba ka da hankali."
Baje-koli a Landan
Amma kuma bai damu da hakan ba, inda yake mayar da hankalinsa kan tattara gwangwanaye 200 zuwa 1,000, ya danganta da abin da yake son samarwa.
Abu ne da ya yi wa mutum daya yawa, kuma wani lokacin yana biyan mutane don su tara masa gwangwanayensu.
Da zarar an tattara gwangwanayen, ana fara wanke su sannan a yayyanka su yadda ake so.
Ifedilichukwu na sayar da abubuwan da yake samarwa, inda wasu sukan kai har dala dubu daya.
Ya zuwa yanzu dai, ya halarci baje-koli sama da 30, ya lashe kambi da dama saboda alkinta muhalli, inda a karshen wannan shekarar zai halarci baje-koli a Landan.