Dubban 'yan kasar Uganda ne suka caba ado da yin kwalliya da tufafin gargajiya inda suka taru a Kampala a wannan makon don gudanar da bikin murnar cika shekaru 30 da hawan Sarkin Buganda, Ronald Muwenda Mutebi II kan mulki.
Shi ne shugaban jama'ar Baganda, daya daga cikin kabilu mafi rinjaye a kasar.
Ronald Muwenda Mutebi II na mika gaisuwa ga dandazon jama'a a lokacin da sautin gangunan masarauta ke tashi. "Wannan lokaci ne na farin ciki," in ji Charlse Peter Mayiga, Firaiministan Buganda.
Al'ummar Baganda na da alaka ta kusa da nuna kauna ga sarauta. Shi ya sa suka yi fitar farin-dango don murnar cika shekaru 30 da hawan Sarki Ronald Muwenda Mutebi II kan mulki.
A kayan sanyawa na gargajiya, ana kiran na maza mai launin fari "Kanzu" sai na mata da yake da kala da ake kira "Bitenge", mutanen sun taru suna yi wa Sarkinsu addu'a.
Sarkin farko na masarautar Buganda a zamanin Daular Kintu shi ne Kato Kintu kuma ya taimaka wajen hade kan masarautar a karni na 13. A karni na 18 da 19 kuma, Buganda ta zama daya daga masarautu mafi karfi a Gabashin Afirka.
Masarautar Buganda ita ce mafi girma a yau a Gabashin Afirka da ta hada da yankin tsakiya da ma Kampala babban birnin Uganda.
Bayan Uganda ta samu 'yancin kai a 1962, an rushe masarautar a lokacin Firaministan Uganda na farko Milton Obote a 1966 wanda ya ayyana Uganda a matsayin Jamhuriya.
A shekarar 1993 ne shugaban Uganda na yanzu Museveni ya sake assasa masarautar.
Masarautar na da kusan mutane miliyan 14 da suka kai yawan kaso 16 na jama'ar Uganda.
"Mun zo nan ne don taya murnar zagayowar ranar nadin sarauta, sannan mu yi addu'ar ci gaba da samun lafiya ga sarkinmu", in ji Annet Nakafeero, wata mai jiran kanti 'yar shekaru 34.
Dalibai sun rera wakoki a yayin bikin a fadar sarki a tsaunin Kampala inda suka nishadantar da shugabannin siyasa da na gargajiya.
Sarkin Buganda ba shi da karfin iko a gwamnatance. Amma yana da karfin fada a ji sosai kuma ana girmama shi.