Ana kallon tufafin gomesi a matsayin tufafin mutunci wajen mata.            

Daga Kudra Maliro

A garin Buganda, tufafin gomesi, wani tufafi mai daukar hankali, wanda ya hada da riga mai kai wa dab da kasa, wuyanta mai kusurwa hudu da hannunta mai ciko, wanta alama ce ta mutunci da kima.

Ana yin ɗamara tufar da ƙyalle a saman mara, sannan ana sakar botir guda biyu a kasan wuyan rigar daga kafadar hagu.

Gomesi ya samo asali daga shekarar 1905, daga wasu teloli biyu 'yan Goan, wadanda aka saka su ɗinka kayan wata makarantar kwana ta 'yan mishan. A hankali, tufafin ya zama tambarin matan Uganda, a cewar masana kwalliyar zamani.

"Gomesi tufafin nuna isa ne ga mata, na shigar mutunci da kima. Yana da ban sha'awa, kuma kalolinsa suna nuna gargajiyar garin Buganda, da Gomesi ko bodingi", in ji Vincent Kisiriko, dan jarida a Uganda wanda ke birnin Kampala ya fada wa TRT Afrika.

An fi amfani da tufafin gomesi a tarukan gargajiya kamar bikin aure.

A yankin tsakiyar Uganda, da sauran yankunan kasar, ba a yin bikin gargajiya ba tare da mata sun yi ado da tufafin gomesi, mai ban sha'awa ba.

Ana iya saka tufan a bukukuwa kamar auren gargajiya, da na binne gawa.

Kisiriko ya kara da cewa, "Wannan tufafin ana iya kara masa kwalliya da sarƙa da kayan ƙawa, bisa la'akari da irin bikin."

Ana dinka yawancin tufafin gomesis daga kyallaye masu hasken launi.

Asalin ɗinkinsa

Labarin ya fara ne a makarantar sakandare ta Gayaza High School (a Kampala) a shekarar 1905, lokacin da Miss Alfreda Allen, shugabar makarantar a lokacin ta nemi wani tela mai suna Mr Gomes, da ya ɗinka wa mata kayan makaranta.

Yawancin tufafin gomesi ana yin su ne da auduga, ko alhariri, ko lailon, amma na alhariri ya fi kowanne tsada.

Ana ɗaura ɗamara mai suna kikooyi ko kanga daga kasan Gomesi don hana ƙyallen lailon ɗin mannewa a jiki.

Gomesi da aka dinka shi da kyau, yakan kunshi kyalle har mita shida. Ana sayar da shi a kusan dukkan shagunan da ke kasar.

Yadda ake daura gomesi yana da tsari na musamman.

A bukukuwan nuna kwalliya kamar na Kampala Fashion Awards, a babban birnin Uganda ana sa ran tufafin ya janyo hankalin 'yan kasuwar tufafi daga yankunan gabashin Afirka.

"Farashin gomesi yana tsakanin dala 10 zuwa dubban daloli. Lokacin bukuwa, duka mata suna saka gomesi," in ji Ms. Hansai.

Baya ga gomesi, 'yan Uganda suna da tufafin gargajiya daga yammacin kasar, kamar na Esuuka, wanda 'yan Banyoro da Batooro suke sakawa, da kuma Omushanana, wanda na mutanen Banyankole da Bakiga ne, su ma daga yammacin kasar.

TRT Afrika