Daga Emmanuel Onyango
Wata babbar bishiyar da rayuwarta ta yi daidai da lokacin farkon isowar ƴan bishara na Biritaniya a Uganda ta fadi ƙasa warwas a daren ranar Litinin bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar da ke gabashin Afirka.
Bishiyar ta atili 'Canarium', wadda aka fi saninta da Omuwafu, an yi hasashe ta haura shekaru 150, kana ta kasance wani ɓangare na fadar sarki na 30 na masarautar Buganda, Sarki Kabaka Muteesa na daya.
A karkashin reshen bishiyar ne wani mai yawon binciken Ingilishi John Hanning Speke da ɗan kasar Scotland James Augustus Grant suka zauna a shekara ta 1862 yayin da suke jiran haduwa da sarkin.
Daga baya suka hadu da Kabaka a cikin fadarsa.
Kazalika, a karkashin bishiyar Omuwafu ne sarkin ya karbi baƙuncin wani mai yawon bincike Ba’amurke Henry Morton Stanley a shekara ta 1875 ya kuma rubuta wa sarauniyar Ingila wasika yana gayyatar masu bishara na Burtaniya.
Ƴan bisharar sun kafa makarantu a masarautar, amma yi ta kai wa Stanley suka sosai saboda rawar da ya taka a mulkin mallaka da turawa suka yi a yankin gabashin Afirka sakamakon hadin gwiwarsa da Sarki Leopold na biyu na kasar Belgium wajen kafa mulkin mallaka na danniya a yankin Kongo.
Fadar sarkin Buganda ta kasance tana da faɗi sosai, a cikinta har da inda jami'ar Kyambogo take a Kampala babban birnin kasar.
Bishiyar Omuwafu tana da matukar daraja da ƙima ta al'adu ga mutanen Buganda.
A baya an yi watsi da shirin gina wata cibiyar ilimi da jami'ar ta yi saboda fargabar hakan na iya fusata al'ummar yankin.
“Bayan samun labarin wannan bishiyar, sai muka bukaci mahukunta (jami’ar) da su bar bishiyar domin tana da tarihin da ya bayana mana labarin inda muka fito da kuma inda za mu je,” in ji Farfesa Elizabeth Kyazike, masanin ilimin kimiya na kayan tarihi a Jami'ar, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta Uganda ta rawaito shi yana cewa.
A kwanakin bishiyar na karshe, Omuwafu ta samar da inuwa ga dalibai yayin zaman tattaunawa da tarurrukan da suka shafi al’adu, a cewar jami'ar.
Bishiyar ta kasance wata aba da ke tunatarwa zuwa ga tarihin masarautar Buganda.
Kazalika sarki na yanzu ya bukaci jami'ar da ta dasa wata sabuwar bishiyar da za ta maye gurbin Omuwafu, kamar yadda masarautar ta wallafa a shafin X, wanda a baya aka fi saninsa da Twitter.
Al'ummar Uganda sun nuna alhininsu tare da kaɗuwa yayin da hotunan faduwar bishiyar suka yaɗu a kafafen intanet.
Mutane da dawa sun yi kira da a adana jikin bishiyar.