Sakon 'Angels for Gaza' na da manufar yada sakonnin nuna goyon baya ga Falasdinawa. Hoto: TRT Afrika

Daga Munier Parker

Bo-Kaap ne wajen da aka fi amfani da manhajar Instagram a Cape Twon, Afirka ta Kudu. Tare da gidajensa masu launi daban-daban da tituna masu duwawatsu da hasumiyoyin masallatai, a yanzu ya zama cibiyar nuna goyon baya ga Falasdinu.

Wani mazaunin yankin Ubeidullah Gierdien ne ya fara wannan fenti na nuna goyon bayan.

Zanen da ake kira da sunan "Angels of Gaza", sun mayar da katangun garin wani dandali na saƙonnin nuna goyon baya ga Falasdinu.

Bo-Kaap shahararren yankin 'yan yawon bude ido ne a Afirka ta Kudu. Hoto: TRT Afrika

Zane-zanen sun zama wata alamar aikin hannu da ke da ƙarfin kawo sauyi, hade kawunan mutane da yaɗa sakon fata nagari a duniya.

Obeidullah ya shaida wa TRT Afirka cewa "Wannan aikin na da manufar nuna goyon baya ga Falasdinawa musamman ma takenmu na "Angels of Gaza" wanda ke nufar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa tana kashe fararen hula da suka haɗa da yara ƙanana da mata masu juna biyu.

Masu zane-zane da ke Bo-Kaap ne suke yin wannan aiki. Hoto: TRT Afrika

An fara wannan aiki a lokacin da Obeidulllah tare da mahaifiyarsa, Aisha Gierdien suka gano amfanin hada kayan gargajiya na gini da saƙon nuna tirjiya waje guda.

Sun zaburar da masu zane-zane na yankin, kuma a yayin da abun ya girmama sai dukkan jama'a suka goyi baya.

Suna kuma yada wayewa ta hanyar 'yan yawon bude idon da ke zuwa yankin, suna daukar hotuna tare da taimakawa wajen yada wannan sako.

Obeidullah ya ci gaba da cewa "Sanin cewa Bo-Kaap yanki ne na 'yan yawon bude ido, na yanke shawarar cewa zan tabbatar da kowanne hoto da na samo daga sassan duniya, ya shiga hannun 'yan yawon bude idon da ke ziyartarmu, wadanda za su dinga yaɗa sakon Bo-Kaap na tare da Falasdinawa da goya musu baya."

Zane-Zanen da ake yi a katangun Bo-Kaap da ke Afirka ta Kudu na bayyana nuna goyon baya a Falasdinawa.  Hoto: TRT Afrika

Tarihin da Bo-Kaap ke da shi, yankin ya taba zama a matsayin matattarar bayi, wannan ya sanya ya zama suke da tirjiye d abijirewa zalunci.

Wannan aiki ya zama shaida ta irin karfin da jama'ar ke da shi, kare kayan da aka gada, da goyon baya mai karfi.

Ya kara da cewa "Ina amfani da wannan abu na gado wajen wayar da kawuna. Ba ma goyon bayan duk wani rikici. Ba ma goyon bayan duk wani tsari na danniya da nuna wariya, ba ma goyon bayan zalunci."

A hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza d ata mamaye ta kashe Falasdinawa sama da 15,000 da mafi yawan su mata ne da yara ƙanana. Ta kuma jikkata sama da mutum 40,000.

Kasashen duniya sun soki wadannan hare-hare da Isra'ila ke kai wa Falasdinawa inda da yawa suke bayyana hakan a matsayin kisan kare dangi da Isra'ila ke aikatawa.

TRT Afrika