Yakin da Isra'ila ke yi a yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya ya kashe mutane akalla 31,341 tare da jikkata 73,134. Harin bama-bamai da take kaiwa a halin yanzu ya shiga wata na biyar.
Hotunan Murals, a cewar masu zane-zanen waɗanda suka yi zanen, sun bayyana irin tsayin dakar Falasdinawa suka yi a mamayar Isra'ila.
Kazalika, wata alama ce da ta nuna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.
Fasahar al'adu na zane-zanen sun kayatar da hanyoyi sannan suna da matukar tasiri a babban birnin kasar Kenya.
Zane-zanen masu launin daban-daban a kan gine-gine da gadoji da kuma unguwannin birnin sun dau hankali sosai.
Masu zane-zane suna bayyana manufarsu kan al'amuran da suka shafe su ta zamantakewa da siyasa na cikin gida ko kuma a duniya ta hanyar rubuce-rubuce da zane-zane a cikin sauran nau'o'in fasahar kan hanyoyi ko tituna.