Mohammed Abou Samour kenan a wani asiiti da yake jinya a Houston, Texas,  bayan an yanke mishi  wasu sassan jikinsa yakin da Isra'ila ke yi a Gaza. (Shugaban Fiona Tagari)  

Daga Indlieb Farazi Saber

A yayin wani wasan kati da suke buga wa, Hadi Zaquut mai shekaru 12 ya sake doke Zalatimo kai tsaye, inda ɗan wasan da ke rike da karin mafi girma ya lashe gasar.

''Raqzi Khalto, raqzi,'' Hadi ya fada cikin harshen larabci yana mai murmushi ga Zalatimo ma'ana ''ki mayar da hankali innarsa'' yana mai naci kan ta mayar da hankali, za ta iya ɗaukar wasu ɗabaru da za su ba ta damar lashe wasan katin.

"Ko da yaushe yana yin ha'inci, amma da murmushi muke rabuwa da shi," a cewar Zalatimo daga gidanta da ke St Louis, Missouri, inda a yanzu Hadi ke yin hutun ƙarshen mako, yana wasa da innarsa, wata mai aikin sa kai na 'Heal Palestine' tare da ɗanta mai shekaru ita 13 Haider.

Hadi ya fito ne daga grain Mawasi dake yammacin Khan Younis a kudancin Gaza. Ya isa Amurka ne tare da mahaifiyarsa Camille Zaqout a watan Mayu don yin jinya, bayan da ya rasa kafarsa ta dama a wani hari da Isra'ila ta kai a watan Nuwambar bara.

''Likitoci a Amurka sun yaba da aikin yanke kafata inda suka ce an yi lafiya kalau, kuma na ce ba shakka, likitoci a Gaza sun zama kwararru a kan wannan aiki,'' kamar yadda yaron ya shaida wa TRT World.

Ƙarancin taimako daga ƙasashen waje

Hadi yana daga cikin rukunin yara 22 da aka kwashe daga Gaza zuwa Masar kafin su isa Amurka a cikin wannan shekara.

Hadi Zaquut, da abokansa suna jin daɗin ice-cream din da suke sha yayin ziyara da suka kai gidan zoo a St Louis, Missouri. Hoto:Shugaban Randah Zalatimo

Sakamakon rufe kan iyakoki da kuma tsaurara bincike, yawancin wadanda aka yanke wa kafafu a wannan yakin ba za su iya barin Gaza don neman lafiya a kasashen waje ba.

Tun daga ranar 12 ga watan Satumba, Majalisar Dinkin Duniya ta ce hukumomin Isra'ila sun ba da izinin fitar da majiyyata 219 ne kawai daga Gaza tun bayan rufe iyakar Rafah a watan Mayu 2024.

Kafin wannan lokaci, daga cikin majinyata 14,000 da aka nemi a fitar da su daga Gaza tun a watan Oktoba na 2023, mutum sama da 5,000 ne aka kwashe kawo yanzu. Ƙasashen da suka karɓe sun haɗa da Turkiyya da Qatar da Afrika ta Kudu.

A Amurka ƙungiyar Heal Palestine ta samu damar samun biza duba lafiya na kwashe yaran, bisa sharaɗin ba za su iya neman mafaka ba, kuma dole ne su bar ƙasar da zarar an kammala yi musu jinya .

Ranar da aka fara ganin canji

Ɗa daya tilo a cikin iyali mai yara mata biyar, Hadi ya kasance mai hazaka ga iyalinsa, wanda ya hakan ya zama abu mai wuya a lokacin da yakin.

Shi ne ya ke zuwa neman ruwan amfani bayan da ak yi ta fama da ƙarancinsa a lokacin da yakin ya barƙe.

Kamar sauran yara masu irin shekarunsa, Hadi Zaquut yana son zama abubuwa da dama idan ya girma, ciki har da mai sarrafa kwamfuta. Hoto:  Shugaban Randah Zalatimo

Tsayawa a kan layi har na tsawon wasu sa'o'i don tabbatar da cewa iyayensa da 'yayyensa mata sun samu ruwa mai tsafta da su sha ya zama aikinsa a kullum, kafin zuwan wata safiya na ranar 11 ga watanNuwamba, lokacin da ya gano wata hanyar samun ruwa ta daban daga bututun da ke kusa da gidansu.

Gidansu Zaquuts na hawan ɓene na huɗu, a yayin da ya shiga ta ƙofar gidan domin ya nuna wa daginsa hikimarsa na samun ruwa, sai ga wani fashewa bam mai ƙarfi, komai ya zama duhu.

"Da na buɗe idona sai ganni cikin baraguzai ta ko'ina, ba na iya jin komai, ban ji zafi a jikina, har lokacin a gigice nake, ina ta kalon ko ina, amma ban gane komai ba. Akwai tarin kura da tarkace," in ji Hadi.

Iyalinsa sun tsallake rijiya da baya, amma baya ga mahaifiyarsa da ta same shi a asibiti a 'yan kwanaki bayan an yanke masa kafafu, tun ranar bai sake ganin mahaifinsa ko yayyensa ba.

Masu aikin ceto ne suka gano Hadi a makale a Ƙarkashin baraguzan ginin sa'o'i bayan fashewar bam ɗin kana aka sanya shi a cikin motar da za a kai shi asibiti. Kusa da shi, ya gane gawarwakin abokansa guda biyu da suka mutu, Mohammed da Tayyab.

"Ba zan taba mantawa da wannan lamarin ba, ban yi tunanin haka zai taba faruwa da ni ba, ban ji komai ba, na dai san cewa akwai jini yawa ta ko'ina kuma ina kallon waɗannan yara biyu maza ina tunani kan me ya faru?' Muna tsaye muna ɗiban ruwa."

A cibiyar kula da lafiya ta Nasser dake Khan Younis, inda Hadi ya samu kulawa, kuma inda mahaifiyarsa ta same shi daga baya, likitoci sun yi masa jinyar hannunsa ta dama da kafarsa ta hagu wadanda dukkansu suka samu munanan raunuka sakamakon harin.

A cikin kwanaki biyu, kafarsa ta shiga cikin haɗarin kamuwa da cuta, sai aka shaida masa cewa za a yanke shi.

Hadi a hannun (hagu) da abokinsa Haider Abu Jaber, ɗan Randah Zalatimo, suna aikni ƙirƙire-ƙirƙire na alamun gwagwarmayar Falasɗinawa. Hoto:  Randah Zalatimo

"Asibitin ya ce, raunin da suke gani daga bama-baman da Isra'ila ke amfani da su suna ɗauke da wani nau'in sinadari da ke haifar da cuta da ke yaduwa a jiki," a cewar innar Hadi.

A farkon yakin, ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce Isra'ila na amfani da "makamai da ba a saba gani ba" waɗanda ke haifar da mummunar kuna a jikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Zargin wanda daga baya ya samu goyon bayan likitocin kasashen duniya da suka kai ziyara.

Jarumi Hadi ya ce abin da ya fara zuwa zuciyarsa shi ne iyalansa waɗanda a yanzu haka suke gudun hijira a wani tanti a Khan Younis.

"Ina tuna cewa ni nenamijin gidanmu bayan mahaifina kuma suna bukatar na kasance a wannan matsayi har na tsawon rayuwata kuma ina bukatar in kasance a wurin. Don haka ina buƙatar in tashi don na iya cika wanna burin, kowa yana bukata na."

Likitoci sun yanke masa kafa, amma hannunsa na bukatar ƙarin kulawa da ba za su iya bayarwa ba, saboda ƙarancin magunguna da kuma yadda wasu da dama suka samu rauni masu muni.

Ɗaya daga cikin ɗubu

Hadi na ɗaya daga cikin wadanda suka yi ''sa'a'' yayin da aka yi masa aikin tiyata ba tare da allurar kashe zafi ba. Amma saboda raguwar kayayyakin jinya da kuma gurɓataccen tsarin kiwon lafiya da harin Isra'ila ya haifar, an yi wa dubbai aikin tiyata ba tare da shi ba.

A watan Yuni ne, shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA) Philippe Lazzarini ya kiyasta sama da yara 2,000 da aka yanke kafafu da hannaye sakamakon wannan yaki, wanda Dr Ghassan Abu-Sittah, babban likitan fida na Birtaniya da Falasdinu ya bayyana, a matsayin babbar ƙungiyar yara wadanda aka yanke wasu sassan jiki a tarihi.

TRT World