Hip-hop ya soma tasiri sosai a Senegal a shekarun 1980. Hoto/ Sister LB

Daga Awa Cheikh Faye

An cika shekara 50 da soma wakokin Hip-hop, wanda wasu shekaru ne masu muhimmanci ga wani salon waka mai alaka da matasa.

Wakar Hip-hop, wadda aka soma ta shekaru 50 da suka gabata a Bronx, ta kunshi al’adu da yanayin rayuwa da rawa da waka da zayyana da dai abubuwa da dama.

Kidan na Hip-hop, wanda matasa a fadin duniya tsawon shekaru suka rinka yi wa rawa, wani makadi dan kasar Jamaica mai suna Clive Campbell wanda aka fi sani da DJ Kool Herc ya kirkire shi a ranar 11 ga watan Agustan 1973.

Hip-hop ya yi tasiri matuka inda ya mamaye Amurka da duniyar waka, da wasanni da ado. Haka kuma Afirka ba ta kasance kashin baya ba.

Hip-hop a Afirka

A Senegal, Hip-hop ya soma tashe a 1988.

Ya soma ne inda kungiyar mawaka wadanda matasa ke hadawa suke kokarin kwaikwayon wata nau’in rawa wadda gwanayensu ke yi a lokacin, wadanda suke kallo a talabijin.

Ana ta taruka domin murnar cika shekara 50 da soma Hip-hop. Hoto/AFP

“Wadannan kananan kungiyoyin sun soma rawa da kuma kokarin ganin yadda za su samar da irin abin da ake yi a Amurka, sai a lokacin da suka yi tunanin hakan zai yiwuwa idan suka yi wakar harshen Wolof.” In ji Farfesa Mamadou Drame, wanda shi ne mataimakin shugaban tsangayar ilimi da horas da kimiyya da fasaha ta Jami’ar Cheik Anta Diop da ke Dakar (Fastef).

“Sun ga cewa yana da muhimmanci su tattauna kuma idan ana so a yi wa mutane magana, akwai bukatar amasu magana ta yaren da suke ganewa, kuma daga wannan lokacin sai suka soma wakar da Wolof,” kamar yadda ya kara da cewa.

Wannan ya biyo bayan wakar gambara da suka yo a Wolof (harshen da ya fi fice a Sengal) wanda mawakan Positive Black Soul suka yi a 1989.

Tafiyar Siyasa

“Da gaske ne a baya ana tattaunawa kan batutuwan siyasa, sai dai ba shi ne ya fi muhimmanci ba. Tun daga wannan gabar zuwa sama, mawaka ne ke bukatar tattaunawar ta siyasa, musamman daga kungiyar Rapadio da kuma gambarar su mai karfi.

Tun daga lokacin, masu gambara sai suka daina magana kan yadda suke ji ko kuma soyayya inda suka koma kan batun siyasa siyasa,” in ji Farfesa Drame.

Galsen ta samu nata kungiyoyin kamar su Positive Black Soul da Rapadio da Daara J da Wa BMG 44 da sauransu wadanda suka bude kofa ga Hip-hop na yau kamar su Sister LB.

Mai wakokin gambara ta Senegal wadda tana alfahari zama ‘yar kungiyar da ta shafe rabin karni, ta bayyana cewa shekaru 50 da soma Hip-hop ya kara karfafa mata gwiwa domin kara juriya.

Positive Black Soul na daga cikin kungiyoyin da suka tallata Hip-hop. Hoto/AFP

“Duk da cewa bangaren Hip-hop na Senegal ya sha gwagwarmaya, amma duk da haka ka’idojin ba su sauya ba.

Har yanzu sha'awar tana nan, kuma hakan ne ya ba mu damar kasancewa a nan, mu yi murna da tafiyar da ta taimaka mana sosai," in ji ta.

Sélbé, wadda asalin sunanta shi ne Sélbé, ta shiga Hip-hop domin samun damar amayar da abin da ke cikinta.

Mai wakar gambarar na amfani da damar ta Hip-hop domin bayyana matsalolinta da kuma fatanta ga al’umma, kamar wadanda suka gabace ta.

Yanayin zuciya

“A Senegal, matasa musamman mata ba a barin su domin shiga wata muhawara. Shi ya sa na dauki makarafon domin baza muryata da muryoyin duka mata sa suka sha wahalar rashin adalci”, kamar yadda ta bayyana da.

Hip-hop, wanda aka fara shi shekaru 50 da suka gabata a Bronx, ya kunshi al'adu da yanayin rayuwa da ke bazuwa a fadin duniya. Hoto/AFP

Farfesa Drame ta bayyana cewa Hip-hop “kimiyyar rayuwa ce” da kuma “yanayin zuciya” wanda ake yin sa a yanayin da matasa ke bayyana kansu a kan titi, ta hanyar kayan da suke sakawa da kuma dabi’arsu.

Ana iya ganin hakan a manyan bangon da ke kan titunan motoci na babban birnin Senegal. Haka kuma za a iya ganinsu a lungunan da kananan masu sayar da kayayyaki suke kamar stylist da Baay Souley.

Sabuwar al’umma a Senegal ta samu tasiri sosai daga hip-hop, musamman daga shekarun 1980 da 1990, sai dai tasirin ya zo ne daga galsen hip hop, kamar yadda Farfesa Drame ta yi bayani.

Hip-hop ya yi tasiri a yanayin rayuwa da kimiyya a Afirka. Hoto/AP

“Hip-hop da farko ya soma tasiri ne a kan wasanni, idan kuka ga masu dambe kamar su Tyson wadanda suka yi ‘Boul fale’,” a cewarsa.

Nesa daga buƙatun siyasa wadanda suka sa suka a shekarun 1990, kuma duk da gasar da Hip-hop din ke fuskanta daga Afrobeat da Mbalax, Galsen hip-hop yana yawan sabunta kansa akai-akai, yana fitar da sabuwar baiwa ko basira lokaci bayan lokaci, wanda ke faranta wa masu son kiɗan rai.

TRT Afrika