Isra’ila ragargaza mafi yawan yankin Gaza da aka mamaye, abin da ya janyo gagarumin ƙarancin muhimman kayan buƙatun ya da kullum da suka hada da abinci da ruwa da magani da lantarki, yayin da aka tilasata wa gaba ɗaya jama’a barin gidajensu. / Hoto: AFP

Falasɗinawa da aka sako sun bayyana cewa sojojin Isra'ila sun kai musu hari da karfi saboda sun ki karanta ayoyin Attaura.

Jamal Al Tawil ya bayyana a ranar Asabar cewa an yi masa mummunan duka sa'o'i kaɗan kafin a sake shi, saboda ya ƙi karanta wata ayar da ta ƙunshi barazana ga Falasdinawa.

Isra'ila ta sha kama fitaccen jagora a Hamas daga Ramallah tun yana ɗan shekara 16, tare da shafe fiye da shekaru 18 a tsare.

Ya yi gudun hijira zuwa Marj al Zuhur a 1992 kuma ya jagoranci yajin cin abinci a 2021 don neman a sako 'yarsa, 'yar jarida Bushra.

A cikin wani faifan bidiyo, yayin da yake karɓar magani a wani asibiti da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, Al Tawil, mai shekaru 61, ya bayyana cewa sojojin Isra'ila sun buƙaci ya karanta wata ayar da ke cewa: "Mutanen waje kada ku manta, ina bin makiyana ina kama su, kuma ba na dawowa har sai na hallaka su."

Da ya ƙi amincewa, sojojin sun yi masa mugun duka, lamarin da ya kai ga taɓarɓarewar lafiyarsa har ya kasa tsayawa a lokacin da ya tashi zuwa motar bas ta Red Cross ta Ƙasa da Ƙasa.

Lamarin ya tilasta wa ƙungiyar agaji ta Red Crescent daukar Al Tawil zuwa motar daukar marasa lafiya tare da miƙa shi asibiti.

Barazana da matsanancin yanayi

Mohammed Dweikat, wani Bafalasɗinen da aka sako, ya ce hukumomin Isra'ila sun tilasta wa fursunoni karanta ayoyin Attaura a wani mataki na tsoratarwa da barazana.

Dweikat ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu bayan sakinsa a kashi na biyar na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas, “Godiya ta tabbata ga Allah da ya raya mu bayan ya yi sanadin mutuwar mu.

"Yau ce sabuwar haihuwarmu bayan mun mutu; mun gode wa Allah da ya ba mu Gaza," in ji Dweikat. Ya shafe shekaru 16 da rabi a gidan yarin Isra'ila, bayan an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 18.

Game da yanayin da ake ciki a gidajen yari, ya ce: "Al'amarin ya koma jahannama bayan 7 ga Oktoba, 2023. Duk abin da mutum zai iya tunani, mun fuskance shi a gidan yari - rayuwa mai tsanani, da wulaƙanci, da rashin abinci da rashin magani, komai ba shi da kyau."

“A cikin kwanaki na ƙarshe al’amura sun ƙara tsananta, mun fuskanci matsin lamba da wulaƙanci, kuma sojojin Isra’ila cikin barazana da zagi sun tilasta mana karanta ayoyin Attaura kamar su: “Ba za mu manta da ku ba, muna tare da ku, kuma za mu saka muku ido har abada.” Inji shi.

Dweikat ya nuna hannunsa inda aka tilasta masa sanya wani abu a hannunsa tare da wannan ayar da aka rubuta da Larabci.

"Jagoran da da aka sako Jamal Al Tawil ya ƙi karanta ayar, kuma sun yi masa mugun duka, wanda hakan ya sa aka kai shi asibiti muna barin wurin da ake tsare da shi." "Ba sa mutunta kowa har da tsofaffi."

"Abin da ya fi sa mu farin ciki shi ne kyakkyawar tarbar da jama'a suka yi mana, abin da ya nuna hadin kan al'ummar Falasɗinawa game da fursunonin," in ji shi lokacin da yake magana game da tarbarsa a lokacin da aka sake shi.

Game da Gaza, ya ce: "Babu wata kalma da za ta iya yin adalci ga Gaza, wadda ta sadaukar da komai - 'ya'yanta, da tsofaffi da gidajenta - don cim ma wannan manufa."

TRT World