Turkiyya ta kuduri aniyar tabbatar da ta sama wa Ukraine 'yancin kanta da kuma cin gajiyar yankunanta, ciki har da Crimea, a cewar Ministan harkokin wajen kasar Hakan Fidan.
"Za mu mara wa Ukraine baya wajen tunkarar barnar tattalin arziki da yakin da ake yi ya haifar. Za kuma mu taimaka mata wajen magance matsalar jinkai da aka samu," a cewar Hakan Fidan a wani taron farfado da Ukraine da aka yi a birnin London ranar Laraba.
Da yake jaddada batun matsayar Ankara game da samun 'yancin Ukraine da ikon mallakar yankunanta, ciki har da Crimea, ya ce: "Matsayinmu yana nan a kan tsari babu gudu babu ja da baya kamar yadda aka saba."
Yayin da tabo batun cinikin hatsin da Ankara ta kulla da kuma yarjejeniyar musayar fursunonin yaki, Fidan ya ce shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yana aiki ba dare babu rana a kokarin rage wahalhalun da yakin da aka yi Ukraine ya haifar.
Sake gina Ukraine
"Yanzu muna bukatar yin aiki ne kan yadda za a fito da tsarin kudin da zai taimaka wajen sake gina Ukraine tare da dawo mata da martabarta," a cewar Fidan.
Ya kuma yi tuni kan cewa, 'yan kwangilar Turkiyya sun gudanar da kusan kashi 50 na wasu ayyuka da suke yi a Ukraine a lokacin da yakin ya soma.
A cewarsa, 'yan kwangilar sun ci gaba da aiwatar da wasu ayyuka 29 a kasar da yaki ya daidaita duk da rikicin da ake ciki.
"Za mu ci gaba da karfafa 'yan kasuwaninmu da 'yan kwangilar gwiwa kan da su biya wa mutanen Ukraine bukatunsu, akowanne yanayi da ake ciki."
Da yake Karin haske game da yarjejeniyar sake gina kasar Ukraine da shugaba Erdogan da shugaban Volodymyr Zelenskyy na Ukraine din suka rattabawa hannu a birnin Lviv a shekarar da ta gabata, ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana cewa, Ankara ta kuduri aniyar gabatar da duk wani gogewa da kwarewata teburin.
"Za mu dora kan abubuwan da muka yi ya zuwa yanzu don tallafawa wajen sake maido da martabar Ukraine," in ji Fidan.