An hango Yevgeny Prigozhin, shugaban kungiyar sojojin haya ta Wagner, yana barin hedikwatar sojin kasa da ke birnin Rostov-on-Don a wata mota kirar SUV a wani bidiyo da kamfanin dillacin labarai na Rasha RIA ya wallafa a Telegram.
Tun da farko Prigozhin ya amince ya dakatar da boren da yake yi wa shugabannin rundunar sojin Moscow bayan shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya yi sulhu a tsakaninsu, kuma fadar Kremlin ta ce zai tafi Belarus a yarjejeniyar da suka kulla.
Prigozhin, wanda ya umarci dakarunsa na Wagner su yi wa shugabannin sojin Rasha bore, zai tafi Belarus kuma za a janye tuhumar da ake yi masa ta aikata lafuka, a cewar Rasha a bayanin da ta yi ranar Lahadi da safe.
"Babban burinmu shi ne a kauce wa zubar da jini da taho-mu-gama da kuma bata-kashin da ba a san karshensa ba," a cewar kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov a hirarsa da 'yan jarida.
Peskov ya kara da cewa a karkashin yarjejeniyar da Shugaba Lukashenko ya jagoranta, ba za a tuhumi mayakan Wagner ba.
"A ko da yaushe muna jinjina musu kan bajintarsu a fagen yaki."
"An amice da yarjejeniyar da za ta sa mayakan Wagner su koma sansanoninsu," in ji Peskov, inda ya kara da cewa za a bai wa mayakan da ba su yi boren ba damar shiga rundunar sojin Rasha.
Babu tabbaci ko Prigozhin ya samu abin da yake so
Peskov ya ki cewa komai kan ko Prigozhin da mayakansa sun samu abin da suke so, baya ga bayar da tabbacin tsaron lafiyarsu — abin da Shugaba Putin ya sha alwashin tabbatarwa — har ya amince ya janye dukkan dakarunsa.
Ya bayyana abin da ya faru a ranar a matsayin wani mai "muni".
"Akwai sharuda da dama da aka sanya da zan gaya muku," in ji Peskov.
Prigozhin ya umarci dakarunsa da suka tunkari birnin Moscow ranar Asabar su janye, abin da ya hana yin arangamar da ka iya zama mafi muni a Rasha a cikin shekaru aru-aru.
Rikici tsakanin shugaban Wagner Prigozhin da rundunar sojin Rasha ya yi kamari, lamarin da ya sa sojojin hayar suka kwace hedikwatar sojin kasa da ke kudancin Rasha sannan suka nufi arewa inda suka tafi babban birnin kasar.
Peskov ya ce ba wani "abin tambaya ba ne" kan ko boren da Wagner suka daina zai yi tasiri kan yakin Rasha da Kiev.
Ya kara da cewa Moscow ta gode wa Lukashenko bisa rawar da ya taka wajen shawo kan rikicin.
Dakarun Wagner sun taka muhimmiyar rawa a yakin Ukraine, inda suka kwace birnin Bakhmut da ke gabashin kasar, wurin da aka dade ana zubar da jini da fafatawa.
Sai dai Prigozhin ya rika sukar rundunar sojin Rasha, inda ya zarge ta da rashin iya aiki da kin bai wa dakarunsa kayan aiki.