Amurka ta zargi Rasha da tsokanar jiragen yakinta a sararin samaniyar Syria

Amurka ta zargi Rasha da tsokanar jiragen yakinta a sararin samaniyar Syria

Wannan ne karo na biyu cikin awa 24 da aka zargi Rasha da tsokanar jiragen yaki marasa matuka na Amurka a wajen.
Har yanzu Rasha ba ta ce komai ba kan ikirarin na Amurka. Hoto: AP

Rundunar Sojin Amurka ta ce jiragen yakin Rasha sun sake yin shawagi mai matukar hadari a kurkusa da jiragen yaki marasa matuka na kasarta a sararin samaniyar Syria, lamarin da ya jawo wuta ta tashi har sai da jiragen Amurkan suka zille don kar ta shafe su.

Wannan ne karo na biyu cikin awa 24 da aka zargi Rasha da tsokanar jiragen yaki marasa matuka na Amurka a wajen.

"Muna kira ga dakarun Rasha a Syria da su dakatar da wannan dabi'ar gangancin tare da bin dokokin da ake so kwararriyar rundunar sojin sama ta bi, ta yadda za mu mayar da hankalinmu kan yakin da muke yi wajen kawar da kungiyar ISIS [Daesh], a cewar Rundunar Sojin Amurkan, a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Har yanzu Rasha ba ta ce komai ba kan ikirarin na Amurka.

Kanal Michael Andrews, mai magana da yawun hedikwatar Rundunar Sojin, ya ce "Rasha ta shafe kusan awa daya tana tsokanar, wacce ta hada da yin shawagi a jiragenta samfurin SU-34 da SU-35 dab da jirgin Amurka samfurin MQ-9, da har ya jawo tartsatsin wuta. Don haka ba shawagin gaggawa ba ne, ya fi kama da na tsokana da na rashin kwarewa."

Hedikwatar Rundunar Sojin ta saki wasu bidiyoyi na yadda lamarin ya faru sau biyun a ranakun Laraba da Alhamis.

A lamarin farko, wanda ya faru da karfe 10.40 na safiyar Larabar a arewa maso yammacin Syria, jiragen yakin Rasha SU-35 suka je dab da jirage marasa matuka na AMurka, sai daya daga cikin matuka jiragen Rashan ya sha gaban jirgin yakin ya matse shi, lamarin da ya sa gudunsa ya karu sosai har wuta ta tashi.

Wutar da ta tashi za ta iya lalata injinan wanda ka iya rage karfin aikin jirgi marar matukin.

Hadari

A karo na biyun kuwa, wanda ya faru a Arewa maso yammacin Syria da karfe 9.30 na safiyar Alhamis, "Jirgin yakin Rasha ya yi tartsatsin wuta a gaban jirage marasa matuka sannan ya yi hsagai mai hadari a dab da su, yana sanya su cikin hadari," in ji Grynkewich.

Babu makamai a jikin jirage marasa matukan kuma an yi su ne don ayyukan sa ido.

Wani babban jami'in sojin Amurka Janar Erik Kurilla a wata sanarwa ya ce keta dokar da Rasha ke yi a kokarin da ake na kawar da barna a sararin samaniyar Syria "yana kara hadarin zafafa al'amura da aikata ba daidai ba."

Kusan dakarun Amurka 900 ne a Syria suke aiki da SDF - wata kungiyar 'yan tawaye da Washington ke goyon baya mai alaka da kungiyar YPG/PKK.

Babu wasu bayanai a kan ayyukan da jirage marasa matukan ke yi.

AP