Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gaya wa takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelenskyy cewa ya cancanta Kiev ya zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO, sai dai ya bukaci su yi tattaunawar zaman lafiya da Moscow.
"Babu tantama cewa ya dace Ukraine ta zama mamba a NATO," kamar yadda Erdogan ya bayyana a taron manema labarai na hadin-gwiwa da suka yi da takawaransa na Ukraine da sanyin safiyar yau Asabar.
Ya kara da cewa akwai bukatar "duka bangarorin biyu su sake tattaunawa kan zaman lafiya".
"A wannan yaki da ya shiga kwana na 500 a yau din nan, jama'ar Ukraine suna kare martabar kasarsu ne. Tun daga lokacin da aka soma shiga hatsarin yakin, mun yi bakin kokarinmu wajen kauce masa," in ji Erdogan.
Ya kara da cewa Turkiyya ta yi "aiki tukuri wajen kawo karshen yakin" Rasha da Ukraine ta hanyar tattaunawa "bisa dokokin kasashen duniya."
"Ina so na jaddada maganar da na sha fada koyaushe: Zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Duk da bambance-bambancen fahimta tsakanin bangarorin biyu, babban burinmu shi ne a sake tattaunawar zaman lafiya nan ba da jimawa ba," in ji Erdogan.
Zelenskyy ya kai ziyara Turkiyya ranar Juma'a ne domin tattaunawa game da dangantakar kasashen biyu da batutuwan da suka shafi yankinsu da kasashen duniya, ciki har da bayyana halin da ake ciki game da yakinsu da Rasha, da yarjejeniyar fitar da hatsi ta Bahar Rum.
Wannan ce ziyararsa ta farko zuwa Turkiyya tun bayan soma yaki tsakanin Rasha da Ukraine a watan Fabrairun 2022.
Shugaban Turkiyya ya ce takwaransa na Rasha Vladimir Putin zai ziyarci kasar a watan Agusta mai zuwa.
"A watan gobe Putin zai kawo ziyara Turkiyya," in ji Erdogan, yana mai karawa da cewa ya tattauna da shugaban na Rasha game da musayar fursunoni.
Ina so na jaddada maganar da na sha fada koyaushe: Zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Duk da bambance-bambancen fahimta tsakanin bangarorin biyu, babban burinmu shi ne a sake tattaunawar zaman lafiya nan ba da jimawa ba
Yarjejeniyar fitar da hatsi
Da yake magana game da yarjejeniyar Bahar Rum ta fitar da hatsi, Erdogan ya ce Ankara yana yunkurin tsawaita ta idan wa'adinta ya kare ranar 17 ga watan Yuli.
"Muna tattaunawa kan yadda ya kamata mu tsawaita yarjejeniyar bayan wa'adin ta ya kare ranar 17 ga watan Yuli. Babban burinmu shi ne a tsawaita ta zuwa akalla sau daya bayan kowane wata uku, ba wata biyu ba. Za mu yi yunkuri domin tsawaita wa'adinta zuwa shekara biyu," a cewar Erdogan.
A watan Yunin da ya gabata, Turkiyya, Majalisar Dinkin Duniya, Rasha da Ukraine sun sanya hannu kan yarjejeniya a Istanbul domin sake komawa fitar da hatsi daga tashoshi uku na Bahar Rum da ke bangaren Ukraine wadda aka dakatar bayan an soma yakin Rasha da Ukraine.
Jami'ai a Turkiyya su ce kawo yanzu an fitar da fiye da tan miliyan 33 na hatsi ga kasashen da ke bukatarsa.