Isra'ila ta samu karuwa a fannin fitar da kayayyakin yaki da take yi zuwa kasashen duniya da dala biliyan 12.5 a bara, inda kasashen Larabawan da ta kulla alaka da su a baya-bayan nan suke kan gaba wajen sayen makamai daga wajenta, a cewar jami'ai.
Ma'aikatar Tsaro, wacce ke lura da kuma amincewa da fitar da kayayyakin yaki na masana'antar tsaron Isra'ila, ta ce kashi daya bisa hudu na kayayyakin da aka fitar jiragen yaki ne marasa matuka ne, yayin da makamai masu linzami da rokoki kuma suka kasance kashi 19 cikin 100.
Alkaluman ma'aikatar sun nuna yadda yawan kayayyakin da ake fita da su din suka karu da ninki biyu a cikin shekara tara da suka wuce.
Alkaluman yawan kayan da aka fitar yankunan sun nuna yadda kayan da kasashen da suka shirya da Isra'ilan suka saya ya karu, daga kayan dala miliyan 853 a 2021 zuwa dala miliyan 2.96 a 2022.
Isra'ila ta sasanta da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Moroko da kuma Sudan a 2020.
Sai dai ma'aikatar tsaron Isra'ila ba ta yi karin bayani kan hakan ba.
Ma'aikatar ta ce yakin Rasha da Ukraine ya sa bukatar makaman da Isra'ila ke kerawa ta karu a Turai.