Fiye da kungiyoyin fararen hula 100 da kwararru kan kare hakkin dan adam 23 ne suka nemi Babban Zauren MDD da ya kafa hukuma mai zaman kanta. / Hoto: Reuters

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya [UNGA] ya kirkiri wata hukuma mai zaman kanta da za ta fayyace makomar dubban 'yan Syria da ba a san inda suka shiga ba tun bayan barkewar yaki a kasar a shekarar 2011, bayan damuwar da aka nuna a Damascus.

"Bayan shafe shekara 12 na rikici da yaki a Jamhuriyar Syria, ba a samu nasara sosai ba wajen kawar da radadin da iyalai ke ciki na samar da amsoshi kan makoma ko labarin dukkan mutanen da suka bata," a cewar matsayar MDD a ranar Alhamis.

Kasa 83 ne suka kada kuri'ar goyon bayan kudurin na MDD, yayin da kasa 11 suka kada kuri'ar kin amincewa, sai kuma kasa 62 da ba su halarci zaman ba.

Syria da Rasha da China da Koriya ta Arewa da Venezuela da Cuba da kuma Iran sun kada kuri'ar kin amincewa.

Hukuma Mai Zaman Kanta kan Neman 'Yan Syrian da Suka Bata "za ta fayyace makoma da gano inda mutanen da suka batan suke" a kasar tare da samar da taimako ga wadanda abin ya shafa da iyalan wadanda suka batan.

Juyin-juya halin Syria da ya rikide ya zama yaki a yanzu ya shiga sekara ta 13 da fara shi, kuma ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 500,000 tare da raba rabin 'yan kasar miliyan 23 da muhallansu.

Hukumar Kasa da Kasa ta Neman Mutanen da Suka Bata ta ruwaito MDD da kiyasta cewa fiye da mutum 130,000 ne suka bata ya zuwa shekarar 2021, sakamakon yakin.

Bayan kammala kada kuri'ar, fiye da kungiyoyin fararen hula 100 da kwararru kan kare hakkin dan adam 23 ne suka nemi Babban Zauren MDD da ya kafa hukuma mai zaman kanta.

Kungiyoyin sun hada da Kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch da kuma gomman kungiyoyi na Syria, inda suka yi kira ga kasashen MDD da"su goyi bayan iyalan' a kan gaskiyarsu.

Sun yi nuni da cewa kungiyar International Committee of the Red Cross da sauran kungiyoyi ma sun goyi bayan kiran.

"Ya kamata kasashen MDD su kada kuri'a don samar da wata hukuma ta jin kai da za ta nemo wa 'yan Syria amsoshin da suka dade suna jiran su ji a game da masoyansu, a cewar Kungiyar Human Rights Watch da sauran kungiyoyin kare hakkin dan adam fiye da 100 na Syria a yau," in ji Kungiyar ta Human Rights Watch.

TRT World