Abin da ya sa MDD za ta fitar da tsarin amfani da kirkirarriyar basira (AI)

Abin da ya sa MDD za ta fitar da tsarin amfani da kirkirarriyar basira (AI)

Ana ci gaba da amfani da kirkirarriyar basira (AI) cikin sauri a fannoni da dama a fadin duniya.
Kirkirarriyar Basira na saukaka wa dan adam rayuwa a yau / Photo: Getty Images

Kirkirarriyar basira (AI) tana da muhimmanci wajen samar da ci gaba, sai dai ana da fargaba kan tasirin haka. Hoto: Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tana kokarin fito da hanyoyi da tsare-tsare kan kirkirarriyar basira (AI) ta yadda dan Adam zai ci gajiyarta.

Majalisar Dinkin Duniya tana fatan fitar da wani tsari ta yadda za a rika amfani da kirkirarriyar basirar, yayin da fasahar take bunkasa cikin hanzari kafin a ankara. A wannan makon ne majalisar ta shirya yin wani babban taro.

Taron wanda ta yi wa take da "AI for Good Global Summit", wato Babban taro kan Alheran Kirkirarriyar Basira" wanda za a yi a birnin Geneva a ranakun Alhamis da Juma'a kuma zai hada masana 3,000 daga kamfanoni kamar Microsoft da Amazon da jami'o'i da manyan kamfanonin duniya don a samar da tsarin amfani da kirkirarriyar basirar.

"Fasahar tana bunkasa cikin hanzari," in ji Doreen Bogdan-Martin wacce ita ce shugabar hukumar sadarwa ta duniya ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta shirya taron.

Za a fitar da tsari

"Abu ne mai matukar muhimmanci masana a fannin kirkirarriyar basira su taru waje guda kuma su tattauna yadda za a rika tafiyar da shi," kamar yadda ta shaida wa manema labatai.

Bogdan-Martin ta ce wajibi ne kirkirarriyar basirar ba za ta ta'azzara matsalolin rashin daidaito da addini da jinsi da siyasa da al'ada da sauransu ba.

"Bai kamata a zuba ido ba. Bani Adam ya dogara a kanta. Saboda haka ya kamata mu dukufa kuma mu yi bakin kokarinmu wajen cewa kirkirarriyar basirar ba ta cutar da makomar mu ba," in ji Bogdan-Martin.

Ta ce taron zai yi nazari kan hanyoyin da suka dace a rika amfani sa kirkirarriyar basirar.

Mahalarta babban taron sun hada da masana a bangaren shugabanci da kasuwanci, kuma taron yana so ne a lalubo hanyoyin da za a ciyar muradin MDD a fannin kiwon lafiya da sauyin yanayi da talauci da yunwa da kuma tsaftataccen ruwa.

Makomar jama'a

"Wannan babban taron zai taimaka mana wajen gano hanyar da kirkirarriyar basirar za ta amfani bani Adam," in ji Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

Sai dai masu son ci gaban da kirkirarriyar basirar ta kawo suna jinjinawa fasahar kan yadda ta sauya al'umma ciki har da yadda ake yin aiki da fannin kiwon lafiya, wasu kuma suna nuna damuwa ne kan yadda za ta iya kawo cikas ga dimokradiyya.

"Muna tsakiyar wata guguwa ce bayan samun wannan fasahar mai tasiri sosai — ba na tunanin basira ce mafificiya — saboda ta yadu sosai kuma ta taimaka wa rayuka, sai dai ba mu shirya mata ba," in ji wani dan kasuwa mai amfani da AI Gary Marcus.

"Muna wani muhimmin mataki ne a tarihi, ko dai mu yi abin da ya dace kuma mu kafa tsarin tafiyar da duniyar da muke bukata, ko kuma mu yi kuskure kuma mu yi rashin nasara mu samu kanmu a wurin da ba ma so, wato inda kamfanoni 'yan kalilan suke juya mutane masu tarin yawa ba tare da hangen nest ba," in ji shi.

TRT Afrika