Kudurin ya biyo bayan kone-konen Kur'ani da ake yi kwanan nan a wasu yankunan Turai. / Hoto: AP Archive

Babbar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da gagarumin rinjaye kan matakin kira ga kasashe su saka himma wajen hana nuna kiyayya ga addini.

Wannan ya faru ne bayan kona Kur'ani da aka yi ta yi a Turai. Matakin ya samu tawaye daga kasashen Yammacin duniya, wadanda suke ganin tsaurara matakan zai janyo gwamnatoci su taka batun 'yancin fadin albarkacin baki.

Zauren Majalisar Kare Hakkin Dan adam ya kaure da tafi a ranar Larabar, bayan da kudurin ya samu rinjaye da kuri'a 28-12, inda kasashe bakwai suke kauracewa kada kuri'a.

Kasashen Pakistan da Falasdinu ne suka gabatar da kudurin, inda yawancin kasashe masu tasowa na Afirka, da China da Indiya, da kasashen Gabas ta Tsakiya suka mara musu baya.

Bayan kada kuri'ar, Ambasada Khalil Hashmi na Pakistan ya jaddada cewa matakin ba ya "nufin kawar da 'yancin fadar albarkacin baka". Amma yana nufin samar da daidaiton hikima tsakanin 'yanci da hakkokin na musamman.

Ya ce, "Masu bijirewa kudurin wadanda tsiraru ne zauren, sun yi hakan ne sakamakon rashin manufarsu ta sukar wulakanta Kur'ani ko sauran littattafai masu tsarki a bainar jama'a".

Ya kara da cewa, "Ba su da karfin hali a siyasance, da shari'a, da ma hukumance, wajen la'antar wannan abu, kuma wannan shi ne mafi karancin abin da majalisar nan za ta bukace su yi.”

Kasashen yamma sun bijire wa mudurin

Kasashen da suka kada kuri'a amincewa su ne:

  • Aljeriya
  • Ajantina
  • Bangladesh
  • Bolivia
  • Kamaru
  • China
  • Ivory Coast
  • Cuba
  • Eritrea
  • Gabon
  • Gambia
  • Indiya
  • Kazakhstan
  • Kyrgyzstan
  • Malawi
  • Malaysia
  • Maldives
  • Moroko
  • Pakistan
  • Qatar
  • Senegal
  • Somalia
  • Afirka ta Kudu
  • Sudan
  • Ukraine
  • Hadaddiyar Daular Larabawa
  • Uzbekistan
  • Vietnam.

Kasashen da suka yi adawa da kudurin su ne:

  • Amurka
  • Birtaniya
  • Belgium
  • Costa Rica
  • The Czech Republic
  • Finland
  • Faransa
  • Jamus
  • Lithuania
  • Luxembourg
  • Montenegro
  • Romania.

Turkiyya ba ta cikin masu damar kada kuri'a, sakamakon tana da matsayin mai saka idon ne a majalisar ta kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin DUniya.

Haka nan, kasashen Birtaniya da Amurka, da ma kasashen Tarayyar Turai sun yi adawa da kudurin sukar kona Kur'ani, a yayin wata muhawara ranar Talata a zauren majalisar kare hakkin dan adam, bayan yaduwar masu harin littafin Kur'anin mai tsarki.

Kudurin yana zuwa ne bayan kona Kur'ani da aka yi a Sweden, inda aka yi kira ga kasashe su saka himma wajen hana nuna kiyayya ga addini, wadda ka iya jawo gaba da tashin hankali.
TRT World