Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta ce farashin kayayyakin abinci sun fadi a watan Mayun 2023, faduwa irin ta ta farko cikin shekara biyu, yayin da farashin man girki da dangogin hatsi da madara suka sauka, su kuwa sikari da nama hawa farashinsu ya yi.
Jerin farashin kayan abinci da hukumar FAO ta fitar, wanda ta bi diddigin kayan abincin da aka fi amfani da su a duniya, ya nuna saukar farashin daga digo 127.7 na watan da ya gabata zuwa digo 124.3 a watan Mayu, kamar yadda hukumar ta fada a ranar Juma'a.
Farashin watan Mayun shi ne mafi karanci tun watan Afrilun 2021 kuma hakan na nufin jerin farashin a yanzu kashi 22 cikin 100, raguwar da ba a samu irinta ba tun watan Marsi din 2022 da aka fara yakin Rasha da Ukraine.
Farashin kayan abinci dangogin hatsi na jerin FAO sun sauka da kusan kashi biyar a Mayu fiye da na watannin baya, abin da ake ganin ya faru ne sakamakon tsawaita yarjejeniyar wucewa da hatsi ta Bahar Aswad daga Ukraine da aka yi ne.
Amma farashin shinkafa a duniya ya karu ne a watan Mayun, saboda rashin fitar da ita sosai daga kasashen da ke samar da ita, a cewar FAO.
A watan da ya gabata hukumar ta bayyana damuwarta kan hauhawar farashin kayan abinci.