Kasashe irin su Iraki, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa da Maroko sun yi sammacin jakadun Sweden da ke kasashensu don nuna bijire wa wannan mummunan aiki. / Hoto: AFP

Kungiyar kasashen Musulmai ta Organisation of Islamic Cooperation (OIC) ta yi kira a dauki matakai da za su sa nan gaba a daina Alkur'ani, kwanaki kadan bayan wani mutum ya kona littafin mai tsarki a wajen wani masallaci a birnin Stockholm.

Kungiyar, wadda ke da mazauni a birnin Jeddah, ranar Lahadi ta yi kira ga dukkan mambobinta su "dauki matakin bai-daya domin hana sake aukuwar irin wannan batu na cin mutuncin" Alkur'ani, a cewar wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na "musamman".

Sakatare janar na kungiyar Hissein Brahim Taha, ya "jaddada bukatar aikewa da sako karara game da kin amincewa da cin mutuncin" Alkur'ani.

"Dole mu aika da sakonnin tunawarwa ga al'ummar duniya game da bukatar gaggawa ta daukar mataki, wanda ya bayyana karara cewa haramun ne nuna kiyayya game da wani addini."

Taha ya yi Allah wadai da matakin da dan kasar Sweden dan asalin Iraki ya dauka na gudanar da wannan "mummunan aiki", kamar yadda sauran duniya ta yi ciki har da gudanar da jerin zanga-zanga a ofishin jakadancin Sweden da ke babban birnin Iraki.

Gudanar da bincike

Kungiyar mai mambobi 57 ta gana a hedikwatarta da ke Jeddah domin yin raddi game da kona Alkur'anin da Salwan Momika, mai shekara 37, ya yi a Sweden.

Ya dauki matakin ne a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Sallar Layya a fadin duniya da kuma kammala aikin Hajjin bana, lamarin da ya harzuka Musulmai.

Tuni kasashe irin su Iraki, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa da Maroko suka yi sammacin jakadun Sweden da ke kasashensu don nuna bijire wa wannan mummunan aiki.

'Yan sandan Sweden sun bai wa Momika damar kona littafin mai tsarki ne don yin biyayya ga dokar da ta ba shi damar bayyana albarkacin bakinsa, ko da yake daga bisani hukumomi sun ce sun soma bincike kan lamarin.

AFP