Kungiyar kasashen Musulmi ta bukaci a dauki tsatsauran mataki kan wannan lamari. Hoto/AA

Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da kona Alkur’ani a Sweden a matsayin hanyar tofa albarkacin baki inda ya ce lamarin ya yi matukar bata masa rai.

“Duk wani littafi da ake masa kallon mai tsarki dole ne a girmama shi da wadanda suka yarda da shi,” kamar yadda Fafaroman ya bayyana a yayin wata tattaunawa da jaridar Al Ittihad ta Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Litinin.

“Na ji haushi na kuma kyamaci wannan mataki. Kada a rinka amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki wurin tozarta wasu kuma barin hakan abin Allah wadai da tir ne.”

Wani mutum ya yaga Alkur’ani sa’annan ya kona shi a Stockholm babban birnin Sweden a makon da ya gabata, abin da ya ja aka rinka tir da lamarin daga kasashe da dama ciki har da Turkiyya wadda Sweden din ke bukatar goyon bayanta domin shiga kungiyar NATO.

Duk da cewa ‘yan sanda a kasar ta Sweden sun ta watsi da bukatar da aka yi ta kaiwa a gabansu ta neman a yi zanga-zangar, amma kotu a kasar ta amince da batun zanga-zangar inda ta ce hanin da ‘yan sandan suka yi take hakkin bil adama ne.

A ranar Lahadi, kasashen Musulmi 57 sun bayyana cewa akwai bukatar daukar dunkulallun matakai domin dakile yunkurin wulakanta Alkur’ani da kuma yin doka ta kasa da kasa domin dakile kiyayyar addini.

AFP