Majalisar Dinkin Duniya MDD ta ba da wani labari mai ban tsoro kan yanayin samar da abinci a duniya a ranar Laraba, inda ta ce, a shekarar da ta gabata mutum biliyan 2.4 ba su samu wadataccen abinci ba.
MDD ta ce daga cikinsu akwai mutum miliyan 783 da suka fuskanci matsananciyar yunwa da kananan yara miliyan 148 da suka yi fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.
A rahoton da hukumomin MDD biyar suka fitar na shekarar 2023 kan yanayin tsaro da abinci mai gina jiki, sun ce adadin mutanen da suka yi fama da matsalar yunwa a duniya a tsakanin 2021 zuwa 2022 ya bayyana yiwuwar samun karin wurare da dama da suka fuskanci matsalar karancin abinci.
Rahoton ya yi nuni da yankin Yammacin Asiya da Caribbean da kuma Afirka inda kashi 20 cikin 100 na al'ummar nahiyoyin ke fama da yunwa, fiye da kashi biyu na matsakaicin yawan adadin duniya.
“Ba a gama farfadowa daga illar da annobar cutar korona ta haifar a duniya ba, sannan ga yakin da ake yi a Ukraine wanda ya shafi abinci masu lafiya da gina jiki,” a cewar Qu Dongyu, babban daraktan Hukumar Samar da Abinci da Ayyukan Noma a cikin wata sanarwa da ya fitar.
"Wadannan su ne sabbin abubuwan da ake fama da su "a rayuwa ta yau da kullum" inda sauyin yanayi da rikice-rikice da rashin samun daidaito a tattalin arziki, suke dada tura mutanen da ke kan iyaka zuwa gabar rashin samun sauki ko kadan," in ji Qu Dongyu.
Masanin tattalin arziki na hukumar FAO Maximo Torero ya ce kididdigar farashin abinci ta FAO tana raguwa kusan wata 15 kenan, kuma ana ci gaba da samun "hauhawar farashin abinci."
Abinci mara kyau
Sai dai ya ce bai san ko za a sabunta yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar jigilar tan 32 na hatsi zuwa kasuwannin duniya da kuma kokarin shawo kan matsalolin da ke hana shigar da hatsi da takin Rasha ba idan har ta kare a ranar 17 ga watan Yuli, domin “hakan ba zai yi kyau ga kasuwanni ba.”
Idan ba a sabunta yarjejeniyar da wuri ba "tabbas za a samu sabuwar hauhawar farashin abinci," amma nawa da kuma tsawon wane lokaci za a dauka zai dogara ne a kan yadda kasuwanni ke amsawa, in ji shi.
A cewar rahoton, yadda mutane ke samun abinci mai kyau ya tabarbare a duniya. Fiye da mutum biliyan 3.1 - kashi 42 cikin 100 na al'ummar duniya - ba su samu ingantaccen abinci ba a shekarar 2021, karin kusan mutum miliyan 134 kenan aka samu idan aka kwatanta da 2019, in ji shi.
A yayin kaddamar da rahoton Torero ya shaida wa taron manema labarai cewa rage yawan mutanen da ke cin abinci mara kyau “babban kalubale ne, domin a zahiri hakan na nuna mana cewa akwai bukatar mu sauya yadda muke amfani da albarkatunmu na fannin noma, a tsarinmu na noma da samar da abinci."
A cewar sabon binciken da aka fitar, ya ce, tsakanin mutum miliyan 691 da miliyan 783, an samu wadanda suka yi fama da mummunar matsalar rashin abinci mai gina jiki a 2022, kusan mutume miliyan 122 aka samu daga cikin miliyan 735, kenan fiye da adadin da aka samu a 2019 kafin bullar cutar korona.
Kalubale mai ban tsoro
Torero ya ce hasashen MDD na shekarar 2030 ya nuna cewa har yanzu mutum miliyan 600 za su kasance cikin fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a shekarar 2030, nesa da cimma burin ci gaba na MDD “Zero Hunger ” a wannan lokacin.
Jigon rahoton shugabannin hukumomi biyar na MDD da suka hada da hukumar samar da abinci da ayyukan noma FAO da Shirin samar da Abinci na Duniya WFP da Asusun Raya Aikin Noma na Duniya FAD da Asusun kula da kananan yara UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya bayyana cewa akwai babban kalubabe mai ban tsaro wajen cimma burin MDD Duniya kan samar da “Zero Yunger.”
Sun yi kira da a ninka kokarin da ake yi "don sauya tsarin samar da abincin da aikin noma tare da amfani da dabarun da aka samar" don cimma burin da aka sa a gaba.
Dangane da yara kuwa, rahoton ya ce suna ci gaba da fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, ban da yara miliyan 148 da ke kasa da shekara biyar da haihuwa masu fama da wannan matsalar, miliyan 45 daga cikinsu na fama da “rashin girman jiki,” yayin da matasa miliyan 37 ke fama da matsalar tsananin kiba.
Matsalar kudi
Torero ya ce, hukumomin biyar sun kuma duba yadda ake samun karuwar al'umma a birane, inda suka gano cewa mutanen karkara da kananan birane na taka rawa wajen cinye kayayyakin da ake samarwa ga al’umma.
“A da can, mun yi hasashen cewa mutanen karkara za su ci abin da suke nomawa ne, amma ba haka lamarin yake ba,” in ji shi.
Yana mai bayanin da cewa a yankunan karkara ana sayen kusan kashi 30 cikin 100 na kwandon abincin iyali daga kasuwa ne, sannan a yankunan kananan birane adadin ya fi yawa, lamarin da ke da tasiri ga abinci mai gina jiki saboda yawan cin abincin da aka sarrafa.
Wani babban masanin tattalin arziki na WFP Arif Husain ya shaida wa manema labarai a wani taron tattaunawa da aka yi da shi cewa, a shekarar 2022 lokacin da ake ci gaba da yaki a UKraine, matsalar abinci ba ta tabarbare sosai ba saboda masu ba da agaji sun kara kaimi wajen ba da kusan dala biliyan 14.2.
Sannan kuma hukumar ta iya ba da taimako ga mutum miliyan 160, sama da adadin mutum miliyan 97 a shekarar 2019.
"Damuwataa anan ita ce, a nan gaba za mu samu raguwar kudade masu yawa," in ji shi, yana mai nuni da gudunmawar da WFP ta bayar ta dala biliyan 4.2 a makon da ya gabata, an samu ragin kasa da kashi 29 cikin 100 idan aka kwatanta da abin da ta bayar a shekarar da ta gabata.