Ta yi aure kuma tana zaune a Istanbul inda Bahadir ta ji labarin abin da ya faru a kasarta. Hoto: AA

Semiha Bahadir, wadda ke zaune nesa daga wurin da aka yi kisan kare-dangin 1992 zuwa 1995, tana fama da rashin da ta yi na ‘yarta mai shekara uku a 1993 sakamakon wannan bala'i, sannan ta yi alhinin mutuwar ‘yan uwanta ‘yan Bosnia.

Ta yi aure kuma tana zaune a Istanbul inda Bahadir ta ji labarin abin da ya faru a kasarta.

A matsayinta na wadda ta kware a bangaren halayar dan adam, an koyar da ita yadda za ta yaki firgici musamman ta bangaren ilimin halayyar dan adam da zamantakewa.

Sai dai babu wani abu a duniya da zai sa ta shirya wa irin bayanan da suka fito na wadanda suka yi kisan kare-dangin Srebrenica – a lokacin da dakarun Serb suka kashe Musulmai 8,000 maza da yara kanana bayan mamaye garin a ranar 11 ga watan Yulin 1995 a matakin karshe na yakin.

Majalisar Dinkin Duniya a hukumance ta ayyana kisan da aka yi a matsayin kisan kare-dangi. Shekara daya bayan hakan ne Yugoslavia ta wargaje a 1991, inda ‘yan kabilar Serb na Bosnia suka yi adawa da ‘yancin Bosnia da Herzegovina tare da aiwatar da kisan kare-dangi kan kabilun, bayan sun soma mamaya mafi tsawo a lokacin.

Kamar yadda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayyana kan Yugoslavia, sama da mutum 100,000 suka rasu a yakin, akalla kashi 70 cikin 100 a cikinsu ‘yan Bosnia ne.

Yakin ya raba sama da farar-hula miliyan biyu da muhallansu, kuma dubban daruruwan ‘yan Bosnia sun yi kaura zuwa Turkiyya.

An nemi Bahadir ta yi amfani da baiwar da take da ita domin taimakon ‘yan uwanta ‘yan Bosnia wadanda suka tsira daga yakin.

Bahadir ta shiga cikin daruruwan matan Turkawa domin taimaka wa ‘yan gudun hijira musamman mata da yara.

Kungiyar agaji ta Turkish Crescent da sauran kungiyoyin agaji su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen taimakon ‘yan gudun hijira 350,000 wadanda suka nemi mafaka a larduna daban-daban na Turkiyya.

A jajiberin cika shekara 28 da kisan kare-dangin – wanda aka rubuta a tarihi a matsayin mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu, Bahadir ta yo bayanin zaluncin da aka aikata kan Musulman Bosnia inda ta rinka bayar da labarin daga abin da ta sani daga mu’amalar da ta yi da wadanda suka tsira.

“Ina so na bayyana abubuwa a karon farko a kan Srebrenica... Abu ne wanda na kulle shi a cikin zuciyata tsawon shekara 20,” in ji Bahadir wadda a yanzu take da shekara 57.

Ta tuna da yadda ta soma kokarin warkarwa da kuma sauya mutanen. “Tsananin takaici daga ciki da waje duk ya sa ni na rasa yadda zan yi,” in ji Bahadir, inda muryarta ke cike da kyarma kan yadda lamarin ya faru.

“Sai ba da dadewa ba na gano cewa mancewa da kuma ci gaba da rayuwa yadda take ba abu ba ne mai yiwuwa a cikin wannan tsananin.

Hakan ya sa na sauya yanayin tambayar: ta ya zan yi rayuwa da wannan takaicin?” Bisa kwarewar da take da ita, sai ta soma kwantar da hankalinta bayan fahimtar juriyar dan adam.

Abin da Bahadir ke so ya zama a bayyane: ta taimaka wa mutanenta samun karfin gwiwa da dawowa da su yadda suke domin su sake gina rayuwarsu.

Wadannan labarai ne na ‘yan Bosnia wadanda suka ga bangaren mafi muni na rayuwa kuma suka rayu domin su bayar da labari.

‘Ku fada musu, ta yadda za a gane me muke nufi’

A wani muhimmin lokaci a lokacin yakin, Alija Izetbegovic – shugaba na farko na Bosnia da Herzegovina wanda ake kuma kira ‘sarki mai basira’ – ya nemi matarsa Halida, wadda a lokacin take zaune a Santambul bayan da aka cece ta daga kasar da yaki ya mamaye.

A lokacin, Bahadir ta rinka aiki da Halida a matsayin mai yi mata tuntuba da kuma fassara tsawon shekara shida, har hakan ya sa suka kulla alaka mai karfi a tsakaninsu.

Bahadir ta tuna a lokacin da Izetbegovic take ba ta labari kan kalaman Alija Izetbegovic ta wayar tarho a lokacin da ya kira ta: “Ki gaya musu, mun fahimta.”

Sai ya ba matarsa umarnin ta jawo hankalin duniya kan matsalolin jin kai da ke faruwa a kasarshi da kuma yankin Balkan baki daya.

Halida Izetbegovic da Semiha Bahadir sun hada wani taro a Jami’ar Marmara, da zummar nuna wa jama’ar Bosnia tarihi kan yadda al’adar Balkans take.

Taron ya jawo mutane daban-daban daga kabilu inda abin mamaki har da Izetbegovic da Bahadir. “Zalunci ba shi da yare ko addini ko kabila ko lokaci,” kamar yadda Bahadir ta shaida wa TRT, inda take nuna goyon bayanta ga ‘yan Bosnia a lokacin taron.

Gangar jikin da ta yi nisa da ruhinta

Bahadir ta nuna a lokacin da ta hadu da wata yarinya ‘yar Bosnia mai shekara shida wadda ta shaida yadda sojojin Serbia suka yi wa mahaifiyarta da kakarta da sauran matan da ke iyalinta fyade na taron dangi.

Yarinyar – wadda aka boye sunanta domin kare mutuncinta – iyalinta ne suka boye ta a cikin duro a lokacin da sojojin Serbia suka fado musu cikin gida.

An fitar da mahaifinta, da kakanta da sauran danginta daga gidan kuma bata sake ganinsu ba.

An ceto ta kuma aka kawo ta sansanin ‘yan gudun hijira a Turkiyya, inda ta samu nutsuwa karkashin mai lura da ita, Bahadir.

“Ita ce ta zamo ta farko da na yi aiki da ita a matsayin kwararre,” a cewar Bahadir. “Ga dai gangan jiki, ga kuma ruhin da aka lahanta, amma ba mu ga abin da ya hade biyun ba.”

Sakamakon kokarin Bahadir, yarinyar ta samu cigaba sosai.

Ta ce “Na ya yadda kyawawan abubuwa suke iya samuwa daga irin wannan yanayi mai hadari”. “Wannan yarinyar ta zo ta samu waraka, ta fara magana da harsuna bakwai tana shekara 16. A yanzu tana da kokari kuma tana magana da muryar babba a tarukan duniya.”

‘Ubangiji ya dauke 17, anna ya ba mu 70,000’

Wata kaka a Bosnia, ita ce ake wa kallon tsatson dangin, kuma ana girmama ta da mutuntatawa a cikin al’ummar Bosniak.

"Radadi wani abu ne da ke zaburarwa don kawo sauyi a duniya, mai haske da lumana da dattako."

A yayin yakin Bosnia, wata kaka ta shiga ran Bahadir a tsakiyar yamutsin. Duk da rasa ‘yan uwa 17, matar mai shekara 85 ta cigaba da karfafar kowa. Ta cigaba ta zama mai kyakkyawan fata da godiyar Allah, duk da cewa jika daya ya rage mata, inda suke rayuwa a sansanin gudun hijira a Turkiyya.

Yayin wata ziyara zuwa wani sansanin, Bahadir ya yi wata zantawa da Nena.

“Me ya sa wadannan matan suke cikin kanfa haka?” ya tambaya, yana nufin sauran matan Bosnia da suke sansanin.

“Ba ma cikin radadi. Wadanda suka mutu sun yi shahada. Allah yana ba su masauki. Wadanda suke da rai suna karkashin kulawar uwa mai tausayi, wato Turkiyya,” a cewar Nena ta bakin Bahadir.

Duka da wannan bala’i, imanin Nena ga Allah bai samu tasgaro ba, in ji Bahadir.

“Ubangiji ya dauki 17, amma ya ba mu 70,000 kari,” haka ta ji tsohuwar tana fadi.

Ta bayyanawa Bahadir cewa radadin wani kaimi ne na kawo sauyi a al’umma da kuma duniya”.

Wannan salo yana kama da irin kyakkyawan tunanin da aka gani a kalaman Alija Izetbegovic: “Sun yi kokarin bine mu, amma ba su san mu iri ba ne.”

“Idan muka manta, za mu ci gaba da kashe mu duk shekara 50”

Bahadir ta ki amincewa ta kira kisan kiyashin da 'yaki, wanda shi ne sunan da ake kira kisan da aka yi wa Musulmin Bosnia a hukumance. “Kiran abin da ya faru a Bosnia da sunan yaki, rashin adalci ne ga ‘yan Bosnia; ai yaki lamari ne tsakanin masu kamanceceniyar karfi.”

Ta nuna sakon da take son isarwa ta hanyar nuna yadda ‘yan Sabia suka yi amfani da fyade, a matsayin makamin yaki, da kuma yadda aka hana mata zubar da cikinsu, a wani salon tursasawa wajan kawo gibi a zuriyar Musulmin Bosnia.

Ta hanyar wannan ta’annati, an lahanta turaku biyar na al’umma, wato tsaron rayuka, da na zukata, da na dukiya, da na tsatso, da ‘yancin addini, a yayin yakin Bosnia. Wannan ya rusa duka matakan rayuwar dan Adam.

Bahadir ta yi nuni kan bukatar sahihan bayanai, da rashin manta baya, da abin da ya faru, saboda ka da azzaluman su kara rura wata musibar a gaba.

Bahadir ya jaddada gargadin da kakanta ya yi, “Idan muka manta, za a ci gaba da kashe mu duk shekara 50.”

Ta ce kalamansa suna jaddada tunanin marigayi Alija Izetbegovic, wanda ya taba yin gargadin cewa, “Duk abin da kuke, kar ku manta da kisan kare dangin. Saboda duk kisan da aka manta da shi, to maimaitashi ake yi.”

TRT World