Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya ya ce Falasdinawa ba su da 'yancin komawa gidajensu.
''Bari na fayyace muku, babu wata dama ko hakki da Falasdinawa suke da su na komawa matsugunansu. Duk kun san da wannan,'' kamar yadda Gilad Erdan ya shaida wa taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis.
"Bukatar mayar da miliyoyin iyalai 'yan gudun hijira tamkar kawar da 'yancin Yahudawa ne, kuma hakan ba zai taba faruwa ba," in ji shi.
A halin yanzu akwai Falasdinawa 'yan gudun hijira miliyan 5.9 a Gaza, da kuma yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma kasashe da ke makwabtaka da yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA.
Kazalika Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya bayyana cewa akwai sama da 'yan Isra'ila 700,000 da suke zaune a yankin Falasdinawa da suka mamaye ciki har da Gabashin birnin Kudus.
Ya ce "mamayar Isra'ila na zama tamkar mamaya ce ta 'yan mulkin-mallaka" yana mai cewa hanya daya tilo da kasashen duniya za su iya kawo karshen hakan ita ce ta magance yanayin irin na 'yan mazan-jiya da 'yan mulkin-mallaka.
Ya yi kira a mayar da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya zuwa wani shiri na aiki tare da daukar matakan da kowace kasa mai son ''zaman lafiya'' za ta dauka don kawar da Isra'ila daga yin mamaya.
Mamayar Isra'ila
Isra'ila ta mamaye Gabashin Kudus, inda Masallacin Al Aqsa yake, a lokacin yakin Larabawa da Isra'ila a shekarar 1967.
A shekarar 1980 ta mamaye Birnin Kudus baki daya, matakin da kasashen duniya ba su amince da shi ba.
Dakarun Isra'ila da tsagerun Yahudawa sun ci gaba da kai hare-hare Masallacin Al Aqsa don tunzura Falasdinawa, kuma a 'yan shekarun baya-bayan nan hare-haren na karuwa kuma suna kazanta.
An yi ta fama da tashe-tashen hankula da zaman dar-dar a 'yan watannin nan a yankin gabar yammacin kogin Jordan sakamokon yawan kai farmaki da cikin da Isra'ila ke kaiwa garuruwan Falasdinawa.