An kai hari da wani babur da aka sanya wa abubuwan fashewa a wajen birnin Damascus kusa da wani hubbare da 'yan Shia ke kai ziyara lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum shida.
An kai harin, wanda kuma ya jikkata mutane da dama a jajiberin ranar Ashura, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana, inda ta ambato wasu bayanai daga ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar.
Ministan Lafiyar Gwamnatin Syria Hassan al Ghabash ya bayyana a wata sanarwa cewa mutum 26 da suka ji rauni a harin unguwar Sayida Zeinab suna karbar magani a asibitoci daban-daban.
Wasu kuma 20 ana ba su magani a wurin da abin ya faru yayin da aka sallami wasu, a cewarsa.
Tun da farko mahukuntan kasar sun ce an boye bam din ne a cikin wata motar tasi, amma daga baya sun ce an boye bam din ne a jikin wani babur wanda ya fashe kusa da wata tasi.
Wata kungiyar Birtaniya ta kare hakkin dan Adam wadda kuma take sanya ido kan yakin da ke faruwa a kasar, Syrian Observatory for Human Rights, ta ce wata mata tana cikin mutanen da suka mutu kuma 'ya'yanta uku sun jikkata.
Kungiyar ta ce harin ya faru ne kusa da wurin da dakarun sa-kai na İran suke, kasar İran kawa ce ga gwamnatin Syria karkashin jagorancin Shugaba Bashar Assad da Rasha a yakin basasar da aka kwashe shekara 13 ana fafatawa.
Hotunan da kafar yada labarai ta Al Ikhbariya da kuma kafar yada labaran da ke goyon bayan gwamnati suka wallafa sun nuna wata tasi da ta kone kurmus, inda mutane da yawa suka kewaye ta da kuma wasu mutane sanye da kakin sojoji.
Tutocin ranar Ashura masu launin kore da ja da kuma baki sun kasance a jikin gine-gine a unguwar.
A wani bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, wasu mutane sun dauko wasu mutum biyu da ke cikin jini kuma suna kiraye-kirayen neman agaji.
Gilasan shagunan da ke kusa sun tarwatse yayin da daya daga cikin shagunan ya kama da wuta.
An sanya wa unguwar sunan hubbaren Sayida Zeinab wato jikar Manzon Allah (SAW).
Kare hubbaren ya kasance wani aiki ne na mayakan 'yan Shia da ke mara wa Shugaba Assad baya a shekarun farkon tashin hankalin yayin da rikicin ya rikide zuwa adawa da gwamnati da komawa yakin basasa daga baya.
Ranar Ashura ita ce ranar 10 ga watan Muharram a kalandar Musulunci, watan yana daga cikin watanni masu tsarki ga 'yan Shia.
Rana ce ta tunawa da kisan jikan Manzon Allah (SAW) wato Imam Hussein da kuma sahabbai 72 a garin Karbala a karni na 7 a kasar Iraki a yanzu. Ranar Ashura ce kololuwar lokacin nuna alhinin.
Wannan harin bam shi ne na biyu a unguwar Sayida Zeinab a yayin da ake tunawa da zagayowar ranar Ashura.
A ranar Talata, kafar yada labarai ta kasar Syria ta ce 'yan sanda sun ce fararen-hula biyu sun jikkata yayin da wasu abubuwan fashewa suka tashi daga jikin wani babur.