NASA

Gaskiyar na nan a bayyane – amma za mu yi aiki sosai.

Masana kimiyya a wajen taro a bainar jama’a na farko da hukumar sararin samaniyar Amurka, NASA ta gudanar game da “wasu halittu masu yawo a sararin samaniya da ba a iya cimma su” (UFO), sun yi kira da a kara kaimi sosai don tantancewa da nemo asalin wadannan daruruwan halittu da ake gani.

A shekarar da ta gabata NASA ta ce tana nazari kan wasu abubuwa da aka gano na yawo a sama wadanda ba tauraron dan adama ba, kuma ba halittu masu rai ba – batun da ya dade yana ci wa mutane tuwo a kwarya, amma kuma masu binciken kimiyya suka yi biris da shi.

Wasu masu bincike masu zaman kansu 16 sun shirya gabatar da rahoton bincikensu nan da karshen watan Yuli, inda taron da suka yi a ranar Alhamis din nan ya zama taro na karshe.

“Bayanan da ake da su a yanzu haka da kuma rahotannin shaidun gani da ido ba za su wadatar ba don kawo karshen binciken,” in ji masanin kimiyyar sararin samaniya David Spergel wanda shi ne jagoran binciken.

Ya kara da cewa ‘Daya daga cikin darussan da muka gano shi ne bukatar karin bayanai da kayan aiki mafiya inganci tare da sanya idanu a lokuta da dama.”

“Yar jaridar kimiyya Nadiya Drake ta ce akwai bayanai sama da 800 da aka tattara a cikin shekara 27, wanda kaso biyu zuwa uku ke bayyana wadannan abubuwa masu yawo a sama da ba a iya cim musu na ta’ajibi ne.

Ana kiran wadannan da “Duk wani abu da ba a iya fahimtar sa ta hanyar aiki ko maganadisu” ko “Wani abu da ke rikitar da tunanin dan adam”.

Dunkulallun halittu a sama

A wani bayani da daraktan kimiyya na Pentagon, Sean Kirkpatrick ya nuna sabon bidiyo na wasu abubuwa biyu da ke yawo a sama, kamar yadda jirgin yaki samfurin P3 ya dauko hotonsu, daga baya kuma suka zama guda uku.

Jirgin saman soji na P3 ya gaza cimma wadannan abubuwa, kuma matukin ya sanar da me ya faru. Amma daga baya masu nazari sun bayyana cewa abubuwan na da nisa sosai, kuma watakila jiragen sama ne da suka lula can sama suke tafiya.

Kirkpatrick ya kara da cewa “Irin wannan abu ne ke bayyana tare da rikitar da kwararrun matukan jirage da ma maganadisun bincike.”

Ya ce ‘Idan ba su da tabbacin me suka gani, su bayar da rahoto, hakan ne abinda ya dace su yi.”

Wani misali guda kuma da yake sake daure kai game da dunkulallun abubuwa masu kama da karfe da ke yawo a sama shi ne wadanda jirgin sama mara matuki samfurin MQ-9 ya hango a wani waje da ba a bayyana ba da ke Gabas ta Tsakiya, in ji Kirkpatrick a lokacin da yake sake kunna bidiyon ga majalisar dokoki a watan da ya gabata.

“Wannan misali ne na karara na abunda muke yawan gani. Muna ganin wadannan abubuwa a fadin duniya.”

A yayin da NASA ta fi mayar da hankali kan binciken duniyar rana da yadda aka rayu a sauran duniyoyi, a karon farko tana bincikar wasu halittu da ake gani a samaniyar duniyar Earth.

Inkarin ganin wani abu

A baya dai hukumar ta dinga inkarin ana ganin wani abu – inda take tabbatar da kawai tsoron dodanni ne yake janyowa ake ganin hakan.

Dan Evans ya bayyana cewa da yawa daga malaman kimiyya da suka shiga binciken sun dinga fuskantar kyara da hantara ta yanar gizo saboda kawai sun shiga aiki.

Ya kara da cewa “Yana da muhimmanci a fahimci yadda duk wata kyara ko hantara ga malaman kimiyyarmu, ba za su yi komai ba illa janye hankulan malaman daga binciken, wanda yake bukatar girmamawa da ladabi daga al’umma.”

Aikin NASA, wanda ya ta’allaka kan abubuwa da dama, ya bambanta da binciken Pentagon, duk da cewar dukkan bangarorin na ayyukan kimiyya tare.

Drake ta takaita da cewa “Ya zuwa yanzu, a ayyukan binciken kimiyya, babu wata hujja da ke nuna asalin yadda UAV suka samu.”

TRT World