Wannan wani hoto ne daga kamfanin OceanGate na sundukin da ke tafiya a karkashin teku wanda aka sanya wa sunan Titanic, kuma ake kai ziyarar zuwa inda tarkacen tsohon jirgin ruwa Titanic yake a karkashin teku. Sundukin ya bace ne tun ranar 18 ga watan Yuni Hoto: AP Archive] AP ARCHIVE      

Dakarun gabar tekun Amurka ya tabbatar da cewa tawagar masu aikin ceton da neman jirgin saman sun jiyo "wani kara daga karkarshin teku" a wurin da ake bincike inda sundukin ya bace kwana biyu da suka wuce.

Jami'ai a Amurka da Kanada suna kokarin gano sundukin yayin da lokaci ke kurewa wajen gano sundukin da ke dauke da mutanen da za su je yawon bude ido wajen tarkacen tsohon jirgin ruwan Titanic a tekun Arewacin Atlantic.

Lokacin da sundukin ya bace, yana iskar oxygen da mutanen da ke ciki suka shaka ta tsawon sa'a 96 – wato tsawon kwana hudu kenan.

"Jirgin saman Kanada na P-3 ya ji yo kara a inda ake neman jirgin. Saboda haka, akwai wata na'ura ta ROV don gano asalin inda karar ya fito," kamar yadda hukumar dakarun gabar ruwan Amurka suka bayyana a shafinta na Twitter a ranar Laraba.

Sakamakon bincike da jirgin ROV ya fitar ya ce "babu bayanan da aka samu amma za a ci gaba da bincike," kamar yadda hukumar sojan ruwa ta bayyana.

Rashin iskar shaka ta iskar

A ranar Laraba, hukumar dakarun ruwan Amurka ta ce iskar oxygen ta sa'a 40 kadai ta rage wa mutanen da ke sundukin yawon bude ido na Titanic wanda ya bace.

"Binciken da ake ya mayar da hankali a kan saman ruwa da karkashin teku, akwai jirage 130 da aiki da na'urori da dama. Sai dai har yanzu ba mu gano komai ba," in ji Kyaftin Jamie Frederick daga bangaren First Coast Guard District.

Masu bincike suna aiki ne a fadin ruwan da ya kai mil 900 a gabashin Cape Cod, mil 400 a kudancin St.John a Kanada, kuma aiki sosai wanda yake bukatar hadin gwiwa, a cewarsa.

Dangane da aikin ceton, sojan ruwan Amurka "sun ce suna zaune ne a cikin ko ta kwana duk lokacin da za a bukaci taimakonsu," kamar yadda fadar White House ta bayyana.

Sojan ruwan "suna da na'urorin da ke iya bincike a karkashin teku wadanda dakarun gabar tekun ba su da su," kamar yadda Shugaban Majalisar Tsaro John Kirby ya bayyana yayin wata ganawa da manema labarai.

Akwai mutum biyar da ke cikin sundukin ciki har da attajirin Birtaniya Hamish Harding da wani fitaccen Bafaranshe mai linkaya Paul-Henri Nargeolet.

TRT World