NASA ta ji duriyar jirgin ‘Ingenuity’ da ta rasa gano shi tsawon kwana 63 a duniyar Mars

NASA ta ji duriyar jirgin ‘Ingenuity’ da ta rasa gano shi tsawon kwana 63 a duniyar Mars

Duk da cewa ba a gama tabbatar da cewa ko Ingenuity ya sauka lafiya ba, an sanar da cewa har yanzu yana aiki kuma an gano inda yake.
Ingenuity NASA

Hukumar Sararin Samaniya ta Amurka NASA, ta gano dan karamin helikwaftan Ingenuity, da ke zagaye duniyar Mars don gano abubuwan da sai jirgin sama jannatin Perseverance ya dauki makonni kafin ya gano su, bayan shafe wata biyu ba a ji duriyarsa ba.

Gidan talabijin na CNN ya ce an gano jirgin ne a ranar 28 ga watan Yuni.

Tawagar da ke sa ido ta NASA ta daina jin duriyar Ingenuity ne a lokacin da ya yi shawagi karo na 52 ranar 26 ga watan Afrilun, inda ya shafe kwana 63 cur kafin a sake jin duriyarsa.

Duk da cewa ba a gama tabbatar da cewa ko Ingenuity ya sauka lafiya ba, an sanar da cewa har yanzu yana aiki kuma an gano inda yake.

Ingenuity shi ne jirgi na farko da mutum ya kera da ya sauka a wata duniyar lafiya kalau.

Dukkan sadarwar da ke gudana tsakanin helikwaftam Ingenuity da NASA yana tafiya ne ta cikin Rokar Perseverance, kuma ana zaton wani tsauni ne ya shiga tsakanin jiragen biyu da har aka dauki tsawon lokaci ba a ji duriyar helikwaftan ba, in ji hukumar sarari samaniyar Amurkan.

“Yankin da rokar Persverance da helikwaftan suke shawagi don gano abubuwa a wajen da Ramin Jezero yake yana da kwazazzabo, abin da ke jawo sadarwa ke daukewa,” a cewar Josh Anderson, shugaban tawagar kula da dakin bincike na helikwaftan Ingenuity a NASA.

Bayan da aka ji duriyar Ingenuity, ya aiko da sabbin sakonni zuwa duniyar Earth da suka hada da bayanan da ya tattara ran 26 ga Afrilu a zagayensa na mita 363 da ya shafe dakika 139 yana yi.

Masana kimiyya suna shirin kaddamar da wani sabon aikin da Ingenuity zai yi nan da makonni kadan masu zuwa, bayan da suka tabbatar injinansu na aiki yadda ya kamata.

Tun 2021 Ingenuity ya sauka a Mars

A ranar 18 ga watan Fabrairun 2021 ne Rokar Perseverance da NASA ta a wajen kera kayayyakin sama jannati a cibiyarta da ke California, ta isa duniyar Mars, wata bakwai bayan kaddamar da ita ran 30 ga watan Yulin 2020.

Karamin helikwaftan mai nauyin kilogiram 1.8 ya zama shi ne na farko da ya fara shawagi a wata duniyar ran 19 ga watan Afrilun 2021.

Da yake karfin maganadison sararin duniyar Mars bai wuce kashi 1 cikin 100 na Earth ba, sai injiniyoyin NASA suka yi amfani da kayayyaki marasa nauyi da farfela hudu masu tsawon kamu hudu kowanne, wajen kera jirgin.

AA