NASA ta saki sabbin hotunan da madubin James Webb Space Telescope ya dauko / Photo: AFP

Madubin hangen nesa na James Webb ya cika shekara daya yana shawagi a sararin samaniya tare da aiko hotunan da yake dauka zuwa duniyar Earth, inda a ranar da ya cika shekara dayan ya aiko wasu kyawawan hotuna na ban mamaki da ke nuna haihuwar sabbin taurari.

NASA ta bayyana sabbin hotunan a ranar Laraba, wadanda ke nuna jariran taurari 50 a cikin wani cakuden gajimare mai nisan shekarun haske 390 daga duniyarmu. Shekarar haske daya daidai take da kusan tafiyar kilomita tiriliyan 9.7.

Yankin da aka haifi jariran taurarin karami ne amma kuma cike yake da iskar gas nau'uka daban-daban da sinadaran haidurojin da kuma kura, sannan da yiwuwar sake haifar wasu taurarin da dama a wajen.

Dukkan jariran taurarin ba su fi Rana girma ba. Masana kimiyya sun ce hotunan masu ban al'ajabi sun dauku radau inda suka nuna yadda rayuwar tauraruwa ke farawa a takaice.

"Wata 'yar alama ce da ke nuna yadda Unguwarmu Ta Rana wato Solar System take, biliyoyin shekaru da suka wuce a lokacin da ake halittarta," kamar yadda wani masanin kimiyya na NASA, Eric Smith ya shaida wa AP.

Hasken tauraruwar ya bar wajen tun shekara 390 da suka wuce

Smith ya yi nuni da cewa hasken taurarin da ake gani a hotunan sun bar yankin ne tun shekara 390 da suka wuce.

A shekarar 1633, an tuhumi dan sama jannati na kasar Italiya Galileo Galilei a birnin Rome kan cewa duniyar Earth na zagaye rana ne. A shekarar 1992 Fadar Vatican ta tabbatar da cewa ba a fahimci Galileo ba, yana da gaskiya.

Wannan cakuden gajimaren da ake kira da Rho Ophiuchi, shi ne yankin da ake haifar taurari mafi kusa da duniyar Earth kuma an gano shi ne a sararin samaniya a kusa da kan iyakar da rukunin taurarin Ophiuchus da Scorpius da the serpent-bearer da kuma scorpion suke.

A yayin da ba a ganin taurarin a kurkusa a kan hoton, NASA ta ce bayanan da aka samar sun fayyace komai. An ga inuwar wasu daga cikin taurarin, abin da ke nuna cewa akwai yiwuwar ana kan halittar wasu duniyoyin ne, a cewar NASA.

Hoton "na nuna yadda ake haifar taurari ne a wani irin yanayi mai ban al'jabi da daure kai," a cewar wani babban jami'i na NASA, Bill Nelson a wani sakon Twitter da ya wallafa.

Shekara daya da aika katafaren madubin hangen nesa da ke shawagi a sararin samaniya

Webb — katafare kuma gagarumin madubin hangen nesa da aka harba sararin samaniya yake tattara bayanai — ya shafe shekara daya yana aiko da kayatattun hotuna na kyawu da al'ajabin samaniyar.

A watan Yulin bara ne aka fara bayyana hoton farko da madubin, wanda aka kera shi a kan kudi dala biliyan 10 ya dauka, bayan harba shi sararin samaniya daga French Guiana.

A bara ne aka fara bayyana hotunan farko da madubin Webb ya dauka a sarrain samaniya. Hoto: NASA

Ana daukarsa a matsayin madubin da ya maye gurbin Hubble Space Telescope, da ya shafe shekara 33 yana zagaye duniya.

Madubin Webb da aka samar a wani kokari na hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA da ta Tarayyar Turai, yana lalube ne a sarrain samaniya daga wani waje mai nisa, kimanin kilomita miliyan 1.6 daga Earth.

Aikin da ke gaban Webb: 'Yan sama jannati na fatan gano taurari da birane wato galaxies na farko da suka fara bayyana a sararin samaniya, a yayin da suke ci gaba da kokarin gano wata alama ta ko akwai rayuwa a duniyoyin da suke wajen Unguwarmu ta Rana.

"Ba mu gano ko daya daga cikinsu ba har yanzu," in ji Smith. "Amma har yanzu shekara daya kawai muka yi da fara wannan aiki."

AP