Ziyarar ta Yellen wata dama ce ga Washington don tsara kokarinta da Beijing wajen taimakawa kasashe masu karamin karfi da ake bi bashi kauce fadawa rikicin kudi./ Hoto: AP

Sakatariyar Baitul Malin Amurka Janet Yellen za ta isa kasar China a ranar Alhamis, a wani yunkuri na daidaita dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Ana sa ran babbar jami'ar ta Amurka za ta gana da takwarorinta na China da wakilai daga manyan kamfanonin Amurka, a ziyarar da za ta fara a ranar 9 ga watan Yuli.

Ga wasu mahimman dalilan da suka haifar da tsamin dangantakar tattalin arziki tsakanin Amurka da China.

Rabuwa da rage hatsarin dakatar da harkokin tattalin arziki

Washington da Beijing sun yi ta kai ruwa rana kan batutuwan da suka shafi yanayin siyasar kasashensu, lamarin da ya sa wasu da ke tsara dokoki cewa, ya kamata Amurka ta kaurace wa duk wani batu na tattalin arziki da China.

Jami'ai da dama daga cikin gwamnatin Joe Biden sun jaddada batun mayar da hankali kan rage hatsarin kariya ga wasu bangarori da ake ganin suna da muhimmaci ga tsaron kasa.

Gwamnatin Biden na nazari kan wani shiri da zai takaita saka hannayen jari na Amurka da suka shafi fasahohi da ke da mutukar jan hankali tare da muhimman abubuwan da suka shafi tsaron kasa - lamarin da ya harzuka jami'ai a China.

"Batun ya samu karbuwa sosai kan yadda Amurka ke kokarin rage karfin da China ke da shi," a cewar Lindsay Gorman wata babbar jami’ar Asusun Marshall na kasar Jamus ga kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.

A fahimtarsu ''Rage hatsarin aukuwar wani abu'' daidai ne da ''cire wani abu ko ware wani abu daga wani wuri,'' in ji ta.

Na'urar 'Chip'

Batun samar da wayoyi ko karafan da ke iya sadar da wutar lantarki, kalubale ne babba a yayin da China ke neman kare masana'antunta na cikin gida daga takunkumin fitar da kayayyaki da Amurka ta kakaba mata.

A watan Maris ne, Beijing ta kaddamar da wani bincike kan kamfanin kera na'ura na Amurka Micron, wata biyar bayan da Washington ta kaddamar da wasu takunkumai don dakatar da hanyoyin China wajen samun na'ura mai kwakwalwa ta Chip, da kayyakin da ake hada na'urar da su da kuma fasahar manhajojin da ake amfani wajen kera su.

Washington ta kakaba wa wasu kamfanonin China da dama takukumi a wani mataki na hana su shiga cikin masu samar da na'urorin zamani masu inganci, yayin da ta tura abokan huldarta su yi koyi da su.

Beijing ta fada a ranar Litinin cewa za ta dakatar da fitar da kayayyaki na wasu karafa biyu da ba su da wani muhimmanci ga masana'antar kera na'ura mai kwakwalwa zuwa kasashen waje '' karafan gallium da germanium'' tana mai dora dalilanta na yin hakan kan matsalolin tsaro.

Bashi

Bashi na daga cikin ajandar da Yellen za ta mayar da hankali a kai, - akwai batun bashin da Amurka ke bin China da kuma ba da rance da Beijing ke yi ga kasashe masu tasowa wadanda a yanzu suke kokarin biya.

"Babbar tambayar a nan ita ce, shin China na dab da cimma yarjejeniya da kasar Sri Lanka ko Ghana kan batun sake fasalin basussuka a hukumance?", in ji Brad Setser, tsohon jami'in Baitulmalin Amurka wanda a yanzu shi ne babban jami'i a majalisar kula da harkokin waje na kasar, kamar yadda ya bayyana wa AFP.

Ziyarar ta Yellen na zama wata dama ga Washington don tsara kokarin da take yi da Beijing wajen taimaka wa kasashe masu karamin karfi da ake bi bashi kauce fada wa rikicin kudi.

Manyan kamfanonin fasahohi

Manyan kamfanonin fasahar kere-kere na China na fuskantar bincike daga kasashen duniya a 'yan shekarun nan, inda suke dora damuwarsu kan matsalar tsaron kasa saboda alakarsu da gwamnatin China.

Amurka ta yi gargadi kan cewa yin amfani da na'urorin da Huawei -- babban kamfanin sadarwa na kasar China -- na nufin ba da damar yin amfani da ababen more rayuwa da za a iya amfani da su wajen leken asirin kasa, ikirarin da Beijing ta musanta.

Har ilau batun shahararren dandalin sada zumunta na TikTok, mallakin ByteDance na Beijing, shi ma ya tayar da kura a Washington, inda masu tsara dokoki a Amurka suka bayyana damuwa game da tsaron bayanan masu amfani da kafar da kuma yiwuwar amfani da manhajar a matsayin kafar yada “farfaganda" ga jam'iyyar kwaminisanci ta China.

Kasuwanci

Kazalika a yayin ziyarar, akwai yiwuwar tattauna batun harajin da aka aiwatar lokacin yakin kasuwanci da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar.

Gorman ta shaida wa AFP cewa ba ta tunanin Amurka za ta yi saurin kawar da batun haraji a yanzu, kuma ko da za ta yi "tabbas ba daga bangare daya ba".

"Ba na tunani kan cewa akwai abu da muka ji daga wurin jama'a da ya nuna ko ya bukaci a saka wannan batun a kan gaba cikin ajandar," in ji ta.

Yanayin kasuwanci

Yanayin kasuwancin kamfanonin Amurka da ke China ya kara fuskantar kalubale, biyo bayan jerin samame da bincike kan kamfanonin kasashen waje, da mahukuntan kasar suka aiwatar.

Sauye-sauye na baya-bayan nan kan dokar dakile leken asiri ta kasar China sun fadada ma'anar leken asiri yayin da aka hana mika bayanan da suka shafi tsaron kasa, hakan ya haifar da damuwa da yawa ga harkokin kasuwancin kamfanonin kasashen waje, in ji Edward Alden, wani babban jami'i a majalisar kula da harkokin kasashen waje.

"Idan aka sake komawa kan teburin tattaunawa, masu zuba jari daga kasashen waje za su dan samu karin kwarin gwiwa cewa zuba jari a China wani shiri ne na dogon zango," in ji shi.

Alden ya kara da cewa, idan kuma alamu suka nuna cewar ba za a samu nasara a tattaunawa tsakanin Amurka da China ba, ''muhimmin abinda ya kamata masu zuba jari na kasashen waje su yi shi ne neman hanyoyin ficewa daga inda suke''.

AFP