Bayanai daga hukumomin kidayar jama’a a China sun kiyasta cewa akwai tsirarun al’ummar kabilar Hui, wadanda mafi yawansu Musulmai ne. Hoto: Michael Martina/Reuters

Hukumomi a garin Nagu, a lardin Yunnan da ke kasar China, sun zartar da shirinsu na rusa hasumiya hudu da kuma rufin Masallacin Najiaying, wanda hakan ya kona wa Musulman al’ummar Hui.

Kasar China ta aika daruruwan ‘yan sanda kuma ta yi kame a yankin wani gari da ke kudu maso yammacin kasar, inda Musulmai ke da rinjaye.

Hakan ya biyo bayan takaddama kan shirin ruguje wani masallaci, kamar yadda wani ganau ya fada.

A ranar Asabar, tarin ‘yan sanda dauke da kulake da silken kariyar zanga-zanga, sun shawo kan gungun mutane a wajen masallacin bayan sun yi ta jifansu da duwatsu, kamar yadda aka gani a wasu bidiyoyi da suke yawo, da kuma yadda wasu ganau suka fada.

Wata ‘yar yankin wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Suna so su yi rushe-rushe, shi ya sa mutane suka fito don hana su,”.

Ta ce, “Masallacin waje ne na Musulmai kamar mu. Idan suka yi yunkurin rusa shi, to kuwa ba za mu bar su ba. Gini ai gine ne kawai, ba ya cutar da kowa. Me ya sa za su ce sai sun rushe shi?"

Wani mazaunin garin wanda ya nemi kar a bayyana sunansa, ya fada ranar Litinin cewa, “Hukumomin garin na Nagu da ke lardin Yunnan, sun aiwatar da shirin nasu na rushe hasumiyoyi hudu da kubbar rufin Masallacin Najiaying”.

Yankin cibiya ce ta da dama daga al’ummar Hui, wadda mafi rinjayensu Musulmai ne ‘yan kabila, wadanda suka fuskanci gagarumar tsangwama.

‘Yan sanda sun kama adadin mutane da ba a bayyana ba bayan faruwar rikicin, kuma an girke daruruwan jami’ai a garin zuwa ranar Litinin, a cewar wasu ganau biyu.

Mutanen da ke makwabtaka da masallacin sun bayyana cewa suna fuskantar matsala katsewar intanet, da wasu matsalolcin sadarwa tun bayan rikicin.

Wata sanarwa da gwamnatin Tonghai ta fitar ranar Lahadi, wadda ita ce ke iko da garin Nagu, ta ce ta fara bincike kan “wata matsala da ta yi barazana matuka ga doka da oda".

Sanarwar ta umarci wadanda suka shiga rikicin da su “gaggauta dakatar da ayyyukan da suka saba wa doka", kuma sun sha alwashin "hukunci mai tsanani" kan duk wanda ya ki bin umarnin kawo kansa gaban hukuma.

Duk wadanda suka kawo kansu ba tare da bijirewa ba, za su samu rangwame, a cewar sanarwar.

Tsananta samame

China tana ta kokarin tsangwama da juya addini a kasar tun lokacin da Shugaba Xi Jinping ya karbi mulki, shekara 10 da suka wuce.

Game da gallazawar da take wa Musulmai, gwamnatin China tana ikirarin cewa tana hakan ne don yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayin.

Bayanai daga hukumomin kidayar jama’a a China sun kiyasta cewa akwai tsirarun al’ummar kabilar Hui, wadanda mafi yawansu Musulmai ne.

Su ne hudu daga kabilu mafi girma a China, daf da kabilar Han Chinese da ke da al’umma biliyan 1.3. Kabilar Zhuang tana da al’umma miliyan 20, sai kuma Uighurs masu al’umma miliyan 12.

An kiyasta al’ummar Uighur miliyan daya, da al’ummar Hui da kuma sauran tsirarun Musulmai aka tsare a yammacin jihar Xinjiang Uighur mai kwarya-kwaryar yanci, tun daga shekarar 2017.

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun ce hakan na faruwa ne karkashin shirin gwamnati na samame.

TRT World