Musulmai al'ummar China ke sallah a wani masallaci. Hoto: Reuters

Al'ummar Musulmai masu rinjaye a garin Hui da ke yankin kudu maso yammacin China sun yi wata arangama da 'yan sanda, lokacin da aka yi yunkurin rusa wani masallaci, a wani mataki na nuna iko a kan addini da jam'iyyar Kwaminisanci ke yi.

A tsawon shekarun da suka gabata, Beijing ta yi ta kokarin aiwatar da tsarin "sauya fuskar addinai" - wato wani yunkuri na sauyawa 'yan China addinansu, musamman na Musulunci.

Ana ganin matakin zai rage tasirin da addinai ke da shi a kan mutane domin samun damar karfafa al'adar kasar da tsarin Jam'iyyar Kwaminisanci a kansu.

A tsakanin gwaje-gwajen da aka yi ta gudanarwa, akwai kabilu da dama daga lardin Najiaying da keYunnan, wani yanki da ya hada iyakar China da kudu maso gabashin Asia, mai dauke da mabiya addinai mabanbanta.

A ranar Asabar ne, gomman jami'an 'yan sanda rike da faranti da hular kare kansu, suka bi kan dandazon mutanen da suka taru a gaban Masallacin Najiaying, kamar yadda hotuna da bidiyoyi da suka karade shafukan sada zumunta suka nuna, da kuma bayanai daga shaidun gani da ido.

Mutane da dama ne jami'an 'yan sandan suka kama biyo bayan lamarin da ya faru, kazalika an jibge daruruwan jami'an tsaro a cikin garin tun daga ranar Litinin, a cewar wasu shaidu biyu.

"Masallaci tamkar gida ne ga Musulmai, idan suka yi yunkurin rusa shi, tabas ba za mu bari su yi hakan ba," a cewar wata mazauniyar garin a hirarta da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Hari ga 'yan kabilar Hui

Musalmai 'yan kabilar Hui sun yi fice a tarihi wajen tsallake rijiya da baya ta fuskar shan wahalhalu da tsayin daka a kasar China da ke da fadi da mabanbantan kabilu.

Tahirin al'ummar Hui ya biyo bayan karnoni da dama da suka gabata, an yi imanin cewa kakanninsu Larabawa ne, da Farisawa da 'yan kasuwar tsakiyar Asia, da kuma manyan malamai da suka yi bulaguro ta kan tsohuwar hanyar silk zuwa China, suka kuma samu mafaka a yankuna da dama a kasar inda suka yi auratayya da 'yan kasar ta China.

A tsawon shekarun, 'yan kabilar Hui sun hade addininsu na Musulunci cikin da al'adu da tsarin kasar China ta hanyar rungumar harsunan kasar don sadarwa da amfani da sunayensu na gargajiya, sun nuna jarumtakarsu wajen cudanya cikin al'ummar China mai yawan gaske.

Masallatai, wurarensu masu tsarki, ba wai sun kasance wajen yin ibada ba ne kawai har ma a matsayin muhimman wuraren zama na jama'a inda 'yan kabilar Hui suka ba da hadin kai tare da kiyaye tarihin addininsu.

Sai dai, gangamin nuna iko da ake yi musu ya haifar da babbar barazana ga al’adu da dabi’o’insu masu matukar daraja, lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin ‘yan kabilar Hui masu fafutuka da al’ummominsu da ke fargabar rushewar asalinsu da kuma tauye musu ‘yancin yin addininsu.

Lokutan Baya

Yunkurin rusa masallacin Najiaying ba shi ne karon farko da ‘yan kabilar Hui suka yi taho-mu-gama da hukumomi domin kare masallatansu ba.

Masu fafutuka ‘yan kabilar Hui sun bayyana cewa, a 'yan shekarun da suka gabata, hukumomi sun yi ta rusa musu gine-ginen addininsu na Musulunci, tare da lalata gidaje sannan sun rusa masallatai fiye da dubu a fadin kasar.

A 2018, wani muhimmin al’amari ya faru a Ningxia, da ke yankin arewa maso yammacin China.

Dubban al’ummar Hui sun gudanar da zanga-zangar zaman dirshan ta kwana uku, da nufin hana shirin sake rushe wani masallaci da manyan masu zanen gine-gine daga yankin Gabas ta Tsakiya suka tsara.

Abubuwan da suka faru a Ningxia sun faru ne bayan aiwatar da kamfe din kin jinin "Larabawa" da "Saudiyya" da gwamnatin China ta fara, bayan da fara aiwatar da sabuwar doka kan harkokin addini a watan Fabrairun 2018.

Wannan gangami dai ba wai Ningxia kadai ya shafa ba, har ma da sauran yankunan da ke kasar musamman al'ummar Musulmai mafi yawa.

Hukumomin yankin Ningxia sun fito karara sun bayyana aniyarsu ta gyara wuraren addini da ke nuna tasirin Larabawa a ciki.

Sun jaddada bukatar samar da sabbin gine-gine da aka yi ko yin gyara a duk fadin yankin don nuna salon gargajiya na China, tare da yin watsi da fasahohin gine-gine, musamman hasumiyar da ke nuna matsayin addinin Musulman Hui.

Da fari dai karamar hukumar ta yi jinkirin aiwatar da shirin rushewar, sakamakon turjiya da al'ummar Hui suka yi.

Ko da yake dai, an cimma matsaya - kuma Musulmai sun amince su maye ma'adinai da aka yi amfani da su wajen gina hasumiyar masallacin da na gargajiya irin na kasar Sin - shawarar da ta nuna dagewar da gwamnati ta yi na bin ka'idojin al'adun kasar Sin.

Tun 2017, yankin Xinjiang Uighur mai cin gashin kansa ya kasance cibiyar kamfe din gwamnati da ya yi sanadin tsare mutum kusan miliyan daya daga ‘yan tsirarun Musulman wajen, ciki har da 'yan kabilar Uighur da 'yan kabilar Hui.

Wannan lamari dai ya janyo cece-kuce a duniya, inda kungiyoyin kare hakkin bil adama daban-daban suka yi masa lakabi da kisan kare dangi.

Yayin da kasar China ke kan bakanta na tsayawa kan al'adunta, makomar Masallacin Najiaying ya haifar da tambayoyi masu yawa game da samun daidaito tsakanin 'yancin addini da ikon gwamnati.

Halin da ake samu ba wai kawai yana gwada juriyar da hakurin al'ummar kabilar Hui ba ne, ya haifar da tunani kan makomar addinai a kan iyakokin kasar ta China.

TRT World