Ma'aikatar cikin gida ta Faransa ta ce an kama mutane 719 cikin dare, kusan rabin adadin da aka kama a daren da ya gabata. / Hoto: AFP

Masu zanga-zanga a Faransa sun kai hari gidan magajin wajen birnin Paris da wata mota da ke ci da wuta a yayin da ake ci gaba da bore a kasar sakamakon kisan da 'yan sanda suka yi wa wani matashi mai suna Nahel M.

Masu boren sun kutsa kai cikin gidan Vincent Jeanbrun, magajin garin L'Hay-les-Roses da ke wajen birnin Paris, da wata mota mai ci da wuta da zummar kona gidan a ranar Lahadi, a cewar masu gabatar da kara.

Gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron ta kwashe kwanaki tana neman shawo kan munanan zanga-zanga bayan wani dan sanda ya harbe Nahel M., mai shekaru 17, a unguwar Nanterre da ke birnin Paris a ranar Talatar da ta gabata a yayin da suke aikin duba ababen hawa.

Kisan Nahel M, dan asalin kasar Aljeriya, ya sake farfado da zargin da aka dade ana yi wa 'yan sandan Faransa na nuna wariyar launin fata, lamarin da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka ce ana yi wa tsirarun mutane ne.

Matar Jeanbrun da ’ya’yansa, masu shekaru tsakanin biyar da bakwai, suna gida, yayin da shi kansa magajin garin ya tafi babban dandalin garin domin shawo kan tarzomar.

An yi wa matarsa "mummunar rauni" inda ta samu karaya a kafa, in ji masu gabatar da kara.

An soma gudanar da bincike kan yunkurin kisan kai.

"Abin da ya faru jiya da daddare ya kai wani mummunan mataki kuma abin tsoro ne da kunya," a cewar sanarwa da magajin garin ya fitar.

"Lamarin ya dan lafa," in ji Firaiminista Elisabeth Borne a hirarta da manema labarai yayin da ta ziyarci L'Hay-les-Roses.

"Irin aika-aikar da muka gani musamman a safiyar yau na da matukar ban tsoro. Ba za mu bari wani tashin hankali ya faru ba" ba tare da an hukunta wadanda suka aikata shi ba.

A kokarin dakile abin da ya zama daya daga cikin manyan kalubale ga Shugaba Macron tun bayan hawansa mulki a shekarar 2017, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce za ta tura 'yan sanda 45,000 a fadin kasar cikin daren Litinin zuwa Talata don kwantar da tarzoma.

Ma'aikatar ta ce an kama mutane 719 cikin dare, kusan rabin adadin da aka kama a daren da ya gabata. Duk da wannan mataki, an ba da rahoton barkewar kazamin fada a wurare da dama, ciki har da birnin Marseille da ke kudancin kasar.

An jibge kimanin 'yan sanda 7,000 a birnin Paris da kewayensa, ciki har da titin Champs Elysees, wurin yawon bude ido, bayan kiraye-kirayen da aka yi a kafafen sada zumunta don yin zanga-zanga a tsakiyar birnin.

Kira don kawo karshen tashe-tashen hankula

Kakar matashin da aka kashe ta yi kira da a kwantar da hankula.

"Ku dakata kar da ku yi fada" in ji Nadia, kamar yadda ta shaida wa gidan talabijin na BFM a wata hira da aka yi da ita ta wayar tarho.

Ta ce masu zanga-zangar suna yin amfani da mutuwarsa jikanta ne kawai a matsayin "hujja" wajen bayyana fushinsu ga gwamnati.

"Ina gaya wa mutanen da ke ta da rikici cewa: Kada a fasa tagogi, ko ku kai hari makarantu ko motocin bas-bas, ku dakata!," in ji ta.

An tuhumi dan sandan da ya yi kisan, mai shekaru 38, da laifin kisan kai kuma tuni aka tsare shi a gidan yari.

Babban kalubale

Zanga-zangar ta haifar da sabon kalubale ga Macron wanda ya yi niyyar ci gaba da aiwatar da alkawuran da ya dauka lokacin da ya soma wa'adinsa na biyu, ciki har kara shekarun ritaya a kasar. An dade ana zanga-zanga kan hakan.

Rikicin ya haifar da damuwa daga kasashen waje, ganin cewa Faransa ce za ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya ta Rugby a lokacin kaka da kuma gasar Olympics ta Paris a lokacin rani na 2024.

Masu shirya gasar tseren keke ta Tour de France sun ce suna mai da hankali sosai kan lamarin a daidai lokacin da suke shirin tsallakawa kan iyakar Faransa a ranar Litinin bayan kwanaki biyu da suka yi a yankin Basque ta kasar Sifaniya.

Macron ya bukaci iyaye su ja wa 'ya'yansu da ke zanga-zanga kunne.

Kusan kashi daya bisa uku na masu wannan aika-aikar “matasa ne ko wadanda ke da kananan shekaru” kamar yadda ministan cikin gida Gerald Darmanin ya ce.

TRT World