An shafe kwanaki ana zanga-zanga a Faransa bayan kisan matashi dan Aljeriya a Faransa. Hoto/AP

Shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev ya zargi Faransa da zama daya daga cikin kasashen da suka ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren mulkin mallaka.

Ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa wadda kasashen ‘yan baruwanmu suka yi a Baku babban birnin kasar.

Aliyev ya bukaci shugaban na Faransa Emmanuel Macron da ya bai wa kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka hakuri.

“Ya bayar da hakuri ga miliyoyin mutane da wadanda suka gabace shi suka yi wa mulkin mallaka, suka yi amfani da su a matsayin bayi suka kashe sa’annan suka azabtar da cin mutuncin su.

“Wannan ba wai kawai zai bayyana abin da ta yi a tarihi ba ne amma zai taimaka mata shawo kan matsalolin da ta fuskanta a siyasance da matsalolin da take ciki na rikici bayan kisan gillar da aka yi wa wani matashi dan kasar Aljeriya,” in ji shi.

Kisan da dan sandan Faransa ya yi wa matashi

Aliyev ya bayyana cewa wariyar launin fata da kuma nuna bambanci ta zama ruwan dare a Faransa har a kafafen sada zumunta.

Nahel M. mai shekara 17 wanda asalin dan kasar Aljeriya ne, wani dan sanda ne ya harbe shi a kusa da kusa a makon da ya gabata a Nanterre da ke gefen birnin Paris.

Ana ta zanga-zanga a kasar Faransa tun bayan kisan da dan sandan ya yi wa matashin.

A halin yanzu dai ana bincike kan dan sandan da ya yi harbin kan zargin kisan kai dagangan kuma tuni aka tsare shi na wucin gadi.

AA