Wata doka da ka yi a wata Mari na 2004 ta haramta wa "dalibai sanya duk wata alama ko tufafi da ke nuna addinin da suke bi a makarantu." / Hoto: AFP

Za a haramta wa mata sanya abaya a makarantun Faransa domin hakan ya saba wa dokokin kasar na kasancewa mara addini, a cewar Ministan Ilimin kasar.

"Ba zai yiwu a ci gaba da sanya abaya a makarantu ba," kamar yadda Ministan Ilimi Gabriel Attal ya shaida wa gidan talbijin na TF1, yana mai cewa zai bayar da "dokoki a fayyace a matakin tarayya" ga shugabannin makarantu gabanin sake bude makarantu ranar 4 ga watan Satumba.

An dauki matakin ne bayan an kwashe watanni ana muhawara game da sanya abaya a makarantun Faransa, inda aka dade da haramta wa mata daura dan-kwali.

Kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ne suka shige gaba wajen ganin an haramta sanya abaya, ko da yake masu sassaucin ra'ayi sun ce matakin ya take hakkin mutane na zamantakewa.

An yi ta samun rahotanni yawaitar mata da ke sanya abaya a makarantu kuma hakan na janyo ka-ce-na-ce tsakanin malamai da iyayens dalibai.

"Matakin ba-ruwanmu-da-addini abu ne da ke nufin samun 'yanci ta hanyar makaranta," a cewar Attal, yana mai bayyana abaya a matsayin "wata hanyar addini da ke son gwada hakurin jamhuriya game da tsarin ba-ruwanmu-da-addini."

"Bai kamata idan ka shiga aji ka gane addinin da dalibai ke bi ba," in ji shi.

Wata doka da ka yi a wata Mari na 2004 ta haramta wa "dalibai sanya duk wata alama ko tufafi da ke nuna addinin da suke bi a makarantu."

Sai dai ba kamar dan-kwali ba, ba a hana sanya abaya ba sai yanzu.

AA