Duniya
Putin ya bai wa Aliyev haƙuri kan hatsarin jirgin saman Azerbaijan
Fadar Kremlin ta ce na'urorin tsaron sararin samaniya sun yi luguden wuta a kusa da Grozny a ranar Laraba saboda wani harin da jirgin saman Ukraine maras matuƙi ya kai, amma shugaban bai bayyana ko na'urorin tsaron ne suka harbo jirgin ba.Türkiye
Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da takwaransa na Azerbaijan Aliyev a Ankara
A yayin da yake magana dangane da halin da ake ciki a Falasɗinu, Erdogan ya yi Allah-wadai da matakin da Isra'ila ta ɗauka, yana mai yi musu laƙabi da masu "ayyukan kisan kiyashi da ke barazana ga zaman lafiyar yanki da ma tsaron duniya."Duniya
Bayani kan jirgin helikwafta ƙirar Amurka da ya yi hatsari da shugaban Iran Raisi
An yi amannar cewar helikwafta samfurin Bell 212 da ya yi hatsari a arewacin Iran lamarin da ya yi sanadin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da tawagarsa, ya kai aƙalla shekara 45 da ƙerawa kuma bayanai sun ce rundunar sojin Iran tana da irinsa guda 10.Duniya
Armenia da Turkiyya sun jinjina wa juna kan sake ƙulla dangantaka
Gwamnatin Turkiyya na fatan sake ƙulla cikakkiyar dangantaka da Armenia bayan da Armenia ta sanar da shirin buɗe iyakokin juna; yayin da hukumomin Armenian da Azerbaijani suka bayyana shirinsu na zaman lafiya a taron Antalya Diplomacy Forum.Türkiye
Turkiyya ta goyi bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin Azerbaijan da Armeniya
Ankara ta bayyana damuwarta game da yunkurin Armeniya na 'amfani da damar da ta samu daga kasashen waje' tare da wuce gona da iri a bin hanyar Lachin don samar da makamai ga kungiyoyin ta'addanci, a cewar jakadan Turkiyya na MDD Sedat Onal.
Shahararru
Mashahuran makaloli