Taron Diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum yana gudana a birnin Antalya na Turkiyya. / Hoto: AA

Jakadan Turkiyya a Armenia ya tattauna kan muhimmancin cim ma cikakkiyar dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu, inda ya yi kira kan neman amincewa juna da kuma haɗin-kai.

"Babban burinmu shi ne cim ma cikakkiyar alaka (da Armenia)," a cewar jakada Serdar Kilic, wanda shi ne Wakili na Musamman na Turkiyya kan Sake Ƙulla Alaƙa da Armenia, da yake magana wajen taron Antalya Diplomacy Forum na 2024 ranar Juma'a.

Yayin da yake magana a zauren "Zaman lafiya, Cigaba, da Haɗin-kai a Yankin Kudancin Caucasus, ya ƙara da cewa, "Tabbas akwai wasu ka'idoji da ake bukata don sake kulla dangantaka, kuma dole mu yi biyayya ga wadannan ka'idoji".

Kilic ya jaddada bukatar matakan neman karfafa aminci da juna wajen tattaunawa da Wakili na Musamman na Armenia, Ruben Rubinyan, kuma ya nanata alfanun mayar da hankali kan haɗin-kai maimakon rarrabuwar kai.

Rubinyan, Mataimakin Kakakin Majalisar Armenia, ya amsa cewa akwai kalubale a dangantakar Armenia da Turkiyya, kuma ya jaddada yin takatsantsan a tattaunawar sake kulla dangantaka, inda za a iya samun sakamako mai kyau da mara kyau.

Ya tabbatar da cewa babu wasu sharudda kan sulhu da Turkiyya, kuma ya sanar da shirye-shiryen bude iyakar Turkiyya da Armenia, ga 'yan sauran ƙasashe, zuwa watan Yulin 2024, don neman fadada haɗin-kai.

Ya ce, "Dole mu iya bude iyakokinmu ba wai lokacin lumana kawai ba, amma har lokutan yaduwar arziki. Yanzu a wannan lokaci, ban ga wani dalilin da iyakar Turkiyya da Armenia za ta zama a rufe ba."

Kilic ya kuma bayyana fatan bude iyakar Turkiyya da Armenia, inda ya shawarci cewa gabatar da wannan a matsayin sharadi zai iya haifar da matsaloli, don haka ya nemi haɗuwa da Rubinyan a birnin Yerevan a sati mai kamawa.

Lumana tsakanin gwamnatin Azerbaijan da Armenia

Yayin da yake nuni kan dadadden rikici tsakanin Azerbaijan da Armenia, Wakilin Turkiyya, Kilic ya yi kira ga ƙasashen su dauki darasi daga gazawar baya, kuma ya nuna muhimmancin duba walwalar al'ummar yankin don kawo kyawawan sakamako daga tsarin zaman lafiya.

Ya yi gargadi kan neman kakaba mafita ta bangare guda ba tare da la'akari da dayan bangaren ba, kuma ya jaddada wajabcin tattaunawa da juna da haɗin gwiwa.

Rubinyan ya yi nuni kan tattaunawar da ke cigaba tare da Azerbaijan, musamman dangane da ƙayyade iyakoki bisa Shelar Almaty ta 1991.

Ya bayyana shirin Armenia na zaman lafiya, kuma ya fayyace cewa ba sa yin ikirari kan wani yanki na Azerbaijan, sannan ya ƙara da cewa yunkurin gwamnatin Armenia na inganta karfinta na tsaro ba ya nufin neman faɗa.

Hikmet Haciyev, Mashawarcin Shugaban Azerbaijan, ya ce yakin da aka yi a Karabakh ya kare a wajen ƙasarsa, sannan zaman lafiya da haɗin-kan yankin shi ne suka sa a gaba.

Da yake nuni kan ayar doka da ke kundin tsarin mulkin Armenia dangane da haɗe Karabakh da Armenia, Haciyev ya ce suna fatan samun bayanin da ya dace kan wannan batu.

Yayin da yake ƙarfafa cewa gwamnatin Azerbaijan ba ta da niyyar katsalandan a harkokin cikin gida na Armenia, Haciyev ya bayyana cewa wasu ayoyin doka a tsarin mulkin Armenia za su iya shafar matsayar iyakokin Azerbaijan.

Ya yi nuni kan yunƙurin gwamnatin Azerbaijan na gabatar da manufofi biyar ga Armenia don kawo zaman lafiya, wanda yake nuni kan cewa ƙasarsa ta shirya cimma zaman lafiya.

Sa'annan ya ƙara da cewa suna son sauƙaƙa mahaƙa da Nakhchivan, da kuma cewa Armenia za ta ci moriyar wannan haɗewar.

Tasirin Turkiyya a Kudancin Caucasus

A zauren tattaunawar, Toivo Klaar, wakilin Tarayyar Turai a Kudancin Caucasus, ya ja hankali kan buƙatar kafa yarjejeniya mai ɗorewa kan zaman lafiya.

Ya ce "Idan muna magana kan batu tsakanin Armenia da Azerbaijan, akwai yiwuwar a farfaɗo da Caucasus," kuma ya jaddada wajibcin cimma yarjejeniya wadda kowa zai yi nasara ta hanyar haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu.

Ya ƙara da cewa, "Ba za mu raina muhimmancin Turkiyya a nan ba. (Turkiyya) maƙwabciyar Georgia da Armenia ce, kuma tana da dangantaka ta musamman da Azerbaijan. Turkiyya tana da babbar dama a yanzu saboda za ta iya haɓaka wannan aikin na samar da zaman lafiya”.

Klaar ya ƙara da cewa aikin zaman lafiya tsakanin Azerbaijan da Armenia zai taimaka wajen fitar da makomar haɗin-kai a Kudancin Caucasus, inda ya ce "Za mu cim ma samun al'ummar mara ɗauke da makamai, ta haka za mu nuna kishin zaman lumana."

TRT World