Turkiyya "ba ta taba samun kwarin gwiwa kamar yanzu ba" game da sayen jirgin yaki na F-16 daga Amurka, in ji shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan.
"Muna sa rai za a samu kyakkyawan sakamako. Ina cike da fatan da ban taba yin irinsa ba (game da wannan batu," kamar yadda Erdogan ya shaida wa manema labarai ranar Laraba a karshen taron NATO A Vilnius, babban birnin Lithuania.
Da yake magana a kan yaki da ta'addanci, ya ce Turkiyya ba za ta gajiya ba wajen fatattakar 'yan ta'adda.
Ya kara da cewa: "Muna sa rai kawayenmu za su dauki mataki mai tsauri a kan wannan batu."
Da yake tsokaci game da kona Alkur'ani a Sweden, shugaban Turkiyya ya ce hakan rashin mutunci ne ba 'yancin fadar albarkacin baki ba ne, yana mai bayyana matakin a matsayin "dabbanci, jahilci da kuma babban ta'addanci."
Ya kara da cewa ya kamata kasashen da suka jefa kuri'ar kin yin tir da wannan mataki a hukumar kula da 'yancin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya "su sake nazari" game da abin da suka fahimta da 'yancin fadin albarkacin baki da na dan adam.
Ranar Talata, Burtaniya, Amurka da wasu kasashen Turai sun ki yin Aallah wadai da kona Alkur'ani yayin wata muhawara ta gaggawa a zauren hukumar kula da 'yancin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva bayan wani mutum ya kona littafin mai tsarki a Sweden, lamarin da ya jawo kassausan suka daga duniya.