Jirgin samfurin Bell 212, wanda direba ɗaya ko biyu za su iya tuƙawa, yana da tsayin mita 17.41, sannan yana da tsawon mita 3.83 daga ƙasa zuwa sama.

Amurka ce ta ƙera jirgin helikwafta samfurin Bell 212 wanda ya yi hatsari a birnin Tabriz na arewacin Iran ranar Lahadi lamarin da ya yi sanadin mutuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa waɗanda suka taso daga Azerbaijan.

Babu fasinjan da aka gani da ransa lokacin da aka gano tarkacen jirgin, wanda Iran ta saya daga Amurka shekaru da dama da suka wuce kafin juyin-juya-halin ƙasar na 1979.

An soma ƙera jirgin samfurin Bell 212 a garin Fort Worth na jihar Texas, kafin a sauyawa kamfanin matsuguni zuwa birnin Mirabel da ke yankin Quebec na ƙasar Canada a 1988, sannan ya daina aiki a 1998.

Ko da yake sojoji sun soma aiki da jirgin ne a 1968, an fi amfani da shi a matsayin jirgin fasinja.

Jirgin samfurin Bell 212 yana iya ɗaukar fasinja 15, ciki har da ma'aikatan cikin jirgin.

Ana iya amfani da shi wurin yaƙi da ɗaukar kaya da sauransu.

Bayanai sun ce an inganta helikwaftan da Raisi ya hau don ya iya ɗaukar fasinja 15.

Na'urorin jirgin

Jirgin samfurin Bell 212, wanda direba ɗaya ko biyu za su iya tuƙawa, yana da tsayin mita 17.41, sannan yana da tsawon mita 3.83 daga ƙasa zuwa sama.

Yana da nauyin kilogiram 2,962 idan ba ya ɗauke da kaya, kuma yana iya ɗaukar kaya masu nauyin da ya kai kilogiram 5,080, kana injinsa yana da nauyin kilowat 1,300 da farfela guda biyu, kowace tana da tsawon mita 14.63.

Jirgin yana iya gudun kilomita 190 duk awa ɗaya amma zai iya kai wa kilomita 220 idan zai yi yaƙi.

Kazalika yana iya tafiya mai nisan kilomita 439 sannan ya kai ƙololuwar nisan da ya kai ƙafa 17,388.

Rashin kayan gyaran jirgi

Iran ta fuskanci ƙalubale da dama wajen gyarawa ko inganta jirage da makamai da sauran ababen hawa da ta saya daga Amurka saboda takunkuman da ta ƙaƙaba mata, lamarin da ya sa ba ta iya samun kayan gyaransu.

An yi amannar cewa jirgin samfurin Bell 212 ya kai aƙalla shekara 45 a hannun Iran kuma rundunar sojin ƙasar tana da irinsu kusan 10.

Tsohon ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya zargi Amurka da hannu wurin mutuwar manyan jami'an gwamnatin ƙasar yana mai cewa mahukunta a Washington "sun sanya takunkuman hana sayar da kayan gyaran jiragen kuma sun hana al'ummar Iran jin daɗin hanyoyin sufurin jiragen sama."

Amma Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce Washington "ba shi da hannu a hatsarin jirgin saman" yayin da Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙasar ta ce "gwamnatin Iran ce take da alhakin abin da ya faru tun da ita ce ta yi amfani da jirgin da ya kai shekara 45 a yanayi maras kyawu."

A gefe guda, gwamnatin Iran ta naɗa kwamitin da zai gudanar da bincike kan "abin da ya haddasa hatsarin."

TRT World