Mene ne musabbabin arangama tsakanin Afghanistan da Iran a kan iyaka?

Mene ne musabbabin arangama tsakanin Afghanistan da Iran a kan iyaka?

Dukkan bangarorin biyu na zargin juna da karya yarjejeniyar 1973 da ta sanya ka’idoji kan kwararowar ruwa a Tafkin Helmand, wanda ya bi ta Afghanistan ya gangara Iran.

An samu zaman lafiya a iyakar Afghanitan da Iran bayan da jami’an tsaronsu suka yi barin wuta a ranar 27 ga Mayu saboda takaddama kan ruwa da aka dade ana yi.

Sojoji uku, biyu daga Iran da daya daga Afghanistan sun rasa rayukansu a arangamar da aka yi a karshen makon da ya wuce, wadda ta faru sakamakon takaddama kan yadda za a raba ruwan Tafkin Helmand da ya bi ta Afghanistan tare da gangarawa Iran.

Yankin gabashin Iran na fuskantar fari, Tehran na dora alhakin hakan kan gwamnatin Kabul da ke tare ruwan.

Wannan ne babban kalubalen da bangarorin biyu ke fuskanta tun bayan da Taliban ta kwace iko da Afghanistan a 2021.

Abin da ya janyo rikici na baya-bayan nan

A farkon watan Mayu, Shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya fara kalaman nuna bacin rai tare da gargadar jami’an gwamnatin Afghanistan da ke karya ka’idar amfani da ruwan Iran a tsawon kilomita 1100 da ke Tafkin Helmand da ya ratsa kasashen biyu.

“Ba za mu sarayar da hakkokin jama’armu ba”, in ji Raisi.

A wani martani na gaggawa, kakakin Masarautar Musulunci ta Afghanistan, Zabihulllah Mujahid ya bayyana cewa amfani da kakkausar murya ba zai taimaka wajen warware rikicin ruwan ba.

Madatsar Ruwa ta Kajaki

Ya ce Kabul na aiki da yarjejeniyar raba daidai kan ruwa da aka kulla a shekarar 1973, kuma karancin ruwan ya afku ne sakamakon yadda babu isasshen ruwa a Tafkin.

Iran na son aika kwararru zuwa ga wata madatsar ruwa da aka gina a kan Tafkin a Afghanistan don tabbatar da cewar lallai ruwan Tafkin ne ya ragu ba wai tare shi ake yi da gangan ba.

Me ya sa tafkin yake da matukar muhimmanci?

Tafkin Helmand ya kasance mai iyaka, ma’ana a karshensa, ba teku yake gangarawa ba, yana taruwa ne a waje guda.

Ruwan Tafkin Helmand na faro wa ne daga tsaunin Hindu Kush wanda dusar kankara take narkewa sannan ta gangaro kasa, ta hadu da ruwan saman da aka yi, kuma tsayin sa ya kai na daya bisa ukun kasar Afghanistan.

A wajen Afganistan, wannan Tafki ne da ba za a iya rayuwa babu shi ba, saboda shi ke bayar da ruwan sha sannan yana taimaka wa wajen noman rani a kasar.

Afghanistan ta sha fuskantar nuna kyama da hantara bisa cewar ita ce kasar da a duniya ta fi kowacce noma ciyawar ‘Opium’ wadda take daga dangin tsirran ‘Poppy’.

Kuma da ita ake sarrafa mafi yawan kayan maye irin su hodar iblis da sauran su.

Tsirran ‘Poppy’ ba sa bukatar ruwa da yawa, a saboda haka ake noma su sosai a Afghanistan. Idan manoman kasar ba su samu isasshen ruwa don noman sauran amfanin gona ba, sai su koma noman tsirran Poppy.

Manoma a yankin Sistan-Balujistan na Iran kuma, yankin da yake a bushe, yake samun ruwan sama dan kadan, su ma sun dogara ne kan Helmand don yin noma – wanda shi ne babban abinda ke kawowa jama’ar yankin kudi.

Idan ana maganar siyasa kuma, Iran da ‘yan Shi’a ke wa jagoranci, na da ruwa da tsaki sama da Afghanistan.

Yankin Sistan-Balujistan da ke cike da rikici, gida ne na Musulmai Ahlussuna wadanda ke yawan korafin fuskantar nuna wariya daga gwamnatin Tehran.

A karshen 2022, an yi zanga-zanga a yankin sakamakon zargin wani jami’in dan sanda da hantarar wata yarinya.

Me ya janyo karancin ruwan?

Ana amfani da ruwan da ke gangarowa daga Tafkin Helmand ne karkashin yarjejeniyar 1973 da aka kulla tsakanin Afghanistan da Iran.

Karkashin wannan yarjejeniyar, Iran za ta dinga samun ruwa mai yawan kubikmita 22 a kowacce dakika.

Tehran na iya sayen karin kubikmita hudu idan tana so, amma ya danganta da yawan ruwan da ke tafkin.

Kabul na cewa Iran na jan ruwa sama da rabonta

Bangarorin biyu na yawan muhawara kan rabon ruwan, musamman ma a loakcin da ake fama da karancin ruwan sama kamar irin wanda aka fuskanta a shekarar 2000.

“Dukkan kasashen biyu sun bayar da gudunmowa wajen gina madatsun ruwa da gina rijiyoyi ba tare da sanya idanu kan muhallai ba.

"Sun dinga sauya hanyar ruwan tare da shuka tsirran da ba su dace da sauyin yanayi ba” in ji Fatemeh Aman, mai bincike da ta rubuta wata makala kan wannan batu.

Duk da adawar da Iran ke nunawa, Afghanistan ta gina madatsun ruwa a kan Tafkin Helmand, da suka hada da Arghandab da Kajaki.

Tsohon shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya kaddamar da madatsar ruwa ta Kamal Khan da aka gina a kan Helmand a yankin Nimruz wanda yake iyaka da Sistan-Balujistan.

Baya ga noman rani, Afghanistan na son gina madatsun ruwa kamar na Kamal Khan don biyan bukatarta ta lantarki, saboda ta dogara ne kan sayen wuta daga kasashen waje don haskaka gidaje da bai wa masana’antu.

TRT World