Babban hafsan sojin Pakistan da makwabcinsa na Iran sun amince su kara inganta hanyoyin hadin gwiwa da musayar bayanan sirri, tare da daukar kwararan matakai don hana kai hare-hare daga mayakan 'yan aware a kan iyakokinsu, a cewar jami'an Pakistan.
An cimma wannan yarjejeniyar ne yayin wata ziyara da babban hafsan sojin na Pakistan, Janar Asim Munir ya kai birnin Tehran a karshen mako, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Litinin.
Janar Munir ya je Tehran a wata ziyarar kwanaki biyu, bayan yawaitar hare-hare a lardin Baluchistan da ke kudu maso yammacin kasar, wanda ke da iyaka da Afghanistan da kuma Iran.
Dangantakar Pakistan da Iran ta gamu da koma baya a ‘yan shekarun baya-bayan nan, saboda hare-haren wuce gona da iri da mayakan ke kai wa, inda suke amfani da yankin Pakistan.
Kananun kungiyoyin ‘yan aware sun dauki tsawon lokaci suna gwabza fada, kan neman yankin Baluchistan mai arzikin mai da iskar gas, ya samu ‘yancin kai daga gwamnatin kasar Pakistan.
Hakazalika, mayakan da ke adawa da Iran sun yi ta kai hari kan iyakar kasar a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya kara tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin kasashen.
Musayar bayanan sirri
A wata sanarwa da rundunar sojin Pakistan ta fitar, Janar Munir ya gana da babban hafsan sojin Iran, Janar Mohammad Hossein Bagheri, inda ya yi kira ga shugaban kasar Ebrahim Raisi, tare da bayyana cewa bangarorin biyu sun amince cewa matsalar ta'addanci barazana ce ga ko wannen su.
"Sun sha alwashin kawar da mummunar matsala ta barazanar ta'addanci a yankunan da ke kan iyakokinsu, ta hanyar musayar bayanan sirri game da hanyoyin sadarwar 'yan ta'adda, tare da fadada hanyoyin inganta hadin gwiwa a fannin tsaro." In ji sanarwar.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakanin Pakistan da shugabannin Taliban na Afghanistan, wadanda Islamabad ta zarga da ba da mafaka ga wata babbar kungiyar ta'addanci da ake kira Tehreek-e-Taliban Pakistan, ko TTP.
Kungiyar ta TTP ta samu karfin gwiwa tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko a Afghanistan, a shekarar 2021.